< 1 Sarakuna 11 >

1 Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa.
והמלך שלמה אהב נשים נכריות רבות--ואת בת פרעה מואביות עמניות אדמית צדנית חתית
2 Sun fito daga al’ummai da Ubangiji ya ce wa Isra’ilawa, “Kada ku yi aurayya da su, domin tabbatacce za su juye zukatanku zuwa ga waɗansu alloli.” Duk da haka Solomon ya manne musu, ya nace, yana ƙaunarsu.
מן הגוים אשר אמר יהוה אל בני ישראל לא תבאו בהם והם לא יבאו בכם אכן יטו את לבבכם אחרי אלהיהם--בהם דבק שלמה לאהבה
3 Ya auri mata ɗari bakwai, haifaffun gidan sarauta, da kuma ƙwarƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa suka karkatar da shi.
ויהי לו נשים שרות שבע מאות ופלגשים שלש מאות ויטו נשיו את לבו
4 Yayinda Solomon yake tsufa, matansa suka juye zuciyarsa ga bin waɗansu alloli, zuciyarsa kuwa ba tă bi Ubangiji Allahnsa ɗungum kamar yadda zuciyar Dawuda mahaifinsa ta kasance ba.
ויהי לעת זקנת שלמה נשיו הטו את לבבו אחרי אלהים אחרים ולא היה לבבו שלם עם יהוה אלהיו כלבב דויד אביו
5 Ya bi Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa.
וילך שלמה--אחרי עשתרת אלהי צדנים ואחרי מלכם שקץ עמנים
6 Saboda haka Solomon ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Bai bi Ubangiji gaba ɗaya kamar yadda Dawuda mahaifinsa ya yi ba.
ויעש שלמה הרע בעיני יהוה ולא מלא אחרי יהוה כדוד אביו
7 A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa.
אז יבנה שלמה במה לכמוש שקץ מואב בהר אשר על פני ירושלם ולמלך שקץ בני עמון
8 Ya yi haka domin dukan baƙin matansa, waɗanda suka ƙone turare suka kuma miƙa hadayu ga allolinsu.
וכן עשה לכל נשיו הנכריות מקטירות ומזבחות לאלהיהן
9 Ubangiji ya yi fushi da Solomon domin zuciyarsa ya juye daga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bayyana masa sau biyu.
ויתאנף יהוה בשלמה כי נטה לבבו מעם יהוה אלהי ישראל הנראה אליו פעמים
10 Ko da yake ya hana Solomon bin waɗansu alloli, Solomon bai kiyaye umarnin Ubangiji ba.
וצוה אליו על הדבר הזה לבלתי לכת אחרי אלהים אחרים ולא שמר את אשר צוה יהוה
11 Saboda haka Ubangiji ya ce wa Solomon, “Da yake halinka ke nan, ba ka kuma kiyaye alkawarina, da ƙa’idodina da na umarce ka ba, tabbatacce zan yage masarautar daga gare ka, in ba da ita ga ɗaya daga cikin bayinka.
ויאמר יהוה לשלמה יען אשר היתה זאת עמך ולא שמרת בריתי וחקתי אשר צויתי עליך--קרע אקרע את הממלכה מעליך ונתתיה לעבדך
12 Amma saboda Dawuda mahaifinka, ba zan yi haka a zamaninka ba. Zan yage ta daga hannun ɗanka.
אך בימיך לא אעשנה למען דוד אביך מיד בנך אקרענה
13 Amma ba zan yage dukan masarautar daga gare shi ba, zan ba shi kabila ɗaya saboda Dawuda bawana, da kuma saboda Urushalima, wadda na zaɓa.”
רק את כל הממלכה לא אקרע שבט אחד אתן לבנך למען דוד עבדי ולמען ירושלם אשר בחרתי
14 Sai Ubangiji ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Hadad, mutumin Edom daga gidan sarautar Edom.
ויקם יהוה שטן לשלמה את הדד האדמי מזרע המלך הוא באדום
15 A shekarun baya Dawuda ya ci Edom da yaƙi. Yowab, shugaban sojojinsa ya tafi can domin yă binne Isra’ilawa waɗanda suka mutu a yaƙi. Sa’ad da suke a can, sojojin Isra’ila suka kashe kowane ɗa namiji a Edom.
