< 1 Sarakuna 6 >

1 A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji.
ויהי בשמונים שנה וארבע מאות שנה לצאת בני ישראל מארץ מצרים בשנה הרביעית בחדש זו הוא החדש השני למלך שלמה על ישראל ויבן הבית ליהוה׃
2 Haikalin da Sarki Solomon ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu talatin ne.
והבית אשר בנה המלך שלמה ליהוה ששים אמה ארכו ועשרים רחבו ושלשים אמה קומתו׃
3 Shirayin da yake a gaban ainihin zauren haikalin, ya ƙara faɗin haikalin da kamu ashirin, ya kuma nausa daga gaban haikalin kamu goma.
והאולם על פני היכל הבית עשרים אמה ארכו על פני רחב הבית עשר באמה רחבו על פני הבית׃
4 Ya yi tagogin da suka fi fāɗi daga ciki fiye da waje a haikalin.
ויעש לבית חלוני שקפים אטמים׃
5 A jikin bangayen babban zaure da kuma cikin wuri mai tsarki, ya gina ɗakuna kewaye da ginin, inda akwai ɗakuna a gefe.
ויבן על קיר הבית יצוע סביב את קירות הבית סביב להיכל ולדביר ויעש צלעות סביב׃
6 Fāɗin ɗakunan ƙasa, kamu biyar ne, fāɗin ɗakunan tsakiya, kamu shida ne, fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa, kamu bakwai ne. Ya yi bangaye kewaye a waje da haikalin don kada a sa wani abu a bangayen haikali.
היצוע התחתנה חמש באמה רחבה והתיכנה שש באמה רחבה והשלישית שבע באמה רחבה כי מגרעות נתן לבית סביב חוצה לבלתי אחז בקירות הבית׃
7 A yin ginin haikalin, duwatsun da aka fafe ne kaɗai daga wurin fafe duwatsu aka yi amfani da su, ba a ji karar guduma ko gizago, ko wani abin da aka yi da ƙarfe a wurin ginin haikali yayinda ake gina shi ba.
והבית בהבנתו אבן שלמה מסע נבנה ומקבות והגרזן כל כלי ברזל לא נשמע בבית בהבנתו׃
8 Ƙofar zuwa ɗakunan ƙasa tana gefen kudu na haikalin; akwai matakai da suka bi zuwa hawa na tsakiya, daga can kuma matakan sun wuce zuwa hawa na uku.
פתח הצלע התיכנה אל כתף הבית הימנית ובלולים יעלו על התיכנה ומן התיכנה אל השלשים׃
9 A haka ya gina haikalin ya kuma gama shi, ya jinƙe shi da manyan katakai da kuma katakan al’ul.
ויבן את הבית ויכלהו ויספן את הבית גבים ושדרת בארזים׃
10 Ya kuma gina ɗakunan gefe duka a gefen haikalin. Tsayin kowanne, kamu biyar ne, aka haɗa su da haikalin da manyan katakan al’ul.
ויבן את היצוע על כל הבית חמש אמות קומתו ויאחז את הבית בעצי ארזים׃
11 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Solomon ta ce,
ויהי דבר יהוה אל שלמה לאמר׃
12 “Game da wannan haikalin da kake ginawa, in ka bi ƙa’idodina, ka cika farillaina, ka kiyaye dukan umarnaina, ka kuma yi biyayya da su, zan cika alkawarin da na yi wa mahaifinka Dawuda ta wurinka.
הבית הזה אשר אתה בנה אם תלך בחקתי ואת משפטי תעשה ושמרת את כל מצותי ללכת בהם והקמתי את דברי אתך אשר דברתי אל דוד אביך׃
13 Zan kuma zauna a cikin Isra’ilawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.”
ושכנתי בתוך בני ישראל ולא אעזב את עמי ישראל׃
14 Saboda haka Solomon ya gina haikalin ya kuma gama shi.
ויבן שלמה את הבית ויכלהו׃
15 Ya rufe bangon ciki da katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama, ya kuma rufe daɓen da katakan itacen fir.
ויבן את קירות הבית מביתה בצלעות ארזים מקרקע הבית עד קירות הספן צפה עץ מבית ויצף את קרקע הבית בצלעות ברושים׃
16 Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi a can ƙuryar haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama.
ויבן את עשרים אמה מירכותי הבית בצלעות ארזים מן הקרקע עד הקירות ויבן לו מבית לדביר לקדש הקדשים׃
17 Tsawon babban zaure a gaban wannan ɗaki, kamu arba’in ne.
וארבעים באמה היה הבית הוא ההיכל לפני׃
18 An yi wa katakan itacen al’ul na cikin haikalin zāne mai fasalin gora da na buɗaɗɗun furanni. An rufe bangon ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin.
