< 1 Bitrus 3 >
1 Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba
Ὁμοίως αἱ γυναῖκες ὑποτασσόμεναι τοῖς ἰδίοις ἀνδράσιν, ἵνα καὶ εἴ τινες ἀπειθοῦσι τῷ λόγῳ, διὰ τῆς τῶν γυναικῶν ἀναστροφῆς ἄνευ λόγου κερδηθήσονται,
2 sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi.
ἐποπτεύσαντες τὴν ἐν φόβῳ ἁγνὴν ἀναστροφὴν ὑμῶν.
3 Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada.
ὧν ἔστω οὐχ ὁ ἔξωθεν ἐμπλοκῆς τριχῶν καὶ περιθέσεως χρυσίων ἢ ἐνδύσεως ἱματίων κόσμος,
4 Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.
ἀλλ᾽ ὁ κρυπτὸς τῆς καρδίας ἄνθρωπος ἐν τῷ ἀφθάρτῳ τοῦ πραέος καὶ ἡσυχίου πνεύματος, ὅ ἐστιν ἐνώπιον τοῦ Θεοῦ πολυτελές.
5 Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya,
οὕτω γάρ ποτε καὶ αἱ ἅγιαι γυναῖκες αἱ ἐλπίζουσαι ἐπὶ τὸν Θεὸν ἐκόσμουν ἑαυτάς, ὑποτασσόμεναι τοῖς ἰδίοις ἀνδράσιν,
6 kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.
ὡς Σάρρα ὑπήκουσε τῷ Ἀβραάμ, κύριον αὐτὸν καλοῦσα· ἧς ἐγενήθητε τέκνα· — ἀγαθοποιοῦσαι καὶ μὴ φοβούμεναι μηδεμίαν πτόησιν.
7 Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.
Οἱ ἄνδρες ὁμοίως συνοικοῦντες κατὰ γνῶσιν, ὡς ἀσθενεστέρῳ σκεύει τῷ γυναικείῳ ἀπονέμοντες τιμήν, ὡς καὶ συγκληρονόμοι χάριτος ζωῆς, εἰς τὸ μὴ ἐγκόπτεσθαι τὰς προσευχὰς ὑμῶν.
8 A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u.
Τὸ δὲ τέλος πάντες ὁμόφρονες, συμπαθεῖς, φιλάδελφοι, εὔσπλαγχνοι, φιλόφρονες,
9 Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka.
μὴ ἀποδιδόντες κακὸν ἀντὶ κακοῦ ἢ λοιδορίαν ἀντὶ λοιδορίας, τοὐναντίον δὲ εὐλογοῦντες, εἰδότες ὅτι εἰς τοῦτο ἐκλήθητε, ἵνα εὐλογίαν κληρονομήσητε.
10 Gama, “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa, yă kuma ga kwanaki masu kyau dole yă ƙame harshensa daga mugunta leɓunansa kuma daga maganar yaudara.
ὁ γὰρ θέλων ζωὴν ἀγαπᾶν καὶ ἰδεῖν ἡμέρας ἀγαθὰς παυσάτω τὴν γλῶσσαν αὐτοῦ ἀπὸ κακοῦ καὶ χείλη αὐτοῦ τοῦ μὴ λαλῆσαι δόλον,
11 Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta; dole yă nemi salama yă kuma bi ta.
ἐκκλινάτω ἀπὸ κακοῦ καὶ ποιησάτω ἀγαθόν, ζητησάτω εἰρήνην καὶ διωξάτω αὐτήν.
12 Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu, amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”
ὅτι ὀφθαλμοὶ Κυρίου ἐπὶ δικαίους καὶ ὦτα αὐτοῦ εἰς δέησιν αὐτῶν, πρόσωπον δὲ Κυρίου ἐπὶ ποιοῦντας κακά.
13 Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta?
Καὶ τίς ὁ κακώσων ὑμᾶς, ἐὰν τοῦ ἀγαθοῦ μιμηταὶ γένησθε;
14 Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”
ἀλλ᾽ εἰ καὶ πάσχοιτε διὰ δικαιοσύνην, μακάριοι. τὸν δὲ φόβον αὐτῶν μὴ φοβηθῆτε μηδὲ ταραχθῆτε,
15 Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,
Κύριον δὲ τὸν Θεὸν ἁγιάσατε ἐν ταῖς καρδίαις ὑμῶν, ἕτοιμοι δὲ ἀεὶ πρὸς ἀπολογίαν παντὶ τῷ αἰτοῦντι ὑμᾶς λόγον περὶ τῆς ἐν ὑμῖν ἐλπίδος μετὰ πραΰτητος καὶ φόβου,
16 tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi.
συνείδησιν ἔχοντες ἀγαθήν, ἵνα ἐν ᾧ καταλαλοῦσιν ὑμῶν ὡς κακοποιῶν, καταισχυνθῶσιν οἱ ἐπηρεάζοντες ὑμῶν τὴν ἀγαθὴν ἐν Χριστῷ ἀναστροφήν.
17 Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.
κρεῖττον γὰρ ἀγαθοποιοῦντας, εἰ θέλοι τὸ θέλημα τοῦ Θεοῦ, πάσχειν ἢ κακοποιοῦντας.
18 Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,
ὅτι καὶ Χριστὸς ἅπαξ περὶ ἁμαρτιῶν ἔπαθε, δίκαιος ὑπὲρ ἀδίκων, ἵνα ἡμᾶς προσαγάγῃ τῷ Θεῷ, θανατωθεὶς μὲν σαρκί, ζωοποιηθεὶς δὲ πνεύματι·
19 ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi
ἐν ᾧ καὶ τοῖς ἐν φυλακῇ πνεύμασι πορευθεὶς ἐκήρυξεν,
20 waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa,
ἀπειθήσασί ποτε, ὅτε ἀπεξεδέχετο ἡ τοῦ Θεοῦ μακροθυμία ἐν ἡμέραις Νῶε κατασκευαζομένης κιβωτοῦ, εἰς ἣν ὀλίγαι, τοῦτ᾽ ἔστιν ὀκτὼ ψυχαί, διεσώθησαν δι᾽ ὕδατος.
21 ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,
ὃ ἀντίτυπον νῦν καὶ ἡμᾶς σῴζει βάπτισμα, οὐ σαρκὸς ἀπόθεσις ῥύπου, ἀλλὰ συνειδήσεως ἀγαθῆς ἐπερώτημα εἰς Θεόν, δι᾽ ἀναστάσεως Ἰησοῦ Χριστοῦ,
22 wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.
ὅς ἐστιν ἐν δεξιᾷ τοῦ Θεοῦ πορευθεὶς εἰς οὐρανόν, ὑποταγέντων αὐτῷ ἀγγέλων καὶ ἐξουσιῶν καὶ δυνάμεων.