< 1 Sarakuna 1 >
1 Sa’ad da Sarki Dawuda ya tsufa ya kuma ƙara shekaru, ba ya iya jin ɗumi ko an rufe shi da abin rufuwa.
大衛王年紀老邁,雖用被遮蓋,仍不覺暖。
2 Saboda haka bayinsa suka ce masa, “Bari mu nemi wata budurwa wadda za tă yi wa ranka yă daɗe, sarki hidima, tă kuma kula da shi. Za tă dinga kwanta kusa da ranka yă daɗe, yă ji ɗumi.”
所以臣僕對他說:「不如為我主我王尋找一個處女,使她伺候王,奉養王,睡在王的懷中,好叫我主我王得暖。」
3 Suka nemi kyakkyawar yarinya cikin fāɗin Isra’ila, sai suka sami Abishag, mutuniyar Shunam, suka kawo ta wa sarki.
於是在以色列全境尋找美貌的童女,尋得書念的一個童女亞比煞,就帶到王那裏。
4 Yarinyar kuwa kyakkyawa ce ƙwarai; ta kuwa lura da sarki, ta kuma yi masa hidima, amma sarki bai yi jima’i da ita ba.
這童女極其美貌,她奉養王,伺候王,王卻沒有與她親近。
5 Adoniya, wanda mahaifiyarsa ce Haggit, ya fito ya ce, “Zan zama sarki.” Saboda haka ya nemi kekunan yaƙi, ya kuma shirya dawakai, tare da mutane hamsin da za su sha gabansa.
那時,哈及的兒子亞多尼雅自尊,說:「我必作王」,就為自己預備車輛、馬兵,又派五十人在他前頭奔走。
6 (A duk rayuwarsa mahaifinsa bai taɓa tsawata masa yă ce, “Me ya sa kake yin haka ba?” Shi kuwa mai kyan gani ne ƙwarai, shi ne aka haifa bayan Absalom.)
他父親素來沒有使他憂悶,說:「你是做甚麼呢?」他甚俊美,生在押沙龍之後。
7 Adoniya ya haɗa baƙi da Yowab ɗan Zeruhiya da kuma Abiyatar firist, suka kuma ba shi goyon baya.
亞多尼雅與洗魯雅的兒子約押,和祭司亞比亞他商議;二人就順從他,幫助他。
8 Amma Zadok firist, Benahiya ɗan Yehohiyada, annabi Natan, Shimeyi, Reyi da kuma matsara na musamman na Dawuda ba su bi Adoniya ba.
但祭司撒督、耶何耶大的兒子比拿雅、先知拿單、示每、利以,並大衛的勇士都不順從亞多尼雅。
9 Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci’yan’uwansa, wato, sauran’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda,
一日,亞多尼雅在隱‧羅結旁、瑣希列磐石那裏宰了牛羊、肥犢,請他的諸弟兄,就是王的眾子,並所有作王臣僕的猶大人;
10 amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benahiya, ko wani daga matsara na musamman, ko kuwa ɗan’uwansa Solomon ba.
惟獨先知拿單和比拿雅並勇士,與他的兄弟所羅門,他都沒有請。
11 Sai Natan ya ce wa Batsheba, mahaifiyar Solomon, “Ki san cewa Adoniya, ɗan Haggit, ya zama sarki ba tare da sanin ranka yă daɗe, sarkinmu Dawuda ba?
拿單對所羅門的母親拔示巴說:「哈及的兒子亞多尼雅作王了,你沒有聽見嗎?我們的主大衛卻不知道。
12 Yanzu bari in ba ki shawara yadda za ki cece ranki da kuma ran ɗanki Solomon.
現在我可以給你出個主意,好保全你和你兒子所羅門的性命。
13 Ki shiga wurin Sarki Dawuda ki ce masa, ‘Ranka yă daɗe sarki, ba ka rantse mini ni baiwarka cewa, “Tabbatacce Solomon ɗanka ne zai zama sarki bayana, yă kuma zauna a kujerar sarautar ba”? To, me ya sa Adoniya ya zama sarki?’
