< 1 Korintiyawa 14 >

1 Ku bi halin ƙauna kuna kuma marmarin neman baye-bayen ruhaniya, musamman baiwar annabci.
把爱作为你最重要的目标! 但也要尽力获得属灵的恩赐,特别是说出神的信息的能力。
2 Gama duk wanda yake magana da wani harshe ba da mutane yake magana ba, sai dai da Allah. Tabbatacce, ba wanda yake fahimtarsa; yana faɗin asirai ta wurin ruhu ne.
那些讲述方言之人,它们讲述的对象不是人,而是上帝。因为没有人能听得懂,它们讲述的是圣灵深处的奥秘。
3 Amma duk wanda yake annabci, yana magana ne da mutane domin yă gina su, yă ƙarfafa su, yă kuma yi musu ta’aziyya.
但为上帝讲道之人却在成就人类,为他们提供鼓舞和安慰。
4 Wanda yake magana da wani harshe kuwa, kansa yake gina, amma mai annabci, ikkilisiya ce yake gina.
说方言知识成就自己,传播上帝之道却是在成就教会。我希望你们都会说方言,但我更希望你们都能讲道。
5 Zan so kowannenku yă yi magana da harsuna, sai dai zan fi so ku yi annabci. Wanda yake annabci ya fi wanda yake magana da harsuna, sai dai in ya fassara don ikkilisiya ta ginu.
因为方言如果不翻译,就无法成就教会。相比之下,讲道之人更重要。
6 To,’yan’uwa, a ce na zo wurinku ina kuma yin magana da waɗansu harsuna, amfanin me zan yi muku in ban zo muku da wani bayani ko sani ko annabci, ko kuma kalmar koyarwa ba?
兄弟姐妹们,如果我到你们那里时只说方言,而不是讲述启示、知识、预言或进行教导,那又能给你们带来什么益处?
7 Abubuwan nan marasa rai ma da sukan yi ƙara, kamar su algaita ko molo, in muryarsu ba tă fita sosai ba, yaya wani zai san abin da ake busawa ko kaɗawa?
很多没有生命的物品也能发出声音,比如箫或琴。但如果它们无法发出清晰的音调,你又怎知它们弹奏的是什么?
8 Haka ma in ba a busa ƙaho sosai ba, wa zai yi shirin yaƙi?
同理,如果军号无法发出清晰的声音,谁又能做好战斗的准备呢?
9 Haka yake sa’ad da kuka yi magana da waɗansu harsunan da ba a fahimta. In babu wanda zai san abin da kuke faɗi, za ka dai yi wa iska magana ne kawai.
你们的情况也是如此,如果口中说出无法听懂的语言,其他人又怎能理解你在说什么?你不过是向空气说话而已。
10 Ba shakka akwai harsuna iri-iri a duniya, duk da haka kowane a cikinsu yana da ma’ana.
世间有那么多种语言,任何一种都有它的意义。
11 To, in ban gane ma’anar abin da wani yake faɗi ba, ni baƙo ne ga mai maganar, shi kuma baƙo ne a gare ni.
如果我不理解这种语言,就无法理解讲述语言之人,他们也无法理解我。
12 Haka yake a gare ku. Da yake kuna marmarin samun baye-bayen ruhaniya, sai ku ba da ƙarfinku ga yin amfani da waɗanda za su gina ikkilisiya.
你们也是如此。如果你们期待获得圣灵的恩赐,就应当设法拥有更多可以成就教会的恩赐。
13 Saboda haka, duk wanda yake magana da harshe, sai yă yi addu’a a yi masa baiwar fassara.
说方言之人应当祈求,让他的方言能够翻译出来。
14 Gama in na yi addu’a da wani harshe, ruhuna ne yake addu’a, amma tunanina bai amfana kome ba.
我若用方言祷告,那么就是我的灵在祷告,对我的理解毫无用处。
15 To, me zan yi? Akwai lokutan da zan yi addu’a da ruhuna; akwai kuma lokutan da zan yi addu’a da hankalina. Wani lokaci ya kamata in yi waƙa da ruhuna, a wani lokacin kuma in yi waƙa da hankalina.
那么我该怎么办呢?我要以灵祷告,也要用心智祷告。我要以灵歌唱,也要以心智歌唱。
16 A cewa waɗansu baƙi suna cikin sujadarku, sa’ad da kuke yabon Allah da ruhunku, yaya waɗanda suke tare ku za su fahimta, har su ce, “Amin,” da yake ba su san abin da kuke faɗi ba?
因为如果你只以灵赞美,普通人就无法知晓你在说什么,在你进行感恩祈祷后,也无法说“阿门。”
17 Ko da yake kuna ba da godiya da kyau, amma wancan mutumin da yake tare da ku bai ginu ba.
你可能进行了一次无以伦比的感恩祈祷,但对其他人却毫无帮助!
