< 1 Korintiyawa 8 >

1 To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina.
περι δε των ειδωλοθυτων οιδαμεν οτι παντες γνωσιν εχομεν η γνωσις φυσιοι η δε αγαπη οικοδομει
2 Mutumin da yake tsammani ya san abu, sanin da yake da shi bai isa ba.
ει δε τις δοκει ειδεναι τι ουδεπω ουδεν εγνωκεν καθως δει γνωναι
3 Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.
ει δε τις αγαπα τον θεον ουτος εγνωσται υπ αυτου
4 To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa, mun san cewa “Gunki ba kome ba ne a duniya”, kuma “Babu wani Allah sai dai ɗaya.”
περι της βρωσεως ουν των ειδωλοθυτων οιδαμεν οτι ουδεν ειδωλον εν κοσμω και οτι ουδεις θεος ετερος ει μη εις
5 Gama ko da akwai abubuwan da ake ce da su alloli, a sama ko a ƙasa (don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa),
και γαρ ειπερ εισιν λεγομενοι θεοι ειτε εν ουρανω ειτε επι της γης ωσπερ εισιν θεοι πολλοι και κυριοι πολλοι
6 duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.
αλλ ημιν εις θεος ο πατηρ εξ ου τα παντα και ημεις εις αυτον και εις κυριος ιησους χριστος δι ου τα παντα και ημεις δι αυτου
7 Amma ba kowa ne ya san wannan ba. Har yanzu, waɗansu mutane sun saba da tunani cewa gumaka ainihi ne, saboda haka sa’ad da suka ci irin abincin nan, sukan ɗauka cewa kamar an miƙa wa ga gunki ne, kuma da yake lamirinsu ba ƙarfi, yakan ƙazantu.
αλλ ουκ εν πασιν η γνωσις τινες δε τη συνειδησει του ειδωλου εως αρτι ως ειδωλοθυτον εσθιουσιν και η συνειδησις αυτων ασθενης ουσα μολυνεται
8 Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.
βρωμα δε ημας ου παριστησιν τω θεω ουτε γαρ εαν φαγωμεν περισσευομεν ουτε εαν μη φαγωμεν υστερουμεθα
9 Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi.
βλεπετε δε μηπως η εξουσια υμων αυτη προσκομμα γενηται τοις ασθενουσιν
10 Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba?
εαν γαρ τις ιδη σε τον εχοντα γνωσιν εν ειδωλειω κατακειμενον ουχι η συνειδησις αυτου ασθενους οντος οικοδομηθησεται εις το τα ειδωλοθυτα εσθιειν
11 Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka.
και απολειται ο ασθενων αδελφος επι τη ση γνωσει δι ον χριστος απεθανεν
12 Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan.
ουτως δε αμαρτανοντες εις τους αδελφους και τυπτοντες αυτων την συνειδησιν ασθενουσαν εις χριστον αμαρτανετε
13 Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe. (aiōn g165)
διοπερ ει βρωμα σκανδαλιζει τον αδελφον μου ου μη φαγω κρεα εις τον αιωνα ινα μη τον αδελφον μου σκανδαλισω (aiōn g165)

< 1 Korintiyawa 8 >