< 1 Yohanna 2 >
1 ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci.
2 Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.
3 Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa.
4 Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa.
5 Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa.
6 Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.
7 Abokaina ƙaunatattu, ba sabon umarni nake rubuta muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne, wanda kuke da shi tun farko. Wannan tsohon umarni shi ne saƙon da kuka riga kuka ji.
8 Duk da haka ina rubuta muku sabon umarni; ana ganin gaskiyar umarnin a cikinsa da kuma cikinku, gama duhu yana shuɗewa, haske na gaskiya kuwa yana haskakawa.
9 Duk wanda ya ce yana cikin haske yana kuma ƙin ɗan’uwansa, ashe a duhu yake har yanzu.
10 Duk wanda yake ƙaunar ɗan’uwansa, a cikin hasken yake rayuwa ke nan, kuma babu wani abin da yake cikinsa da zai sa yă yi tuntuɓe.
11 Amma duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, cikin duhu yake, yana kuma tafiya cikin duhu ke nan; bai ma san inda za shi ba, domin duhun ya makanta shi.
12 Ina rubuta muku,’ya’yana ƙaunatattu, domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.
13 Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kun ci nasara a kan mugun nan.
14 Ina rubuta muku,’ya’yana ƙaunatattu, domin kun san Uba. Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kuna da ƙarfi, maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku, kun kuma ci nasara a kan mugun nan.
15 Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa.
16 Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.
17 Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada. (aiōn )
18 ’Ya’yana ƙaunatattu, waɗannan su ne kwanakin ƙarshe; kuma kamar yadda kuka ji cewa magabcin Kiristi yana zuwa, ko yanzu ma abokan gāban Kiristi da yawa sun zo. Ta haka muka san cewa kwanakin ƙarshe sun iso.
19 Waɗannan masu gāba da Kiristi suna cikinmu a dā, amma sun bar mu, don tun dā ma su ba namu ba ne. Ai, da su namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun bar mu, wannan ya nuna a fili cewa su ba namu ba ne.
20 Amma ku kam, kuna da shafewa daga wurin Mai Tsarkin nan, kuma dukanku kun san gaskiya.
21 Ina rubuta muku ba domin ba ku san gaskiya ba ne, a’a, sai dai domin kun santa, kun kuma san cewa babu yadda ƙarya za tă fito daga gaskiya.
22 Wane ne maƙaryaci? Ai, shi ne mutumin da yake mūsun cewa Yesu shi ne Kiristi. Irin wannan mutum shi ne magabcin Kiristi, ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan.
23 Ba wanda yake mūsun Ɗan, sa’an nan yă ce yana da Uban; duk wanda ya yarda da Ɗan, yana da Uban a cikinsa ke nan.
24 Ku lura fa cewa abin da kuka ji daga farko, bari yă ci gaba da kasance a cikinku. In kuwa ya ci gaba da zama a cikinku, za ku kasance a cikin Ɗan, da kuma a cikin Uban.
25 Wannan shi ne abin da ya yi mana alkawari, wato, rai madawwami. (aiōnios )
26 Ina rubuta muku waɗannan abubuwa ne game da waɗanda suke ƙoƙari su sa ku kauce.
27 Game da ku kuwa, shafan nan da kuka karɓa daga gare shi tana nan a cikinku, ba kwa kuma bukata wani yă koyar da ku. Amma kamar yadda shafan nan tasa tana koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.
28 Yanzu fa, ya ku’ya’yana ƙaunatattu, sai ku ci gaba a cikinsa, domin sa’ad da ya bayyana, mu iya tsaya gabagadi babu kunya a dawowarsa.
29 In kun san cewa shi mai adalci ne, to, kun dai san cewa duk mai aikata abin da yake daidai haifaffensa ne.