18 Na gode wa Allah, domin ina magana da harsuna fiye da ku duka.
感谢上帝,我擅长的方言比你们大家都多。
19 Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe.
但在教会中,我宁愿用大家都理解的五句话去教导人,胜过用方言说出的千言万语。
20 ’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya.
兄弟姐妹们,不要像孩子一样思考。对于恶,你应该像婴儿般纯洁,但在思想上要成熟。
21 A cikin Doka yana a rubuce cewa, “Ta wurin mutane masu baƙin harsuna da kuma ta leɓunan baƙi zan yi magana da waɗannan mutane, amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,” in ji Ubangiji.
正如律法所记:“主说:我要借助说其他语言之人、借助外族人的嘴对我的子民讲话,但尽管如此,他们仍然不肯听我。”
22 Harsuna fa alama ce ba ga masu bi ba, sai dai ga marasa bi. Annabci kuwa ga masu bi ne ba ga marasa bi ba.
说方言即是一个信号,并非讲给信徒,而是讲给那些不信之人。但讲述上帝预言之道恰好相反:这个信号讲述的对象并非那些不信之人,而是信主之人。
23 Saboda haka, in dukan ikkilisiya ta taru, kowa kuma yana magana da waɗansu harsuna, sai waɗansu jahilai ko waɗansu marasa bi suka shigo, ashe, ba za su ce kuna hauka ba?
如果整个教会聚在一起,大家都说方言,如果这时又不明就里或不信上帝之人走进来,难道不会觉得你们疯了吗!
24 Amma in wani marar bi, ko jahili ya shigo sa’ad da kowa yana annabci, sai maganar kowa ta ratsa shi, za su shawo kansa yă gane cewa shi mai zunubi ne saboda abin da kowa yake faɗi,
如果大家都讲上帝之道,不相信上帝或不理解这一切的人走进来,就会被众人说服,承认自己的罪。
25 asirin zuciyarsa kuma su bayyana a fili. Don haka, zai fāɗi a ƙasa yă yi wa Allah sujada yana cewa, “Lalle, Allah yana cikinku!”
他心里的隐秘会显露出来,他会跪倒敬拜上帝,确认上帝真正在你们之中。
26 Me za mu ce ke nan’yan’uwa? Sa’ad da kuka taru, wani yakan yi waƙa, wani koyarwa, wani wahayi, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Dole ne a yi duka don gina ikkilisiya.
兄弟姐妹们,你们应该怎么办呢?当你们聚集在一起,各司其职,比如唱歌、教导、预言、以方言表达和进行翻译,这样就能做好一切,成就和鼓励教会。
27 In kuwa waɗansu za su yi magana a wani harshe, to, kada su fi mutum biyu ko uku, kuma a yi bi da bi, wani kuma yă fassara.
如果有人想说方言,那么只能有两个人这样做,或最多三人,并且要轮流说,还要有一个人翻译。
28 In babu mai fassara, sai mai magana yă yi shiru a cikin ikkilisiya, yă yi wa kansa magana da kuma Allah.
如果没有人翻译,说方言之人就应该在教会中保持沉默,只对自己和上帝说好了。
29 Annabawa biyu ko uku za su iya yin magana, sauran kuma sai su auna a hankali abin da aka faɗa.
同理,也要有两三个人讲述预言,让其他人思考他们所讲的一切。
30 In kuma wahayi ya zo wa wani da yake zaune, sai mai magana na farko yă yi shiru.
但如果聚会中有人获得特别的启示,之前发言之人就应该停下来,让那人讲述。
31 Dukanku kuna iya yin annabci bi da bi, domin kowa yă sami koyarwa da ƙarfafawa.
你们可以轮流讲述上帝之道,以便大家可以学习,可以获得勉励。
32 Ruhohin annabawa kuwa suna ƙarƙashin sarrafawar annabawa.
讲述上帝之道的人,需要控制他们的预言灵感,
33 Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka.
因为上帝不会混乱,而是和平且安静。
34 Ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi.
妇女在教会中应当保持沉默,不应发言。他们应该如律法所属,顺从这样的场合。
35 In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace tă yi magana a cikin ikkilisiya.
如果她们希望学习,可以在家中询问自己的丈夫,因为女性不适合在教会中发言。
36 Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso?
为什么?难道上帝之道由你而起?难道只有你才被赐予这道吗?
37 In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yă gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne.
如果你认为自己是先知或拥有圣灵的馈赠,就应该意识到我写给你们的字字句句,都是主的命令。
38 In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.
如果有人不理会,别人也不必理会他。
39 Saboda haka’yan’uwana, ku yi marmarin yin annabci, kada kuma ku hana magana da harsuna.
所以我的兄弟姐妹们,要将讲述上帝之道作为你的目标,不要禁止以方言进行的表述。
40 Sai dai a yi kome daidai da kuma cikin tsari.
要确保一切都恰当而有序地进行。

< 1 Korintiyawa 14 >