< 1 Sarakuna 15 >

1 A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yerobowam ɗan Nebat, Abiyam ya zama sarkin Yahuda,
尼八的兒子耶羅波安王十八年,亞比央登基作猶大王,
2 ya kuma yi mulki a Urushalima shekara uku. Sunan mahaifiyarsa Ma’aka ne,’yar Abisalom.
在耶路撒冷作王三年。他母親名叫瑪迦,是押沙龍的女兒。
3 Shi ma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Zuciyarsa ba tă bi Ubangiji Allahnsa, kamar yadda zuciyar Dawuda kakansa ta yi ba.
亞比央行他父親在他以前所行的一切惡,他的心不像他祖大衛的心,誠誠實實地順服耶和華-他的上帝。
4 Duk da haka, saboda Dawuda Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima ta wurin ta da wani da ya gāje shi, ta wurinsa kuma Urushalima ta yi ƙarfi.
然而耶和華-他的上帝因大衛的緣故,仍使他在耶路撒冷有燈光,叫他兒子接續他作王,堅立耶路撒冷。
5 Gama Dawuda ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, bai kuma fasa kiyaye wani daga umarnan Ubangiji ba dukan kwanakinsa, sai dai a batun Uriya mutumin Hitti.
因為大衛除了赫人烏利亞那件事,都是行耶和華眼中看為正的事,一生沒有違背耶和華一切所吩咐的。
6 Aka yi yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam a duk kwanakin Abiya.
羅波安在世的日子常與耶羅波安爭戰。
7 Game da sauran ayyukan mulkin Abiyam kuwa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka yi yaƙi tsakanin Abiyam da Yerobowam.
亞比央其餘的事,凡他所行的,都寫在猶大列王記上。亞比央常與耶羅波安爭戰。
8 Sai Abiyam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
亞比央與他列祖同睡,葬在大衛的城裏。他兒子亞撒接續他作王。
9 A shekara ta ashirin ta Yerobowam sarkin Isra’ila, Asa ya zama sarkin Yahuda,
以色列王耶羅波安二十年,亞撒登基作猶大王,
10 ya yi mulki a Urushalima shekara arba’in da ɗaya. Sunan mahaifiya mahaifiyarsa, Ma’aka ne’yar Abisalom.
在耶路撒冷作王四十一年。他祖母名叫瑪迦,是押沙龍的女兒。
11 Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi.
亞撒效法他祖大衛行耶和華眼中看為正的事,
12 Ya kori dukan maza karuwai na masujadai daga ƙasar, ya kuma yi waje da dukan gumakan da mahaifinsa ya yi.
從國中除去孌童,又除掉他列祖所造的一切偶像;
13 Ya tuɓe mahaifiya mahaifiyarsa Ma’aka daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, gama ta gina ƙazantaccen ginshiƙin Ashera. Asa ya yanke ginshiƙin, ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron.
並且貶了他祖母瑪迦太后的位,因她造了可憎的偶像亞舍拉。亞撒砍下她的偶像,燒在汲淪溪邊,
14 Ko da yake bai cire masujadai da suke kan tuddai ba, zuciyar Asa ta kasance da aminci ɗungum ga Ubangiji dukan kwanakinsa.
只是邱壇還沒有廢去。亞撒一生卻向耶和華存誠實的心。
15 Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyakin da shi da mahaifinsa suka keɓe a haikalin Ubangiji.
亞撒將他父親所分別為聖與自己所分別為聖的金銀和器皿都奉到耶和華的殿裏。
16 Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu.
亞撒和以色列王巴沙在世的日子常常爭戰。
17 Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda.
以色列王巴沙上來要攻擊猶大,修築拉瑪,不許人從猶大王亞撒那裏出入。
18 Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus.
於是亞撒將耶和華殿和王宮府庫裏所剩下的金銀都交在他臣僕手中,打發他們往住大馬士革的亞蘭王-希旬的孫子、他伯利們的兒子便‧哈達那裏去,
19 Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.”
