< 1 Korintiyawa 2 >
1 Da na zo wurinku’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba.
И аз пришед к вам, братие, приидох не по превосходному словеси или премудрости возвещая вам свидетелство Божие:
2 Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye.
не судих бо ведети что в вас, точию Иисуса Христа, и Сего распята:
3 Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai.
и аз в немощи и страсе и трепете мнозе бых в вас.
4 Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu,
И слово мое и проповедь моя не в препретелных человеческия премудрости словесех, но в явлении духа и силы,
5 domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.
да вера ваша не в мудрости человечестей, но в силе Божией будет.
6 Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. (aiōn )
Премудрость же глаголем в совершенных, премудрость же не века сего, ни князей века сего престающих, (aiōn )
7 A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. (aiōn )
но глаголем премудрость Божию, в тайне сокровенную, юже предустави Бог прежде век в славу нашу, (aiōn )
8 Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. (aiōn )
юже никтоже от князей века сего разуме: аще бо быша разумели, не быша Господа славы распяли. (aiōn )
9 Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”
Но якоже есть писано: ихже око не виде, и ухо не слыша, и на сердце человеку не взыдоша, яже уготова Бог любящым Его.
10 Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa. Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah.
Нам же Бог открыл есть Духом Своим: Дух бо вся испытует, и глубины Божия.
11 Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.
Кто бо весть от человек, яже в человеце, точию дух человека, живущий в нем? Такожде и Божия никтоже весть, точию Дух Божий.
12 Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake.
Мы же не духа мира сего прияхом, но Духа иже от Бога, да вемы яже от Бога дарованная нам,
13 Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya.
яже и глаголем не в наученых человеческия премудрости словесех, но в наученых Духа Святаго, духовная духовными сразсуждающе.
14 Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.
Душевен же человек не приемлет яже Духа Божия: юродство бо ему есть, и не может разумети, зане духовне востязуется.
15 Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum.
Духовный же востязует убо вся, а сам той ни от единаго востязуется.
16 “Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji, har da zai koya masa?” Amma muna da tunani iri na Kiristi ne.
Кто бо разуме ум Господень, иже изяснит и? Мы же ум Христов имамы.