你進去見大衛王,對他說:『我主我王啊,你不曾向婢女起誓說:你兒子所羅門必接續我作王,坐在我的位上嗎?現在亞多尼雅怎麼作了王呢?』
14 Yayinda kike can kina magana da sarki, zan shiga in kuma tabbatar da abin da kika faɗa.”
你還與王說話的時候,我也隨後進去,證實你的話。」
15 Saboda haka Batsheba ta je don tă ga sarki. A yanzu dai sarki ya tsufa, yana nan kuma a cikin ɗakinsa, inda Abishag mutuniya Shunam take masa hidima.
拔示巴進入內室見王,王甚老邁,書念的童女亞比煞正伺候王。
16 Batsheba ta rusuna ta kuma durƙusa a gaban sarki. Sai sarki ya tambaye ta ya ce, “Me kike so?”
拔示巴向王屈身下拜;王說:「你要甚麼?」
17 Ta ce masa, “Ranka yă daɗe, kai kanka ka rantse mini ni baiwarka da sunan Ubangiji Allahnka cewa, ‘Solomon ɗanka zai zama sarki bayana, zai kuma zauna a kujerar sarautata.’
她說:「我主啊,你曾向婢女指着耶和華-你的上帝起誓說:『你兒子所羅門必接續我作王,坐在我的位上。』
18 Amma yanzu Adoniya ya zama sarki, kai kuwa ranka yă daɗe sarki, ba ka san wani abu game da shi ba.
現在亞多尼雅作王了,我主我王卻不知道。
19 Ya miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa, ya kuma gayyaci dukan’ya’yan sarki maza, da Abiyatar firist, da Yowab shugaban mayaƙa, amma bai gayyaci Solomon bawanka ba.
他宰了許多牛羊、肥犢,請了王的眾子和祭司亞比亞他,並元帥約押;惟獨王的僕人所羅門,他沒有請。
20 Ranka yă daɗe sarki, idanun dukan Isra’ila suna a kanka, domin su san wa zai zauna a kujerar ranka yă daɗe sarkina, a bayanka.
我主我王啊,以色列眾人的眼目都仰望你,等你曉諭他們,在我主我王之後誰坐你的位。
21 In ba haka, bayan an binne ranka yă daɗe sarki, tare da kakanninsa, za a wulaƙance ni da Solomon ɗana, kamar masu laifi.”
若不然,到我主我王與列祖同睡以後,我和我兒子所羅門必算為罪人了。」
22 Yayinda take cikin magana tare da sarki, sai annabi Natan ya iso.
拔示巴還與王說話的時候,先知拿單也進來了。
23 Sai aka faɗa wa sarki, “Ga annabi Natan.” Da Natan ya je gaban sarki, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.
有人奏告王說:「先知拿單來了。」拿單進到王前,臉伏於地。
24 Natan ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki, ko ka furta cewa Adoniya ne zai zama sarki a bayanka, yă kuma zauna a kujerar sarautarka?
拿單說:「我主我王果然應許亞多尼雅說『你必接續我作王,坐在我的位上』嗎?
25 Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’
他今日下去,宰了許多牛羊、肥犢,請了王的眾子和軍長,並祭司亞比亞他;他們正在亞多尼雅面前吃喝,說:『願亞多尼雅王萬歲!』
26 Amma bai gayyace ni bawanka, da Zadok firist, da Benahiya ɗan Yehohiyada, da kuma bawanka Solomon ba.
惟獨我,就是你的僕人和祭司撒督,耶何耶大的兒子比拿雅,並王的僕人所羅門,他都沒有請。
27 Ranka yă daɗe, sarki, ko ka tabbatar da haka, amma ba ka ko faɗa wa fadawanka, cewa ga wanda zai gāje Ranka yă daɗe, sarki ba?”
