< 1 Korintiyawa 16 >

1 To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa.
Περὶ δὲ τῆς λογίας τῆς εἰς τοὺς ἁγίους, ὥσπερ διέταξα ταῖς ἐκκλησίαις τῆς Γαλατίας, οὕτω καὶ ὑμεῖς ποιήσατε.
2 A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba.
Κατὰ μίαν σαββάτων ἕκαστος ὑμῶν παρ᾽ ἑαυτῷ τιθέτω, θησαυρίζων ὅ τι ἂν εὐοδῶται, ἵνα μή, ὅταν ἔλθω, τότε λογίαι γίνωνται.
3 In kuwa na iso sai in ba da wasiƙun gabatarwa ga mutanen da kuka amince da su, in kuma aike su da taimakonku zuwa Urushalima.
Ὅταν δὲ παραγένωμαι, οὓς ἐὰν δοκιμάσητε δι᾽ ἐπιστολῶν, τούτους πέμψω ἀπενεγκεῖν τὴν χάριν ὑμῶν εἰς Ἱερουσαλήμ·
4 In kuma ya dace in tafi, to, sai su tafi tare da ni.
ἐὰν δὲ ᾖ ἄξιον τοῦ κἀμὲ πορεύεσθαι, σὺν ἐμοὶ πορεύσονται.
5 Bayan na zazzaga Makidoniya, zan zo wurinku, domin zan ratsa ta Makidoniya.
Ἐλεύσομαι δὲ πρὸς ὑμᾶς, ὅταν Μακεδονίαν διέλθω· Μακεδονίαν γὰρ διέρχομαι·
6 Wataƙila zan ɗan jima a wajenku, ko ma in ci damina a can, domin ku yi mini rakiya a tafiyata, duk inda za ni.
πρὸς ὑμᾶς δὲ τυχὸν παραμενῶ, ἢ καὶ παραχειμάσω, ἵνα ὑμεῖς με προπέμψητε οὗ ἐὰν πορεύωμαι.
7 Ba na so in gan ku yanzu in wuce kawai, ina fata zan yi’yan kwanaki tare da ku, in Ubangiji ya yarda.
Οὐ θέλω γὰρ ὑμᾶς ἄρτι ἐν παρόδῳ ἰδεῖν· ἐλπίζω δὲ χρόνον τινὰ ἐπιμεῖναι πρὸς ὑμᾶς, ἐὰν ὁ Κύριος ἐπιτρέπῃ.
8 Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos,
Ἐπιμενῶ δὲ ἐν Ἐφέσῳ ἕως τῆς Πεντηκοστῆς·
9 domin an buɗe mini wata hanya mai fāɗi don aiki mai amfani, ko da yake akwai mutane da yawa masu gāba da ni.
θύρα γάρ μοι ἀνέῳγε μεγάλη καὶ ἐνεργής, καὶ ἀντικείμενοι πολλοί.
10 In Timoti ya zo, ku tabbata ya sami sakewa a cikinku, domin aikin Ubangiji yake yi kamar yadda nake yi.
Ἐὰν δὲ ἔλθῃ Τιμόθεος, βλέπετε ἵνα ἀφόβως γένηται πρὸς ὑμᾶς· τὸ γὰρ ἔργον Κυρίου ἐργάζεται ὡς καὶ ἐγώ.
11 Kada fa wani yă ƙi karɓansa. Ku sallame shi lafiya, domin yă koma wurina. Ina duban hanyarsa tare da’yan’uwa.
Μή τις οὖν αὐτὸν ἐξουθενήσῃ· προπέμψατε δὲ αὐτὸν ἐν εἰρήνῃ, ἵνα ἔλθῃ πρός με· ἐκδέχομαι γὰρ αὐτὸν μετὰ τῶν ἀδελφῶν.
12 Batun ɗan’uwanmu Afollos kuwa, na roƙe shi sosai yă zo wurinku tare da’yan’uwa. Bai so zuwa yanzu ba, amma zai zo in ya sami zarafi.
