< 1 Korintiyawa 6 >

1 In wani a cikinku yana da damuwa da wani, don me zai kai ƙara a gaban marasa bi, maimakon yă kai ƙara a gaban tsarkaka?
Dare any of you, having a matter against another, go to be judged before the unjust, and not before the saints?
2 Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan.
Know you not that the saints shall judge this world? And if the world shall be judged by you, are you unworthy to judge the smallest matters?
3 Ba ku san cewa za mu yi wa mala’iku shari’a ba? Balle al’amuran da suka shafi duniyan nan!
Know you not that we shall judge angels? how much more things of this world?
4 Saboda haka, in kuna da damuwa game da irin waɗannan al’amura, sai ku naɗa alƙalai ko cikin waɗanda ba kome ba ne a ikkilisiya!
If therefore you have judgments of things pertaining to this world, set them to judge, who are the most despised in the church.
5 Na faɗi haka ne don ku ji kunya. Ashe, ba za a iya samun wani a cikinku mai hikima wanda zai iya sasanta tsakanin masu bi ba?
I speak to your shame. Is it so that there is not among you any one wise man, that is able to judge between his brethren?
6 Me zai sa ɗan’uwa yă kai ƙarar ɗan’uwa, a gaban marasa bi?
But brother goeth to law with brother, and that before unbelievers.
7 Ƙarar junanku ma da kuke yi, ai, kāsawa ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura ko an zambace ku?
Already indeed there is plainly a fault among you, that you have lawsuits one with another. Why do you not rather take wrong? Why do you not rather suffer yourselves to be defrauded?
8 Amma ga shi ku da kanku kuna cuta, kuna kuma zamba, har ma ga’yan’uwanku ne kuke yi wannan.
But you do wrong and defraud, and that to your brethren.
9 Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko’yan daudu,
Know you not that the unjust shall not possess the kingdom of God? Do not err: neither fornicators, nor idolaters, nor adulterers,
10 ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.
Nor the effeminate, nor liers with mankind, nor thieves, nor covetous, nor drunkards, nor railers, nor extortioners, shall possess the kingdom of God.
11 Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
And such some of you were; but you are washed, but you are sanctified, but you are justified in the name of our Lord Jesus Christ, and the Spirit of our God.
12 “Ina da dama in yi kome,” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ina da dama in yi kome” sai dai ba abin da zai mallake ni.
All things are lawful to me, but all things are not expedient. All things are lawful to me, but I will not be brought under the power of any.
13 “An yi abinci domin ciki ne, ciki kuma domin abinci.” Amma Allah zai hallaka su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.
Meat for the belly, and the belly for the meats; but God shall destroy both it and them: but the body is not for fornication, but for the Lord, and the Lord for the body.
14 Ta wurin ikonsa, Allah ya tashe Ubangiji daga matattu, haka zai tashe mu mu ma.
Now God hath both raised up the Lord, and will raise us up also by his power.
15 Ba ku sani ba cewa jikunanku gaɓoɓin Kiristi ne kansa? Zai kyautu in ɗauki gaɓoɓin Kiristi in haɗa da jikin karuwa? Sam!
Know you not that your bodies are the members of Christ? Shall I then take the members of Christ, and make them the members of an harlot? God forbid.
16 Ba ku san cewa shi wanda ya haɗa jikinsa da karuwa sun zama ɗaya a cikin jiki ke nan ba? Gama an ce, “Biyun za su zama jiki ɗaya.”
Or know you not, that he who is joined to a harlot, is made one body? For they shall be, saith he, two in one flesh.
17 Wanda kuwa ya haɗa jikinsa da Ubangiji ya zama ɗaya da shi ke nan a ruhu.
But he who is joined to the Lord, is one spirit.
18 Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.
Fly fornication. Every sin that a man doth, is without the body; but he that committeth fornication, sinneth against his own body.
19 Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne;
Or know you not, that your members are the temple of the Holy Ghost, who is in you, whom you have from God; and you are not your own?
20 saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.
For you are bought with a great price. Glorify and bear God in your body.

< 1 Korintiyawa 6 >