這事果然出乎我主我王嗎?王卻沒有告訴僕人們,在我主我王之後誰坐你的位。」
28 Sai Dawuda ya ce, “Kira Batsheba tă shiga.” Sai ta zo gaban sarki ta kuma tsaya a gabansa.
大衛王吩咐說:「叫拔示巴來。」拔示巴就進來,站在王面前。
29 Sai sarki ya yi rantsuwa, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya cece ni daga kowace damuwa,
王起誓說:「我指着救我性命脫離一切苦難、永生的耶和華起誓。
30 tabbatacce a yau zan aikata abin da na yi miki rantsuwa da sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila; Solomon ɗanki zai zama sarki bayana, kuma shi zai zauna a kan kujerar sarautata a maimakona.”
我既然指着耶和華-以色列的上帝向你起誓說:你兒子所羅門必接續我作王,坐在我的位上。我今日就必照這話而行。」
31 Sai Batsheba ta rusuna da fuskarta har ƙasa, ta kuma durƙusa a gaban sarki ta ce, “Bari ran Sarkina Dawuda yă daɗe, har abada!”
於是,拔示巴臉伏於地,向王下拜,說:「願我主大衛王萬歲!」
32 Sarki Dawuda ya ce, “Ku kira mini Zadok firist, annabi Natan, da Benahiya ɗan Yehohiyada.” Da suka zo gaban sarki,
大衛王又吩咐說:「將祭司撒督、先知拿單、耶何耶大的兒子比拿雅召來!」他們就都來到王面前。
33 sai ya ce musu, “Ku ɗauki bayin sarki tare da ku, ku kuma sa ɗana Solomon a kan dokina, ku gangara da shi zuwa Gihon.
王對他們說:「要帶領你們主的僕人,使我兒子所羅門騎我的騾子,送他下到基訓;
34 A can ku sa Zadok firist, da annabi Natan su shafe shi sarki a bisa Isra’ila. Ku busa ƙaho, ku kuma yi ihu, kuna cewa, ‘Ran Sarki Solomon yă daɗe!’
在那裏,祭司撒督和先知拿單要膏他作以色列的王;你們也要吹角,說:『願所羅門王萬歲!』
35 Sa’an nan ku haura tare da shi, zai kuwa zo yă zauna a kujera sarautata, yă yi mulki a maimakona. Na naɗa shi mai mulki a bisa Isra’ila da Yahuda.”
然後要跟隨他上來,使他坐在我的位上,接續我作王。我已立他作以色列和猶大的君。」
36 Benahiya ɗan Yehohiyada ya amsa wa sarki, ya ce, “Amin! Bari Ubangiji Allah na ranka yă daɗe sarkina, yă tabbatar da haka.
耶何耶大的兒子比拿雅對王說:「阿們!願耶和華-我主我王的上帝也這樣命定。
37 Kamar yadda Ubangiji ya kasance da ranka yă daɗe, sarki, haka ma bari yă kasance da Solomon, yă kuma mai da kujerar sarautarsa tă fi kujerar sarautar ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, girma!”
耶和華怎樣與我主我王同在,願他照樣與所羅門同在,使他的國位比我主大衛王的國位更大。」
38 Sai Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa suka gangara, suka sa Solomon a kan dokin Sarki Dawuda, suka raka shi zuwa Gihon.
於是,祭司撒督、先知拿單、耶何耶大的兒子比拿雅,和基利提人、比利提人都下去使所羅門騎大衛王的騾子,將他送到基訓。
39 Zadok firist ya ɗauki ƙahon mai daga tenti mai tsarki, ya shafe Solomon. Sa’an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka yi ihu, suna cewa “Ran Sarki Solomon yă daɗe!”
祭司撒督就從帳幕中取了盛膏油的角來,用膏膏所羅門。人就吹角,眾民都說:「願所羅門王萬歲!」
40 Dukan mutane kuwa suka haura suka bi shi, suna busan sarewa, suna farin ciki sosai, har ƙasa ta girgiza saboda sowa.
眾民跟隨他上來,且吹笛,大大歡呼,聲音震地。
41 Adoniya tare da dukan baƙin da suke tare da shi kuwa suka ji wannan sa’ad da suke gama bikinsu. Da jin busan ƙaho, sai Yowab ya yi tambaya, ya ce, “Me ya jawo surutu haka a birni?”