ויהי בהיות דוד את אדום בעלות יואב שר הצבא לקבר את החללים ויך כל זכר באדום
16 Yowab da dukan Isra’ilawa suka zauna a can, wata shida, sai da suka hallaka dukan mutane a Edom.
כי ששת חדשים ישב שם יואב וכל ישראל עד הכרית כל זכר באדום
17 Amma Hadad yana ɗan yaro a lokaci, wanda ya gudu zuwa Masar tare da shugabannin mutanen Edom waɗanda suka yi wa mahaifinsa hidima.
ויברח אדד הוא ואנשים אדמיים מעבדי אביו אתו--לבוא מצרים והדד נער קטן
18 Suka taso daga Midiyan suka tafi Faran. Sa’an nan suka ɗauki mutane daga Faran suka tafi Masar, zuwa wurin Fir’auna wanda ya ba wa Hadad gida da ƙasa, ya kuma tanada masa da abinci.
ויקמו ממדין ויבאו פארן ויקחו אנשים עמם מפארן ויבאו מצרים אל פרעה מלך מצרים ויתן לו בית ולחם אמר לו וארץ נתן לו
19 Fir’auna ya ji daɗin Hadad har ya ba shi’yar’uwar matarsa, Sarauniya Tafenes, aure.
וימצא הדד חן בעיני פרעה מאד ויתן לו אשה את אחות אשתו אחות תחפניס הגבירה
20 ’Yar’uwar Tafenes ta haifi masa ɗa wanda ya kira Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a fadan sarki. A can, Genubat ya yi zama da’ya’yan Fir’auna.
ותלד לו אחות תחפניס את גנבת בנו ותגמלהו תחפנס בתוך בית פרעה ויהי גנבת בית פרעה בתוך בני פרעה
21 Yayinda yake a Masar, Hadad ya ji Dawuda ya huta tare da kakanninsa, ya kuma ji cewa Yowab shugaban mayaƙa ya mutu. Sai Hadad ya ce wa Fir’auna, “Bari in tafi, don in koma ƙasata.”
והדד שמע במצרים כי שכב דוד עם אבתיו וכי מת יואב שר הצבא ויאמר הדד אל פרעה שלחני ואלך אל ארצי
22 Fir’auna ya tambaye shi, ya ce, “Me ka rasa a nan da kake so ka koma garinka?” Ya ce, “Ba kome, amma ka dai bar ni in tafi!”
ויאמר לו פרעה כי מה אתה חסר עמי והנך מבקש ללכת אל ארצך ויאמר לא כי שלח תשלחני
23 Allah kuwa ya tayar wa Solomon wani abokin gāba, mai suna Rezon, ɗan Eliyada, wanda ya gudu daga maigidansa, Hadadezer sarkin Zoba.
ויקם אלהים לו שטן את רזון בן אלידע אשר ברח מאת הדדעזר מלך צובה--אדניו
24 Rezon ya tattara mutane kewaye da shi, ya zama kuma shugaban’yan tawaye sa’ad da Dawuda ya hallaka mayaƙan Zoba;’yan tawayen suka tafi Damaskus, inda suka zauna, suka kuma yi mulki.
ויקבץ עליו אנשים ויהי שר גדוד בהרג דוד אתם וילכו דמשק וישבו בה וימלכו בדמשק
25 Rezon ya zama babban abokin gāban Isra’ila cikin dukan kwanakin mulkin Solomon. Ya ƙara rikici a kan rikicin Hadad. Rezon ya ƙi mulkin Isra’ila da dukan ransa. Saboda haka Rezon ya yi mulki a Aram ya kuma ƙi jinin Isra’ila.
ויהי שטן לישראל כל ימי שלמה ואת הרעה אשר הדד ויקץ בישראל וימלך על ארם
26 Haka ma Yerobowam, ɗan Nebat, shi ma ya yi wa sarki tawaye. Shi ɗaya ne daga shugabannin Solomon, shi mutumin Efraim ne daga Zereda, mahaifiyarsa kuwa gwauruwa ce, mai suna Zeruwa.
וירבעם בן נבט אפרתי מן הצרדה ושם אמו צרועה אשה אלמנה עבד לשלמה וירם יד במלך
27 Ga yadda ya tayar wa sarki Solomon. Sarki Solomon ya gina madogaran gini, ya ciccika wurare a katangar birnin Dawuda mahaifinsa da ƙasa.
וזה הדבר אשר הרים יד במלך שלמה בנה את המלוא--סגר את פרץ עיר דוד אביו
28 To, Yerobowam mutum ne mai fasaha. Sa’ad da Solomon ya ga yadda matashin yake aiki da himma, sai ya sa shi yă lura da dukan aikin gandu na gidan Yusuf.
