< 1 Sarakuna 20 >
1 Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tattara mayaƙansa gaba ɗaya. Sarakuna talatin da biyu suka tafi tare da shi haɗe da dawakansu da kekunan yaƙinsu. Ya haura ya yi wa Samariya kwanto, ya kuma yaƙe ta.
2 Ya aika da’yan aika zuwa cikin birnin wurin Ahab sarkin Isra’ila yana cewa, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce,
3 ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Mafi kyau cikin matanka da’ya’yanka nawa ne.’”
4 Sarkin Isra’ila ya amsa, ya ce, “Kamar dai yadda ka faɗa, ranka yă daɗe, sarki. Ni da dukan abin da nake da shi, naka ne.”
5 Sai’yan aikan suka sāke dawo suka ce, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce, ‘Na aika ka ba da azurfarka da zinariyarka, matanka da kuma’ya’yanka.
6 Amma war haka gobe zan aika shugabannina su bincika fadanka da kuma gidajen shugabanninka. Za su kwashe dukan abubuwan da kake ganin darajarsu su tafi.’”
7 Sarkin Isra’ila ya tattara dukan dattawan ƙasar, ya ce musu, “Ku duba fa, wannan mutum yana neman tsokana! Sa’ad da ya aika in ba shi matana da’ya’yana, azurfana da zinariyana, ban hana masa ba.”
8 Dattawa da dukan mutane suka amsa, suka ce, “Kada ka saurare shi ko ka yarda da abin da yake bukata.”
9 Saboda haka ya ba wa’yan aikan Ben-Hadad amsa, ya ce, “Ku faɗa wa ranka yă daɗe, sarki, ‘Bawanka zai yi dukan abin da ka bukaci da farko, amma wannan na ƙarshe ba zan iya yin ba.’” Suka tafi suka kai amsar wa Ben-Hadad.
10 Sai Ben-Hadad ya aika da wani saƙo wa Ahab, ya ce, “Bari alloli su yi da ni yadda suke so, su kuma yi haka da tsanani, in isashen ƙura ta rage a Samariya da za a iya ba wa mutanena a tafin hannu.”
11 Sarki Isra’ila ya amsa, ya ce, “Ku faɗa masa, ‘Wanda ya sa kayan yaƙinsa bai kamata yă yi fariya ba sai ya tuɓe su.’”
12 Ben-Hadad ya ji wannan saƙo yayinda shi da sarakunan suke sha a cikin tentunansu, sai ya umarce mutanensa, ya ce, “Ku shirya don yaƙi.” Saboda haka suka shirya don su yaƙi birnin.
13 Ana cikin haka sai wani annabi ya zo wurin Ahab sarkin Isra’ila ya sanar masa cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka ga wannan ɗumbun mayaƙa? Zan ba da su cikin hannunka a yau, sa’an nan za ka san cewa ni ne Ubangiji.’”
14 Ahab ya ce, “Amma wa zai yi haka?” Annabin ya amsa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Sojoji matasa na shugabannin yankuna za su yi haka.’” Ya tambaya, “Wa kuma zai fara yaƙin?” Annabin ya amsa, “Kai za ka fara.”
15 Saboda haka Ahab ya kira sojoji matasa na shugabannin yankuna, mutum 232. Sa’an nan ya tattara sauran Isra’ilawa su 7,000 gaba ɗaya.
16 Suka fita da tsakar rana yayinda Ben-Hadad tare da sarakuna 32 masu goyon bayansa suke cikin tentunansu suna sha, suna buguwa.
17 Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka fara fita. Ben-Hadad kuwa ya riga ya aiki’yan leƙen asiri, waɗanda suka ce, “Mutane suna zuwa daga Samariya.”
18 Ya ce, “In sun fito don salama, ku kamo su da rai; in sun fito yaƙi ne, ku kamo su da rai.”
19 Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka taka suka fita daga birnin da mayaƙa a bayansu.
20 Kowannensu kuwa ya buge abokin gābansa. Ganin wannan, sai Arameyawa suka gudu, Isra’ilawa suna bi. Amma Ben-Hadad na Aram ya tsere a kan dokinsa tare da waɗansu mahayan dawakansa.
21 Sarki Isra’ila ya bi, ya kuma sha ƙarfin dawakan da keken yaƙin, ya kashe Arameyawa da yawa.
22 Daga baya, annabin ya zo wurin sarkin Isra’ila ya ce, “Ka ƙarfafa matsayinka ka kuma ga abin da za a yi, gama a bazara mai zuwa sarkin Aram zai sāke kawo yaƙi.”
