< 1 Sarakuna 21 >

1 Ana nan bayan haka sai waɗannan abubuwa suka faru. Nabot mutumin Yezireyel yana da gonar inabi a Yezireyel, a yankin Samariya, kusa da gidan Sarki Ahab.
Voici ce qui arriva à la suite de ces événements. Naboth, le Jezreélite, demeurant à Jezreël, possédait une vigne auprès du palais d’Achab, roi de Samarie.
2 Sai Ahab ya ce wa Nabot, “Ka ba ni gonar inabinka in yi amfani da ita don kayan lambu, da yake tana kusa da fadana. Zan ba ka wata gonar inabin da ta fi wannan, ko kuma in ka gwammace, sai in biya ka duk abin da ya dace da ita.”
Achab paria ainsi à Naboth: "Cède-moi ta vigne pour que j’en fasse un jardin potager, car elle est près de ma maison; je te donnerai en échange une vigne meilleure. Si tu le préfères, je t’en remettrai la valeur en argent."
3 Amma Nabot ya amsa wa Ahab ya ce, “Ubangiji yă sawwaƙe in ba ka gādon kakannina.”
Naboth répondit à Achab: "Le Seigneur me préserve de te céder l’héritage de mes pères!"
4 Ahab ya cika da fushi saboda Nabot, mutumin Yezireyel ya ce, “Ba zan ba ka gādon kakannina ba.” Ya kwanta a gadonsa yana zub da hawaye, ya kuma ƙi cin abinci.
Achab rentra chez lui triste et abattu, à cause de la réponse que lui avait faite Naboth le Jézreélite, en disant: "Je ne te céderai pas l’héritage de mes pères." Il se jeta sur son lit, la face tournée vers le mur, et ne prit point d’aliments.
5 Matarsa Yezebel ta shiga ciki ta tambaye shi, ta ce, “Me ya sa ka kumbura? Me ya sa ba za ka ci abinci ba?”
Jézabel, sa femme, vint le voir et lui dit: "Pourquoi ton esprit est-il abattu et ne prends-tu pas de nourriture?"
6 Sai ya amsa mata, ya ce, “Domin na ce wa Nabot mutumin Yezireyel, ‘Ka sayar mini gonar inabinka; ko kuwa in ka gwammace, zan ba ka wata gonar inabi a maimakonta.’ Amma ya ce, ‘Ba zan ba ka gonar inabina ba.’”
Il lui répondit: "C’Est que j’ai parlé à Naboth, le Jezreélite, et lui ai dit: "Donne-moi ta vigne à prix d’argent, ou, si tu le préfères, je t’en donnerai une autre à la place. Il a répondu: Je ne te donnerai point ma vigne."
7 Yezebel matarsa ta ce, “Yaya kake yi kamar ba kai ne sarki Isra’ila ba? Tashi ka ci abinci! Ka yi farin ciki. Zan ba ka gonar inabin Nabot mutumin Yezireyel.”
Jézabel, sa femme, lui répondit: "Est-ce bien toi qui exerces aujourd’hui la royauté sur Israël? Lève-toi, prends de la nourriture et sois de bonne humeur; c’est moi qui te procurerai la vigne de Naboth, le Jezreélite."
8 Sai ta rubuta wasiƙu a sunan Ahab, ta buga hatiminsa a kansu, sa’an nan ta aika su ga dattawa da manyan gari waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake.
Elle écrivit des lettres au nom d’Achab, les scella du sceau royal et les expédia aux anciens et aux nobles de sa ville, qui demeuraient près de Naboth.
9 Cikin waɗannan wasiƙu ta rubuta, “Ku yi shelar ranar azumi, ku zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane.
Elle avait écrit dans ces lettres: "Proclamez un jeûne, faites asseoir Naboth à la tête du peuple;
10 Amma ku zaunar da waɗansu’yan iska biyu ɗaura da shi, ku sa su ba da shaida cewa ya zagi Allah da sarki. Sa’an nan ku ɗauke shi ku jajjefe shi da dutse sai ya mutu.”
placez en face de lui deux individus sans scrupules, qui déposeront contre lui, en disant: Tu as outragé Dieu et le Roi. Puis on le fera sortir, et on le tuera à coups de pierres."
11 Sai dattawa da manyan gari, waɗanda suke zama a birnin da Nabot yake, suka yi kamar yadda Yezebel ta umarta a cikin wasiƙun da ta rubuta.
Les anciens et les nobles, qui habitaient dans sa ville, exécutèrent l’ordre de Jézabel, tel qu’il était consigné dans les lettres qu’elle leur avait envoyées.
12 Suka yi shelar azumi, suka kuma zaunar da Nabot a wuri mai martaba a cikin mutane.
Ils proclamèrent un jeûne, et placèrent Naboth à la tête du peuple.
13 Sa’an nan’yan iska biyu suka zo, suka zauna ɗaura da shi, suka kawo zarge a kan Nabot a gaban mutane, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.” Saboda haka aka ɗauke shi waje da birnin, aka jajjefe shi da dutse har ya mutu.
Les deux hommes, des gens pervers, vinrent s’asseoir en face de lui, et déposèrent contre Naboth en présence du peuple en disant: "Naboth a outragé Dieu et le roi." On l’emmena hors de la ville, on le lapida, et il mourut.
