< 1 Korintiyawa 10 >
1 Ba na so ku kasance da rashin sani,’yan’uwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku.
Ina son ku sani, 'yan'uwa, cewa ubaninmu duka suna karkashin gajimarai kuma sun bi ta cikin teku.
2 An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku.
Dukansu an yi masu baftisma cikin gajimarai da kuma teku,
3 Dukansu sun ci abincin ruhaniya guda
kuma dukansu sun ci abincin ruhaniya iri daya.
4 suka kuma sha ruwan ruhaniyan nan guda; gama sun sha daga dutsen ruhaniya nan, wanda ya yi tafiya tare da su, wannan dutsen kuwa Kiristi ne.
Dukansu sun sha abin sha na ruhaniya iri daya. Gama sun sha daga wani dutsen ruhaniya da ya bisu, kuma wannan dutsen Almasihu ne.
5 Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu ko’ina a cikin hamada.
Amma Ubangiji bai ji dadin yawancinsu ba, saboda haka gawawakin su suka bazu a jeji.
6 To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.
Wadan nan al'amura, an rubuta mana su domin muyi koyi da su, kada mu yi sha'awar miyagun ayyuka kamar yadda suka yi.
7 Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.”
Kada ku zama masu bautar gumaka kamar yadda wadansun su suka yi. Wannan kamar yadda aka rubuta ne, “Mutanen sukan zauna su ci su sha kuma su tashi suyi wasa.”
8 Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu.
Kada mu shiga zina da faskanci kamar yadda yawancin su suka yi, a rana guda mutane dubu ashirin da uku suka mutu.
9 Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su.
Kada mu gwada Almasihu kamar yadda yawancinsu suka yi, macizai suka yi ta kashe su.
10 Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su.
kada kuma ku zama masu gunaguni kamar yadda suka yi, suka yi ta mutuwa a hannun malaikan mutuwa.
11 Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. (aiōn )
Wadannan abubuwa sun faru dasu ne a matsayin misalai a garemu. An rubuta su domin gargadinmu - mu wadanda karshen zamanai yazo kanmu. (aiōn )
12 Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!
Saboda haka, bari duk wanda yake tunanin shi tsayyaye ne, to yayi hattara kada ya fadi.
13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
Babu gwajin da ya same ku wanda ba a saba da shi ba cikin dukan mutane. A maimako, Allah mai aminci ne. Da ba zaya bari ku jarabtu ba fiye da iyawarku. Tare da gwajin zai tanadar da hanyar fita, domin ku iya jurewa.
14 Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka.
Saboda haka ya kaunatattu na, ku guji bautar gumaka.
15 Ina magana da ku a kan ku mutane ne fa masu azanci; ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.
Ina magana da ku kamar masu zurfin tunani, domin ku auna abin da ni ke fadi.
16 Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba?
Kokon albarka da muke sa wa albarka, ba tarayya bane cikin jinin Almasihu? Gurasa da muke karyawa ba tarayya bane cikin jikin Almasihu?
17 Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda.
Domin akwai gurasa guda, mu da muke dayawa jiki daya ne. Dukanmu munci daga gurasa daya ne.
18 Ku dubi mutanen Isra’ila mana. Ashe, waɗanda suke cin hadayu, ba ɗaya suke da juna cikin cin hadayun da aka miƙa a bagade ba?
Dubi mutanen Isra'ila: ba wadanda ke cin hadayu ke da rabo a bagadi ba?
19 To, me kuke tsammani nake nufi a nan? Hadayar da aka miƙa wa gunki ce wani abu, ko kuma gunkin ne wani abu?
Me nake cewa? gunki wani abu ne? Ko kuma abincin da aka mika wa gunki hadaya wani abu ne?
20 A’a, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu.
Amma ina magana game da abubuwan da al'ummai suke hadaya, suna wa aljannu ne hadaya ba Allah ba. Ba na son kuyi tarayya da al'janu!
21 Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a teburin aljanu.
Ba zaku sha daga kokon Ubangiji ku kuma sha na Al'janu ba, ba za kuyi zumunta a teburin Ubangiji ku yi a na Al'janu ba.
22 Ashe, so muke mu tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?
Ko muna so mu sa Ubangiji kishi ne? Mun fi shi karfi ne?
23 “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa.
“Komai dai dai ne,” amma ba komai ke da amfani ba, “Komai dai dai ne,” amma ba komai ke gina mutane ba.
24 Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma.
Kada wani ya nemi abinda zaya amfane shi. A maimako, kowa ya nemi abinda zaya amfani makwabcinsa.
25 Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito,
Kana iya cin duk abin da ake sayarwa a kasuwa, ba tare da tamboyoyin lamiri ba.
26 gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.”
Gama “duniya da duk abin da ke cikin ta na Ubangiji ne.”
27 In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito.
Idan marar bangaskiya ya gayyace ka cin abinci, kana kuma da niyyar zuwa, ka je ka ci duk abinda aka kawo maka, ba tare da tamboyoyin lamiri ba.
28 Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yă kasance babu laifi
Amma idan wani ya ce maka, “Wannan abinci an yi wa gumaka hadaya da shi ne” To kada ka ci. Wannan za ka yi ne saboda wanda ya shaida maka, da kuma lamiri ( gama duniya da dukan abinda ke cikin ta na Ubangiji ne).
29 ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shari’anta’yancina?
Ba ina nufin lamirin ka ba, amma lamirin wanda ya fada maka. Don me za a hukunta 'yanci na domin lamirin wani?
30 In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?
Idan na ci abincin tare da bada godiya, don mi za a zage ni don abin da na bada godiya a kansa?
31 Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah.
Saboda haka, ko kana ci ko kana shi, ka yi komai domin daukakar Allah.
32 Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah
Kada ka zama sanadiyyar tuntube, ga Yahudawa, ko Helenawa, ko ikilisiyar Allah.
33 kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto.
Na yi kokari in farantawa dukan mutane rai cikin dukan abubuwa. Ba riba nake nema wa kaina ba, amma domin kowa. Na yi wannan ne domin su sami ceto.