Περὶ δὲ Ἀπολλὼ τοῦ ἀδελφοῦ, πολλὰ παρεκάλεσα αὐτὸν ἵνα ἔλθῃ πρὸς ὑμᾶς μετὰ τῶν ἀδελφῶν· καὶ πάντως οὐκ ἦν θέλημα ἵνα νῦν ἔλθῃ, ἐλεύσεται δὲ ὅταν εὐκαιρήσῃ.
13 Ku zauna a faɗake; ku dāge cikin bangaskiya; ku zauna da ƙarfafawa; ku yi ƙarfi.
Γρηγορεῖτε, στήκετε ἐν τῇ πίστει, ἀνδρίζεσθε, κραταιοῦσθε.
14 Ku yi kome da ƙauna.
Πάντα ὑμῶν ἐν ἀγάπῃ γινέσθω.
15 Kun san cewa iyalin gidan Istifanas ne suka fara tuba a Akayya. Sun kuma ba da kansu ga yi wa tsarkaka hidima. Ina roƙonku’yan’uwa,
Παρακαλῶ δὲ ὑμᾶς, ἀδελφοί—οἴδατε τὴν οἰκίαν Στεφανᾶ, ὅτι ἐστὶν ἀπαρχὴ τῆς Ἀχαΐας, καὶ εἰς διακονίαν τοῖς ἁγίοις ἔταξαν ἑαυτούς—
16 ku ba da kanku ga irin waɗannan, ga kuma kowa da ya haɗa hannu a aikin, yana kuma faman a cikinsa.
ἵνα καὶ ὑμεῖς ὑποτάσσησθε τοῖς τοιούτοις, καὶ παντὶ τῷ συνεργοῦντι καὶ κοπιῶντι.
17 Na yi farin ciki da isowar Istifanas, Fortunatus da Akaikus, domin sun biya bukatar da ba ku iya biya ba.
Χαίρω δὲ ἐπὶ τῇ παρουσίᾳ Στεφανᾶ καὶ Φουρτουνάτου καὶ Ἀχαϊκοῦ, ὅτι τὸ ὑμῶν ὑστέρημα οὗτοι ἀνεπλήρωσαν.
18 Gama sun wartsake ruhuna da kuma naku. Ya kamata ku girmama irin waɗannan mutane.
Ἀνέπαυσαν γὰρ τὸ ἐμὸν πνεῦμα καὶ τὸ ὑμῶν· ἐπιγινώσκετε οὖν τοὺς τοιούτους.
19 Ikkilisiyoyin da suke a lardin Asiya suna gaisuwa. Akwila da Firiskila suna gaishe ku sosai cikin Ubangiji, haka ma ikkilisiyar da takan taru a gidansu.
Ἀσπάζονται ὑμᾶς αἱ ἐκκλησίαι τῆς Ἀσίας· ἀσπάζονται ὑμᾶς ἐν Κυρίῳ πολλὰ Ἀκύλας καὶ Πρίσκιλλα, σὺν τῇ κατ᾽ οἶκον αὐτῶν ἐκκλησίᾳ.
20 Dukan’yan’uwa a nan suna gaisuwa. Ku gai da juna da sumba mai tsarki.
Ἀσπάζονται ὑμᾶς οἱ ἀδελφοὶ πάντες. Ἀσπάσασθε ἀλλήλους ἐν φιλήματι ἁγίῳ.
21 Ni, Bulus nake rubuta wannan gaisuwa da hannuna.
Ὁ ἀσπασμὸς τῇ ἐμῇ χειρὶ Παύλου.
22 Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji, la’ana ta zauna a kansa. Zo, ya Ubangiji!
Εἴ τις οὐ φιλεῖ τὸν Κύριον Ἰησοῦν Χριστόν, ἤτω ἀνάθεμα. Μαρὰν ἀθά.
23 Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da ku.
Ἡ χάρις τοῦ Κυρίου Ἰησοῦ Χριστοῦ μεθ᾽ ὑμῶν.
24 Ina gaishe ku duka, gaisuwar ƙaunata cikin Kiristi Yesu. Amin.
Ἡ ἀγάπη μου μετὰ πάντων ὑμῶν ἐν Χριστῷ Ἰησοῦ. Ἀμήν.

< 1 Korintiyawa 16 >