< 1 Korintiyawa 9 >
1 Ba ni da’yanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ni ban gan Yesu Ubangijinmu ba ne? Ba ku ne sakamakon aikina cikin Ubangiji ba?
2 Ko da waɗansu ba su ɗauke ni a matsayin manzo ba, tabbatacce, ni manzo ne a gare ku! Gama ku ne hatimin manzancina a gaban Ubangiji.
3 Wannan ita ce kāriyata ga waɗanda suke tuhumata game da manzancina.
4 Ba mu da’yancin ci da sha ne?
5 Ba mu da’yancin tafiya tare da matar da muka aura mai bi kamar sauran manzanni da’yan’uwan Ubangiji da kuma Kefas suke yi?
6 Ko ni da Barnabas ne kawai ba mu da’yanci a ɗauke mana aikin ci da kai?
7 Wa yake ciyar da kansa yayinda yake aikin soja? Wa yake shukar gonar inabi, da ba ya cin amfaninta? Wa yake kiwon garke, da ba ya sha madararsa?
8 Ina faɗin wannan bisa ga ra’ayin mutum kawai ne? Ashe, Doka ma ba tă faɗa haka ba?
9 Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi sa’ad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu sa’ad da ya ce haka?
10 Babu shakka, ya yi maganan nan saboda mu ne. Ko ba haka ba? I, an rubuta wannan saboda mu ne, domin sa’ad da mai noma yake noma, mai sussuka kuma yana sussuka, suna wannan ne da bege za su sami rabonsu daga girbin.
11 In muka shuka iri na ruhaniya a cikinku, ashe, bai kamata mu yi girbin abin biyan bukatarmu daga gare ku ba?
12 In waɗansu suna samun wannan taimako daga gare ku, ashe, mu ba mu fi cancanta mu samu ba? Amma ba mu yi amfani da wannan’yancin ba. A maimakon haka, mun jure da kome, domin kada mu hana bisharar Kiristi yaɗuwa.
13 Ashe, ba ku san cewa waɗanda suke hidima a haikali suna samun abincinsu daga haikali ba ne, waɗanda kuma suke hidima a bagade suna samun rabo a hadayar da suka miƙa ba ne?
14 Haka ma Ubangiji ya umarta cewa ya kamata waɗanda suke wa’azin bishara, su sami abin biyan bukatarsu daga bisharar.
15 Amma ban yi amfani da ko ɗaya daga cikin waɗannan’yancin ba. Ba kuma ina rubuta muku wannan da fata za ku yi mini waɗannan abubuwa ba ne. Gwamma in mutu, da wani yă hana ni wannan abin taƙama.
16 Duk da haka, sa’ad da ina wa’azin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi wa’azi. Kaitona, in ban yi wa’azin bishara ba!
17 In na yi wa’azi da yardar rai, ina da lada; in ba da yardar rai ba, ina dai cika amana da aka danƙa mini ne.
18 To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi wa’azin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da’yancina cikin wa’azin ba.
19 Ko da yake ina da’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa.
20 Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka.
21 Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar.
22 Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu.
23 Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.
24 Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada.
25 Duk’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama.
26 To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba.
27 A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.