亞多尼雅和所請的眾客筵宴方畢,聽見這聲音;約押聽見角聲就說:「城中為何有這響聲呢?」
42 Tun yana cikin magana, sai Yonatan ɗan Abiyatar ya iso. Adoniya ya ce, “Shigo! Ai, mutumin kirki irinka, lalle ka kawo labari mai daɗi ne.”
他正說話的時候,祭司亞比亞他的兒子約拿單來了。亞多尼雅對他說:「進來吧!你是個忠義的人,必是報好信息。」
43 Yonatan ya ce wa Adoniya, “A ina! Ranka yă daɗe, Sarkinmu Dawuda ya naɗa Solomon sarki.
約拿單對亞多尼雅說:「我們的主大衛王誠然立所羅門為王了。
44 Sarki ya aika shi tare da Zadok firist, annabi Natan, Benahiya ɗan Yehohiyada, Keretawa, da Feletiyawa, suka sa shi a kan dokin sarki,
王差遣祭司撒督、先知拿單、耶何耶大的兒子比拿雅,和基利提人、比利提人都去使所羅門騎王的騾子。
45 Zadok firist kuwa da annabi Natan sun shafe shi sarki a Gihon. Daga can suka haura suna kirari, birni kuwa ta ɓarke da sowa. Surutun da kake ji ke nan.
祭司撒督和先知拿單在基訓已經膏他作王。眾人都從那裏歡呼着上來,聲音使城震動,這就是你們所聽見的聲音;
46 Ban da haka ma, Solomon ne sarki yanzu.
並且所羅門登了國位。
47 Yanzu haka, fadawa sun zo suna wa ranka yă daɗe, Sarki Dawuda, sam barka, suna cewa, ‘Bari Allahnka yă sa sunan Solomon yă zama sananne fiye da naka, bari kuma sarautarsa tă fi taka girma!’ Sarki kuwa ya rusuna, ya yi sujada a kan gadonsa
王的臣僕也來為我們的主大衛王祝福,說:『願王的上帝使所羅門的名比王的名更尊榮;使他的國位比王的國位更大。』王就在床上屈身下拜。
48 ya ce, ‘Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bar idanuna suka ga magāji a kan kujerar sarautata a yau.’”
王又說:『耶和華-以色列的上帝是應當稱頌的;因他賜我一人今日坐在我的位上,我也親眼看見了。』」
49 A nan fa, dukan baƙin Adoniya suka taso da rawar jiki suka watse.
亞多尼雅的眾客聽見這話就都驚懼,起來四散。
50 Amma Adoniya, don tsoron Solomon, ya je ya kama ƙahon bagade ya riƙe.
亞多尼雅懼怕所羅門,就起來,去抓住祭壇的角。
51 Sa’ad da aka faɗa wa Solomon cewa, “Adoniya yana tsoron Sarki Solomon, kuma ya manne wa ƙahonin bagade. Yana cewa, ‘Bari Sarki Solomon yă rantse mini a yau cewa ba zai kashe bawansa da takobi ba.’”
有人告訴所羅門說:「亞多尼雅懼怕所羅門王,現在抓住祭壇的角,說:『願所羅門王今日向我起誓,必不用刀殺僕人。』」
52 Solomon ya amsa ya ce, “In ya nuna kansa mai biyayya, ba gashin kansa da zai fāɗi ƙasa; amma in aka same mugunta a cikinsa, zai mutu.”
所羅門說:「他若作忠義的人,連一根頭髮也不致落在地上;他若行惡,必要死亡。」
53 Sai Sarki Solomon ya aiki mutane, suka kuma sauko da shi daga bagade. Adoniya kuwa ya zo, ya rusuna wa Sarki Solomon, sai Solomon ya ce, “Tafi gidanka.”
於是所羅門王差遣人,使亞多尼雅從壇上下來,他就來,向所羅門王下拜;所羅門對他說:「你回家去吧!」