14 Sa’an nan suka aika wa Yezebel. “An jajjefe Nabot, ya kuma mutu.”
Puis on envoya dire à Jézabel: "Naboth a été lapidé, il est mort."
15 Nan da nan sa’ad da Yezebel ta ji cewa an jajjefe Nabot da dutse ya kuma mutu, sai ta ce wa Ahab, “Tashi ka mallaki gonar inabin Nabot mutumin Yezireyel wanda ya ƙi ya sayar maka. Ba shi da rai, ya mutu.”
En recevant cette nouvelle, Jézabel dit à Achab: "Va, prends possession de la vigne de Naboth, le Jezreélite, qui avait refusé de te la céder à prix d’argent; Naboth a cessé de vivre, et il est mort."
16 Da Ahab ya ji cewa Nabot ya mutu, sai ya tashi ya gangara don yă mallaki gonar inabin Nabot.
En apprenant la mort de Naboth, Achab se leva et se dirigea vers la vigne de Naboth pour en prendre possession.
17 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe.
Mais la parole de l’Eternel s’adressa à Elie, le Tisbite, en ces termes:
18 Ta ce, “Gangara don ka sadu da Ahab sarkin Isra’ila, wanda yake mulki a Samariya. Yanzu yana a gonar inabin Nabot, inda ya tafi yă mallake ta.
"Lève-toi, va au-devant d’Achab, roi d’Israël, qui est à Samarie; il se trouve dans la vigne de Naboth, où il est descendu pour en prendre possession.
19 Ka ce masa, Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba ka kashe mutum ka kuma ƙwace kayansa ba?’ Sa’an nan ka ce masa ga abin da Ubangiji ya ce, ‘A inda karnuka suka lashe jinin Nabot, karnuka za su lashe jininka, I, naka!’”
Tu lui parleras en ces termes: Ainsi a dit l’Eternel: Quoi! Tu as assassiné et maintenant tu prends possession! Ainsi parle l’Eternel: A cette même place où les chiens ont léché le sang de Naboth, ils lécheront aussi le tien."
20 Ahab ya ce wa Iliya, “Wato, ka same ni kuma, abokin gābana!” Sai ya amsa ya ce, “Na same ka, domin ka sayar da kanka ga yin mugunta a gaban Ubangiji.
Achab dit à Elie: "Tu m’as donc atteint, ô mon ennemi? Je t’ai atteint, répondit-il, parce que tu t’es livré toi-même en faisant ce qui déplaît à l’Eternel.
21 ‘Zan kawo masifa a kanka. Zan kawar da zuriyarka, in kuma yanke daga Ahab kowane ɗa namiji na ƙarshe cikin Isra’ila, bawa ko’yantacce.
Eh bien! Moi, (dit l’Eternel), je susciterai le malheur contre toi, je balaierai tes derniers vestiges, je ne laisserai point subsister d’Achab la plus infime créature, ni retraite, ni ressources en Israël.
22 Zan mai da gidanka kamar gida Yerobowam ɗan Nebat, da na Ba’asha ɗan Ahiya, domin ka tsokane ni har na yi fushi, ka kuma sa Isra’ila ya yi zunubi.’
Bref, je traiterai ta maison comme celle de Jéroboam, fils de Nebat, et comme celle de Baasa, fils d’Ahiyya, parce que tu as provoqué mon irritation et fait pécher Israël.
23 “Game da Yezebel kuwa Ubangiji ya ce, ‘Karnuka za su cinye Yezebel a katangar Yezireyel.’
Et sur Jézabel aussi le Seigneur a dit cette parole: Les chiens dévoreront Jézabel dans le territoire de Jezreël.
24 “Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ahab waɗanda suka mutu a cikin birni, tsuntsayen sararin sama kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.”
Ceux d’Achab qui mourront dans la ville seront dévorés par les chiens, et ceux qui mourront dans la campagne seront la proie des oiseaux du ciel."
25 (Babu wani mutum kamar Ahab, wanda ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Yezebel matarsa ce ta zuga shi.
En vérité, personne encore ne s’était, comme Achab, adonné à faire ce qui déplaît à l’Eternel, entraîné qu’il fut par sa femme Jézabel.
26 Ya yi abar ƙyama ƙwarai ta wurin bin gumaka, kamar Amoriyawan da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ila.)
Il commit force abominations, en adoptant le culte des impures idoles, comme avaient fait les Amorréens, que l’Eternel avait dépossédés en faveur des enfants d’Israël.
27 Sa’ad da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, sai ya yage rigarsa, ya sa rigunan makoki, ya kuma yi azumi. Ya kwanta a kayan makoki, ya kuma yi tafiya cikin sauƙinkai.
Lorsque Achab entendit ces paroles, il déchira ses vêtements, se couvrit le corps d’un cilice et jeûna; il coucha dans ce cilice, et se traînait en marchant.
28 Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe, ta ce,
Alors l’Eternel s’adressa en ces termes à Elie, le Tisbite:
29 “Ka lura da yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana kuwa? Domin ya ƙasƙantar da kansa, ba zan kawo wannan masifa a kwanakinsa ba, amma zan kawo ta a kan gidansa a kwanakin ɗansa.”
"Tu as vu comme Achab s’est humilié devant moi! Pour prix de cette humilité, je ne susciterai pas le malheur sous son règne; c’est du temps de son fils que je susciterai le malheur sur sa maison."

< 1 Sarakuna 21 >