< 1 Yohanna 1 >

1 Wannan da ya kasance tun farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, wannan ne muke shela game da Kalman rai.
That which was from the beginning, which we have heard, which we have seen with our eyes, which we have contemplated, and our very hands have felt concerning the Word of life,
2 Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu. (aiōnios g166)
(for this Life was manifested, and we saw it; and we testify and declare unto you that eternal Life, which was with the Father, (aiōnios g166)
3 Muna yin muku shelar abin da muka gani, muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi.
and was manifested unto us) what we have seen and heard we declare unto you, that ye also may have communion with us: and our communion is with the Father and with his Son Jesus Christ.
4 Muna rubuta wannan domin farin cikinmu yă zama cikakke.
And these things we write unto you, that your joy may be complete.
5 Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan.
Now this we have heard from Him, and declare unto you, that God is light, and in Him there is no darkness at all.
6 In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya.
If we say that we have communion with Him, and walk in darkness, we lie and do not practise the truth:
7 Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi.
but if we walk in the light, as He is in the light, we have communion with one another, and the blood of Jesus Christ his Son cleanseth us from all sin.
8 In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu.
If we say that we have no sin, we deceive ourselves, and the truth is not in us.
9 In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.
If we confess our sins, He is faithful and just to forgive us our sins, and to cleanse us from all unrighteousness:
10 In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.
but if we say that we have not sinned, we make him a liar, and his word is not in us.

< 1 Yohanna 1 >