והאיש ירבעם גבור חיל וירא שלמה את הנער כי עשה מלאכה הוא ויפקד אתו לכל סבל בית יוסף
29 Da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahiya, mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahiya yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai.
ויהי בעת ההיא וירבעם יצא מירושלם וימצא אתו אחיה השילני הנביא בדרך והוא מתכסה בשלמה חדשה ושניהם לבדם בשדה
30 Sai Ahiya ya kama sabuwar rigar da yake saye da ita ya yage ta gida goma sha biyu.
ויתפש אחיה בשלמה החדשה אשר עליו ויקרעה--שנים עשר קרעים
31 Sa’an nan ya ce wa Yerobowam, “Ɗauki gida goma wa kanka, gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce ke nan, ‘Duba, zan yage masarauta daga hannun Solomon in ba ka kabilu goma.
ויאמר לירבעם קח לך עשרה קרעים כי כה אמר יהוה אלהי ישראל הנני קרע את הממלכה מיד שלמה ונתתי לך את עשרה השבטים
32 Amma saboda bawana Dawuda da kuma birnin Urushalima, wadda na zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila, zai sami kabila guda.
והשבט האחד יהיה לו--למען עבדי דוד ולמען ירושלם העיר אשר בחרתי בה מכל שבטי ישראל
33 Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba.
יען אשר עזבוני וישתחוו לעשתרת אלהי צדנין לכמוש אלהי מואב ולמלכם אלהי בני עמון ולא הלכו בדרכי לעשות הישר בעיני וחקתי ומשפטי--כדוד אביו
34 “‘Amma ba zan ɗauki dukan masarautar daga hannun Solomon ba; na naɗa shi sarki, dukan kwanaki ransa saboda Dawuda bawana, wanda na zaɓa, wanda kuma ya kiyaye umarnai da farillaina.
ולא אקח את כל הממלכה מידו כי נשיא אשתנו כל ימי חייו למען דוד עבדי אשר בחרתי אתו אשר שמר מצותי וחקתי
35 Zan ɗauke masarautar daga hannuwan ɗansa ne, in ba ka kabilu goma.
ולקחתי המלוכה מיד בנו ונתתיה לך את עשרת השבטים
36 Zan ba da ɗaya ga ɗansa don kullum Dawuda bawana yă kasance da fitila a gabana a Urushalima, birnin da na zaɓa in sa Sunana.
ולבנו אתן שבט אחד--למען היות ניר לדויד עבדי כל הימים לפני בירושלם העיר אשר בחרתי לי לשום שמי שם
37 Amma fa, ga kai, zan ɗauke ka, za ka kuwa yi mulki bisa dukan abin da zuciyarka take so; za ka zama sarki a bisa Isra’ila.
ואתך אקח--ומלכת בכל אשר תאוה נפשך והיית מלך על ישראל
38 In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka.
והיה אם תשמע את כל אשר אצוך והלכת בדרכי ועשית הישר בעיני לשמור חקותי ומצותי כאשר עשה דוד עבדי--והייתי עמך ובניתי לך בית נאמן כאשר בניתי לדוד ונתתי לך את ישראל
39 Zan ƙasƙantar da zuriyar Dawuda saboda wannan, amma ba har abada ba.’”
ואענה את זרע דוד למען זאת--אך לא כל הימים
40 Solomon ya yi ƙoƙari yă kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tsere zuwa Masar, zuwa wurin sarki Shishak, ya zauna a can sai bayan mutuwar Solomon.
ויבקש שלמה להמית את ירבעם ויקם ירבעם ויברח מצרים אל שישק מלך מצרים ויהי במצרים עד מות שלמה
41 Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, da dukan abubuwan da ya yi, da hikimar da ya nuna, an rubuta su a littafin tarihin Solomon.
ויתר דברי שלמה וכל אשר עשה וחכמתו--הלוא הם כתבים על ספר דברי שלמה
42 Solomon ya yi mulki a Urushalima, a bisa dukan Isra’ila, shekaru arba’in.
והימים אשר מלך שלמה בירושלם על כל ישראל--ארבעים שנה
43 Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda mahaifinsa. Sai Rehobowam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
וישכב שלמה עם אבתיו ויקבר בעיר דוד אביו וימלך רחבעם בנו תחתיו

< 1 Sarakuna 11 >