< 1 Sarakuna 9 >

1 Sa’ad da Solomon ya gama ginin haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki, ya kuma yi dukan abin da yake so yă yi,
所羅門建造耶和華殿和王宮,並一切所願意建造的都完畢了,
2 sai Ubangiji ya bayyana gare shi sau na biyu, kamar yadda ya bayyana masa a Gibeyon.
耶和華就二次向所羅門顯現,如先前在基遍向他顯現一樣,
3 Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu’arka da kuma roƙon da ka yi a gabana; na tsarkake wannan haikali wanda ka gina, ta wurinsa Sunana zai kasance a can har abada. Idanuna da zuciyata kullum za su kasance a can.
對他說:「你向我所禱告祈求的,我都應允了。我已將你所建的這殿分別為聖,使我的名永遠在其中;我的眼、我的心也必常在那裏。
4 “Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina,
你若效法你父大衛,存誠實正直的心行在我面前,遵行我一切所吩咐你的,謹守我的律例典章,
5 zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’
我就必堅固你的國位在以色列中,直到永遠,正如我應許你父大衛說:『你的子孫必不斷人坐以色列的國位。』
6 “Amma in kai, ko’ya’yanka maza, suka juye daga gare ni, ba ku kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da na ba ku ba, kuka yi gaba, kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka kuma yi musu sujada,
倘若你們和你們的子孫轉去不跟從我,不守我指示你們的誡命律例,去事奉敬拜別神,
7 sai in yanke mutanen Isra’ila daga ƙasar da na ba su, in kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Isra’ila kuwa za tă zama abin gori da abin dariya a cikin dukan mutane.
我就必將以色列人從我賜給他們的地上剪除,並且我為己名所分別為聖的殿也必捨棄不顧,使以色列人在萬民中作笑談,被譏誚。
8 Wannan haikali zai zama tarin juji. Duk wanda ya wuce ta hanyan nan kuwa zai ji tausayi, yă kuma yi tsaki yana cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka ga wannan ƙasa da kuma wannan haikali?’
這殿雖然甚高,將來經過的人必驚訝、嗤笑,說:『耶和華為何向這地和這殿如此行呢?』
9 Mutane za su amsa su ce, ‘Saboda sun yashe Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna yin musu sujada, suna bauta musu ne, ya sa Ubangiji ya kawo dukan masifan nan a kansu.’”
人必回答說:『是因此地的人離棄領他們列祖出埃及地之耶和華-他們的上帝,去親近別神,事奉敬拜他,所以耶和華使這一切災禍臨到他們。』」
10 A ƙarshen shekaru ashirin da Solomon ya ɗauka yana gina haikalin Ubangiji da fadan sarki,
所羅門建造耶和華殿和王宮,這兩所二十年才完畢了。
11 sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki.
泰爾王希蘭曾照所羅門所要的,資助他香柏木、松木,和金子;所羅門王就把加利利地的二十座城給了希蘭。
12 Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya don yă ga garuruwan da Solomon ya ba shi, sai bai ji daɗi ba.
希蘭從泰爾出來,察看所羅門給他的城邑,就不喜悅,
13 Sai ya ce, “Wanda irin garuruwa ke nan ka ba ni, ɗan’uwana?” Saboda haka ya kira su Ƙasar Kabul, sunan da suke da shi har wa yau.
說:「我兄啊,你給我的是甚麼城邑呢?」他就給這城邑之地起名叫迦步勒,直到今日。
14 Hiram kuwa ya aika wa sarki talenti 120 na zinariya.
希蘭給所羅門一百二十他連得金子。
15 Ga lissafin ma’aikatan gandun da Sarki Solomon ya ɗauka don ginin haikalin Ubangiji, da fadarsa, da madogaran gini, da katangar Urushalima, da kuma Hazor Megiddo da Gezer.
所羅門王挑取服苦的人,是為建造耶和華的殿、自己的宮、米羅、耶路撒冷的城牆、夏瑣、米吉多,並基色。
16 (Fir’auna sarkin Masar ya kai wa Gezer hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Ya sa mata wuta, ya kashe Kan’aniyawanta mazaunan wurin, ya kuma ba da ita a matsayin kyautar aure ga’yarsa, matar Solomon.
先前埃及王法老上來攻取基色,用火焚燒,殺了城內居住的迦南人,將城賜給他女兒所羅門的妻作妝奩。
17 Solomon kuwa ya sāke gina Gezer.) Ya gina Bet-Horon ta Kwari,
所羅門建造基色、下伯‧和崙、
18 da Ba’alat, da Tadmor a hamada, na cikin ƙasarsa.
巴拉,並國中曠野裏的達莫,
19 Haka kuma ya gina dukan biranen ajiyarsa, da garuruwa domin kekunan yaƙinsa, da garuruwa domin dawakansa. Ya gina duk abin da ya so yă ginawa a Urushalima, da Lebanon, da kuma ko’ina a dukan yankin da ya yi mulki.
又建造所有的積貨城,並屯車和馬兵的城,與耶路撒冷、黎巴嫩,以及自己治理的全國中所願建造的。
20 Dukan Amoriyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa da Yebusiyawan da suka ragu a ƙasar (waɗanda ba Isra’ilawa ba ne),
至於國中所剩下不屬以色列人的亞摩利人、赫人、比利洗人、希未人、耶布斯人,
21 wato, waɗanda suka ragu a ƙasar, waɗanda Isra’ilawa ba su iya hallakawa ba, su ne Solomon ya ɗauka su zama bayinsa don aikin gandu, kamar yadda yake har wa yau.
就是以色列人不能滅盡的,所羅門挑取他們的後裔作服苦的奴僕,直到今日。
22 Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi ba; su ne mayaƙansa, shugabannin gwamnatinsa, dogarawansa, shugabannin sojojinsa, da shugabanninsa na kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙinsa.
惟有以色列人,所羅門不使他們作奴僕,乃是作他的戰士、臣僕、統領、軍長、車兵長、馬兵長。
23 Su ne kuma manyan shugabanni masu lura da ayyukan Solomon, su ne shugabanni 550 masu lura da mutanen da suke aiki.
所羅門有五百五十督工的,監管工人。
24 Bayan’yar Fir’auna ta haura daga Birnin Dawuda zuwa fadan da Solomon ya gina mata, sai ya gina madogaran gini.
法老的女兒從大衛城搬到所羅門為她建造的宮裏。那時,所羅門才建造米羅。
25 Sau uku a shekara Solomon kan miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji, yana ƙone turare a gaban Ubangiji haɗe da su, ta haka ya cika abin da ake bukata na haikali.
所羅門每年三次在他為耶和華所築的壇上獻燔祭和平安祭,又在耶和華面前的壇上燒香。這樣,他建造殿的工程完畢了。
26 Sarki Solomon ya kuma gina jiragen ruwa a Eziyon Geber, wadda take kusa da Elot a Edom, a bakin Jan Teku.
所羅門王在以東地紅海邊,靠近以祿的以旬‧迦別製造船隻。
27 Hiram kuwa ya aiki mutanensa, masu tuƙan jirgin ruwa waɗanda suka san teku, don su yi hidima a jerin jiragen ruwa tare da mutanen Solomon.
希蘭差遣他的僕人,就是熟悉泛海的船家,與所羅門的僕人一同坐船航海。
28 Suka tafi Ofir suka kuma dawo da talenti 420 na zinariya, wanda suka ba wa Sarki Solomon.
他們到了俄斐,從那裏得了四百二十他連得金子,運到所羅門王那裏。

< 1 Sarakuna 9 >