< 1 Korintiyawa 12 >
1 To, game da baye-baye na ruhaniya,’yan’uwa, ba na so ku kasance da rashin sani.
Now concerning spiritual things, brothers, I do not want you to be ignorant.
2 Kun san cewa sa’ad da kuke masu bautar gumaka, ya zama, an shawo kanku, aka kuma ɓad da ku ga bin gumaka marasa magana.
You know that when you were unbelievers, you were led away to those mute idols, however you might be led.
3 Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.
Therefore I make known to you that no one speaking by God's Spirit says, "Jesus is accursed." No one can say, "Jesus is Lord," but by the Holy Spirit.
4 Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne.
Now there are various kinds of gifts, but the same Spirit.
5 Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne.
There are various kinds of service, and the same Lord.
6 Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.
There are various kinds of workings, but the same God, who works all things in all.
7 An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa.
But to each one is given the manifestation of the Spirit for the profit of all.
8 Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda.
For to one is given through the Spirit the word of wisdom, and to another the word of knowledge, according to the same Spirit;
9 Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda.
to another faith, by the same Spirit; and to another gifts of healings, by the one Spirit;
10 Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna.
and to another workings of miracles; and to another prophecy; and to another discernings of spirits; to another different kinds of tongues; and to another the interpretation of tongues.
11 Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so.
But the one and the same Spirit works all of these, distributing to each one separately as he desires.
12 Jiki guda ne, ko da yake an yi shi da gaɓoɓi da yawa; gaɓoɓin kuma ko da yake da yawa suke, jiki ɗaya ne. Haka yake da Kiristi.
For as the body is one, and has many members, and all the members of the body, being many, are one body; so also is Christ.
13 Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda zuwa ga jiki guda, ko Yahudawa ko Hellenawa, bawa ko’yantacce, an kuma ba wa dukanmu wannan Ruhu guda mu sha.
For in one Spirit we were all baptized into one body, whether Jews or Greeks, whether bond or free; and were all given to drink of one Spirit.
14 To, ba a yi jiki da gaɓa ɗaya kawai ba, amma da gaɓoɓi da yawa.
For the body is not one member, but many.
15 Da ƙafa za tă ce, “Saboda ni ba hannu ba ce, ni ba gaɓar jiki ba ce.” Wannan ba zai hana ta zama gaɓar jikin ba.
If the foot would say, "Because I'm not a hand, I'm not part of the body," that would not make it less a part of the body.
16 Da kunne zai ce, “Saboda ni ba ido ba ne, ni ba gaɓar jiki ba ne.” Wannan ba zai hana shi zama gaɓar jikin ba.
And if the ear would say, "Because I'm not the eye, I'm not part of the body," that would not make it less a part of the body.
17 Da a ce dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da kuma a ce dukan jiki kunne ne, da me za a sansana?
If the whole body were an eye, where would the hearing be? If the whole were an ear, where would the sense of smell be?
18 Tabbatacce, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowannensu, kamar yadda yake so su zama.
But as a matter of fact, God has arranged the members of the body, each one of them, according to his design.
19 Da a ce dukan jiki gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin?
If they were all the same member, where would the body be?
20 Yadda yake dai, akwai gaɓoɓi da yawa, amma jiki ɗaya.
So now there are many members, but one body.
21 Ba dama ido ya ce wa hannu, “Ba na bukatarka ba!” Kai kuma ba zai ce wa ƙafafu, “Ba na bukatarku ba!”
The eye cannot say to the hand, "I have no need for you," or again the head to the feet, "I have no need for you."
22 A maimakon haka, gaɓoɓin jiki da ake gani kamar ba su da ƙarfi, su ne masu muhimmanci.
On the contrary, those members which seem to be weaker are essential,
23 Kuma gaɓoɓin da muke tsammani ba su da martaba sosai, su ne mukan fi ba su girma. Sa’an nan gaɓoɓi marasa kyan gani, mun fi mai da hankali a kansu,
and the parts which we think less honorable we treat with greater honor, and our unpresentable parts are treated with dignity,
24 gaɓoɓi masu kyan gani kuwa, ba su bukatar yawan girmamawa. Allah ya harhaɗa jikunanmu yadda gaɓoɓin da ake gani kamar ba su da muhimmanci suna da amfani,
whereas our presentable parts have no such need. But God has put the body together, giving greater honor to the lesser member,
25 don kada rarrabuwa ta kasance a jiki, sai dai gaɓoɓin jiki su kula da juna.
that there may be no division in the body, but that the members should have the same concern for one another.
26 In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.
When one member suffers, all the members suffer with it. If a member is honored, all rejoice with it.
27 To, ku jikin Kiristi ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne.
Now you are the body of Christ, and members individually.
28 A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri.
God has set some in the church: first apostles, second prophets, third teachers, then miracle workers, then gifts of healings, helps, governments, and various kinds of tongues.
29 Shin, duka ne manzanni? Duka ne annabawa? Duka ne malamai? Duka ne suke da baiwar yin ayyukan banmamaki?
Are all apostles? Are all prophets? Are all teachers? Are all miracle workers?
30 Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara?
Do all have gifts of healings? Do all speak with tongues? Do all interpret?
31 Sai dai ku yi marmarin neman baye-baye mafi girma. Yanzu kuwa zan nuna muku mafificiyar hanya.
But earnestly desire the greater gifts. Moreover, I show a most excellent way to you.