וארז אל הבית פנימה מקלעת פקעים ופטורי צצים הכל ארז אין אבן נראה׃
19 Ya shirya wuri mai tsarki na ciki can cikin haikali don yă sa akwatin alkawarin Ubangiji a can.
ודביר בתוך הבית מפנימה הכין לתתן שם את ארון ברית יהוה׃
20 Tsawon wuri mai tsarki na ciki kamu ashirin, fāɗin kamu ashirin, tsayin kuma kamu ashirin. Ya dalaye cikin da zinariya zalla, ya kuma dalaye bagade al’ul ɗin.
ולפני הדביר עשרים אמה ארך ועשרים אמה רחב ועשרים אמה קומתו ויצפהו זהב סגור ויצף מזבח ארז׃
21 Solomon ya rufe cikin haikalin da zinariya zalla, ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban wuri mai tsarki na ciki, wanda aka dalaye da zinariya.
ויצף שלמה את הבית מפנימה זהב סגור ויעבר ברתיקות זהב לפני הדביר ויצפהו זהב׃
22 Haka ya dalaye dukan cikin da zinariya. Ya kuma dalaye bagade na cikin wuri mai tsarki da zinariya.
ואת כל הבית צפה זהב עד תם כל הבית וכל המזבח אשר לדביר צפה זהב׃
23 A wuri mai tsarki na can ciki, ya yi kerubobi biyu na itacen zaitun, kowanne mai tsayi kamu goma.
ויעש בדביר שני כרובים עצי שמן עשר אמות קומתו׃
24 Fiffike ɗaya na kerub na fari tsawonsa kamu biyar ne, ɗayan fiffike kuma kamu biyar, kamu goma daga ƙarshen fiffike zuwa ƙarshen fiffike.
וחמש אמות כנף הכרוב האחת וחמש אמות כנף הכרוב השנית עשר אמות מקצות כנפיו ועד קצות כנפיו׃
25 Kerub na biyun shi ma kamu goma ne, gama kerubobi biyun sun yi kama da juna a girma da kuma siffa.
ועשר באמה הכרוב השני מדה אחת וקצב אחד לשני הכרבים׃
26 Tsayin kowane kerub kamu goma ne.
קומת הכרוב האחד עשר באמה וכן הכרוב השני׃
27 Ya ajiye kerubobin a ɗaki na can cikin haikalin, da fikafikansu a buɗe. Fiffiken kerub ɗaya ya taɓa bango guda, yayinda fiffiken ɗayan ya taɓa ɗayan bangon, kuma fikafikansu sun taɓa juna a tsakiyar ɗakin.
ויתן את הכרובים בתוך הבית הפנימי ויפרשו את כנפי הכרבים ותגע כנף האחד בקיר וכנף הכרוב השני נגעת בקיר השני וכנפיהם אל תוך הבית נגעת כנף אל כנף׃
28 Ya dalaye kerubobin da zinariya.
ויצף את הכרובים זהב׃
29 A bangaye kewaye da haikali, a ɗakuna ciki da waje, ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da furanni buɗaɗɗu.
ואת כל קירות הבית מסב קלע פתוחי מקלעות כרובים ותמרת ופטורי צצים מלפנים ולחיצון׃
30 Ya kuma rufe ƙasan ɗakuna ciki da wajen haikali da zinariya.
ואת קרקע הבית צפה זהב לפנימה ולחיצון׃
31 Don ƙofar shiga wuri mai tsarki na ciki kuwa, ya yi ƙofofin katakon zaitun da madogarai masu gefe biyar.
ואת פתח הדביר עשה דלתות עצי שמן האיל מזוזות חמשית׃
32 A kan ƙofofin katakan zaitun kuwa ya zāzzāna kerubobi, itatuwa dabino, da furanni buɗaɗɗu, ya kuma dalaye kerubobin, da kuma itatuwan dabinon da zinariya.
ושתי דלתות עצי שמן וקלע עליהם מקלעות כרובים ותמרות ופטורי צצים וצפה זהב וירד על הכרובים ועל התמרות את הזהב׃
33 Haka ma ya yi madogarai masu gefe huɗu na katakon zaitun don ƙofar shiga zuwa babban zaure.
וכן עשה לפתח ההיכל מזוזות עצי שמן מאת רבעית׃
34 Ya yi ƙofofi biyu na itacen fir, kowanne yana da shafi biyu da suke juyewa a maɗaurai.
ושתי דלתות עצי ברושים שני צלעים הדלת האחת גלילים ושני קלעים הדלת השנית גלילים׃
35 Ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da kuma furanni buɗaɗɗu a kansu, ya kuma dalaye su da zinariyar da aka buga daidai a kan sassaƙa.
וקלע כרובים ותמרות ופטרי צצים וצפה זהב מישר על המחקה׃
36 Ya kuma gina filin ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu, jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul.
ויבן את החצר הפנימית שלשה טורי גזית וטור כרתת ארזים׃
37 An kafa tushen haikalin Ubangiji a shekara ta huɗu, a watan Zif.
בשנה הרביעית יסד בית יהוה בירח זו׃
38 A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.
ובשנה האחת עשרה בירח בול הוא החדש השמיני כלה הבית לכל דבריו ולכל משפטו ויבנהו שבע שנים׃

< 1 Sarakuna 6 >