23 Ana cikin haka, shugabannin sarkin Aram suka ba shi shawara, “Allolinsu, allolin tuddai ne. Shi ya sa suka fi mu ƙarfi. Amma in mun yaƙe su a fili, tabbatacce za mu fi su ƙarfi.
24 Ka yi wannan. Ka cire dukan sarakuna daga matsayinsu ka sa waɗansu shugabanni a maimakonsu.
25 Dole kuma ka tā da waɗansu mayaƙa kamar waɗanda ka rasa, doki don doki, keken yaƙi kuma don keken yaƙi, saboda mu iya yaƙe Isra’ila a fili. Ta haka tabbatacce za mu fi ƙarfinsu.” Sai ya yarda da su, ya kuma yi haka.
26 Bazara na biye Ben-Hadad ya tattara Arameyawa, ya haura zuwa Afek don yă yaƙi Isra’ila.
27 Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin.
28 Sai mutumin Allah ya zo ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Domin Arameyawa suna tsammani Ubangiji allahn tuddai ne, ba allahn kwari ba, zan ba da wannan ɗumbun mayaƙa a hannuwanka, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’”
29 Kwana bakwai suka yi sansani ɗaura da juna, a rana ta bakwai sai yaƙi ya haɗu. Isra’ilawa suka kashe sojojin kafa na Arameyawa dubu ɗari a rana ɗaya.
30 Sauransu suka tsere zuwa birnin Afek, inda katangar ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai. Sai Ben-Hadad ya gudu zuwa birni ya ɓuya a ciki cikin ɗaki.
31 Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra’ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa’an nan mu tafi wurin sarkin Isra’ila, wataƙila zai bar ka da rai.”
32 Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’” Sarki ya amsa, “Har yanzu yana da rai? Shi ɗan’uwana ne.”
33 Da ma abin da fadawan suke so su ji ke nan, sai suka yi sauri, suka karɓi maganar a bakinsa, suka ce, “I, ɗan’uwanka, Ben-hadad!” Sarki ya ce, “Ku je ku kawo shi.” Da Ben-Hadad ya fita, sai Ahab ya sa aka kawo shi cikin keken yaƙinsa.
34 Ben-Hadad ya ce, “Zan mayar da biranen mahaifinka da na ƙwace daga mahaifinka. Za ka iya sa wurin kasuwarka a cikin Damaskus, kamar yadda mahaifinka ya yi a Samariya.” Ahab ya ce, “Bisa wannan yarjejjeniya zan sake ka.” Saboda haka ya yi yarjejjeniya da shi, sai ya bar shi ya tafi.
35 Ta wurin maganar Ubangiji, ɗaya daga cikin’ya’ya maza na annabawa ya ce wa abokinsa, “Ka buge ni da makaminka,” amma mutumin ya ƙi.
36 Sai annabin ya ce, “Domin ba ka yi biyayya da Ubangiji ba, da zarar ka bar ni zaki zai kashe ka.” Daga baya mutumin ya tafi, zaki ya same shi, ya kuma kashe shi.
37 Annabin ya sami wani mutum ya ce, “Ka buge ni, ina roƙonka.” Sai mutumin ya buge shi, ya ji masa ciwo.
38 Sa’an nan annabin ya tafi ya tsaya a bakin hanya yana jiran sarki. Ya ɓad da kamanni da ƙyalle a kansa. Ƙyallen ya sauka zuwa bisa idanunsa.
39 Yayinda sarki yake wucewa, sai annabin ya yi kira da ƙarfi gare shi ya ce “Ni bawanka na tafi yaƙi, sai ga wani ya kawo mini wani mutum, ya ce, ‘Ka riƙe wannan mutum, kada ka bar shi yă kuɓuta ko da ƙaƙa, idan ka bari ya kuɓuta, a bakin ranka, ko kuwa ka biya talanti ɗaya na azurfa.’
40 Yayinda bawanka yana fama, yana kai da kawowa, sai mutumin ya ɓace.” Sai sarkin Isra’ila ya ce, “Hukuncinka ke nan, ka furta shi da kanka.”
41 Sai annabin ya cire ƙyallen da sauri daga kansa, da ya rufe idanunsa, sarkin Isra’ila kuwa ya gane shi a matsayi ɗaya daga cikin annabawa.
42 Sai ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka saki mutumin da na ƙudura yă mutu. Saboda haka ranka zai zama a maimakon ransa, mutanenka a maimakon mutanensa.’”
43 Cike da fushi, sarkin Isra’ila ya tafi fadarsa a Samariya.