說:「你父曾與我父立約,我與你也要立約。現在我將金銀送你為禮物,求你廢掉你與以色列王巴沙所立的約,使他離開我。」
20 Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali.
便‧哈達聽從亞撒王的話,派軍長去攻擊以色列的城邑;他們就攻破以雲、但、亞伯‧伯‧瑪迦、基尼烈全境、拿弗他利全境。
21 Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza.
巴沙聽見,就停工不修築拉瑪了,仍住在得撒。
22 Sai Sarki Asa ya ba da umarni ga dukan Yahuda, kuma babu wanda aka ware, kowa yă taimaka a kwashe duwatsu da katakan da Ba’asha yake amfani da su daga Rama. Da duwatsu da katakan ne Sarki Asa ya gina Geba a Benyamin da kuma Mizfa.
於是亞撒王宣告猶大眾人,不准一個推辭,吩咐他們將巴沙修築拉瑪所用的石頭、木頭都運去,用以修築便雅憫的迦巴和米斯巴。
23 Game da sauran ayyukan mulkin Asa, dukan nasarorinsa, dukan abin da ya yi, da kuma biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. A tsufansa, sai ƙafafunsa suka kamu da cuta.
亞撒其餘的事,凡他所行的,並他的勇力與他所建築的城邑,都寫在猶大列王記上。亞撒年老的時候,腳上有病。
24 Sai Asa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin kakansa Dawuda. Sai Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
亞撒與他列祖同睡,葬在他祖大衛城他列祖的墳地裏。他兒子約沙法接續他作王。
25 Nadab ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a shekara ta biyu ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekara biyu.
猶大王亞撒第二年,耶羅波安的兒子拿答登基作以色列王共二年,
26 Ya yi mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin mahaifinsa da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi.
拿答行耶和華眼中看為惡的事,行他父親所行的,犯他父親使以色列人陷在罪裏的那罪。
27 Ba’asha ɗan Ahiya na gidan Issakar ya yi maƙarƙashiya gāba da shi, ya buge shi a Gibbeton, a wani garin Filistiyawa, yayinda Nadab da dukan Isra’ila suke wa garin kwanto.
以薩迦人亞希雅的兒子巴沙背叛拿答,在非利士的基比頓殺了他。那時拿答和以色列眾人正圍困基比頓。
28 Ba’asha ya kashe Nadab a shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma gāje shi a matsayin sarki.
在猶大王亞撒第三年巴沙殺了他,篡了他的位。
29 Nan da nan da ya fara mulki, sai ya kashe dukan iyalin Yerobowam. Bai bar wa Yerobowam wani da rai ba, amma ya hallaka su duka, bisa ga maganar Ubangiji da ya ba wa bawansa Ahiya, mutumin Shilo.
巴沙一作王就殺了耶羅波安的全家,凡有氣息的沒有留下一個,都滅盡了,正應驗耶和華藉他僕人示羅人亞希雅所說的話。
30 Wannan abu ya faru saboda zunuban da Yerobowam ya yi, ya kuma sa Isra’ila ya yi, kuma saboda ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya yi fushi.
這是因為耶羅波安所犯的罪使以色列人陷在罪裏,惹動耶和華-以色列上帝的怒氣。
31 Game da sauran ayyukan mulkin Nadab da kuma dukan abin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.
拿答其餘的事,凡他所行的,都寫在以色列諸王記上。
32 Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu.
亞撒和以色列王巴沙在世的日子常常爭戰。
33 A shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, Ba’asha ɗan Ahiya ya zama sarkin dukan Isra’ila a Tirza, ya kuma yi sarauta shekara ashirin da huɗu.
猶大王亞撒第三年,亞希雅的兒子巴沙在得撒登基作以色列眾人的王共二十四年。
34 Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi.
他行耶和華眼中看為惡的事,行耶羅波安所行的道,犯他使以色列人陷在罪裏的那罪。

< 1 Sarakuna 15 >