< 1 Tarihi 9 >
1 Haka aka lissafta dukan Isra’ila a tarihin zuriyoyi a littafin sarakunan Isra’ila. Aka kwasa mutanen Yahuda zuwa zaman bauta a Babilon domin rashin aminci.
全以色列都統計了,且記載在以色列列王實錄上。[充軍後耶路撒冷的居民]猶大人因犯罪作惡被擄往巴比倫去。
2 To, na farkon da aka sāke zaunar da su a mallakarsu a garuruwansu, su ne waɗansu Isra’ilawa, firistoci, Lawiyawa da kuma masu hidimar haikali.
最初回來住在自己城內復業的,是以色列人、司祭、肋未人和獻身者。
3 Waɗanda suke daga Yahuda, daga Benyamin, da kuma daga Efraim da Manasse waɗanda suka zauna a Urushalima su ne,
遷回耶路撒冷的,有猶大、本雅明、厄弗辣因和默納協的子孫。
4 Uttai ɗan Ammihud, ɗan Omri, ɗan Imri, ɗan Bani, zuriyar Ferez ɗan Yahuda.
猶大的子孫中有:阿米胡得的兒子烏泰;阿米胡得是敖默黎的兒子,敖默黎是依默黎的兒子,依默黎是巴尼的兒子,巴尼是猶大的兒子培勒茲的兒子。
5 Na mutanen Shilo kuwa su ne, Asahiya ɗan fari da’ya’yansa maza.
舍拉人中,有長子阿撒雅和他的兒子們;
6 Na mutanen Zera su ne, Yewuyel. Mutane daga Yahuda sun kai 690.
則辣黑的子孫中,有耶烏耳。他們同族兄弟共計六百九十人。
7 Na Benyamin su ne, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Hodawiya, ɗan Hassenuwa;
本雅明的子孫中,有默叔藍的兒子撒路;默叔藍是曷狄雅的兒子,曷狄雅是哈斯奴阿的兒子。
8 Ibnehiya ɗan Yeroham; Ela ɗan Uzzi, ɗan Mikri; da Meshullam ɗan Shefatiya, ɗan Reyuwel, ɗan Ibniya.
此外,尚有耶路罕的兒子依貝乃雅,烏齊的兒子厄拉;烏齊是米革黎的兒子;又有舍法提雅的兒子默叔藍,舍法提雅是勒烏耳的兒子,勒烏耳是依貝尼雅的兒子。
9 Mutane daga Benyamin, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, sun kai 956. Dukan waɗannan mutane kawunan iyalansu ne.
按家系他們同族兄弟,共計九百五十六人:這些人都是各家族的族長。
10 Na firistoci su ne, Yedahiya; Yehoyarib; Yakin;
司祭中,有耶達雅、約雅黎布、雅津,
11 Azariya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, shugaban da yake lura da gidan Allah;
和希耳克雅的兒子阿匝黎雅;希耳克雅是默叔藍的兒子,默叔藍是匝多克的兒子、匝多克是默辣約特的兒子,默辣約特是阿希突布的兒子,阿希突布是天主聖殿之長。
12 Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya; da Ma’asai ɗan Adiyel, ɗan Yazera, ɗan Meshullam, ɗan Meshillemit, ɗan Immer.
此外,有耶洛罕的兒子阿達雅;耶洛罕是帕市胡爾的兒子,帕市胡爾是瑪耳基雅的兒子;還有阿狄耳的兒子瑪賽;阿狄耳是雅赫則辣的兒子,雅赫則辣是默叔藍的兒子,默叔藍是默史肋米特的兒子,默史肋米特是依默爾的兒子;
13 Firistocin da suke kawunan iyalai, sun kai 1,760. Dukansu ƙwararru ne, masu hakkin hidima a cikin gidan Allah.
連他們同族的兄弟,家族的族長,共計一千七百六十人,為天主聖殿服務,都是有本領的人。
14 Na Lawiyawa su ne, Shemahiya ɗan Hasshub, ɗan Azrikam, ɗan Hashabiya, mutumin Merari;
肋未人中,有哈叔布的兒子舍瑪雅;哈叔布是阿次黎岡的兒子,阿次黎岡是哈沙彼雅的兒子:以上默辣黎的子孫。
15 Bakbakkar, Heresh, Galal da Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zikri, ɗan Asaf;
還有巴刻巴卡、赫勒士、加拉耳和米加的兒子瑪塔尼雅;米加是齊革黎的兒子,齊革黎是阿撒夫的兒子;
16 Obadiya ɗan Shemahiya, ɗan Galal, ɗan Yedutun; da Berekiya ɗan Asa, ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofawa.
還有舍瑪雅的兒子敖巴狄雅;舍瑪雅是加拉耳的兒子,加拉耳是耶杜通的兒子;還有阿撒的兒子貝勒基雅;阿撒是厄耳卡納的兒子;厄耳卡納居住在乃托法人的村莊內。
17 Matsaran ƙofofi su ne, Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman da’yan’uwansu. Shallum ne babbansu
守門者中,有沙隆、阿谷布、塔耳孟和阿希曼;他們的兄弟沙隆為首,
18 da aka ajiye a Ƙofar Sarki a gabas, har zuwa wannan lokaci. Waɗannan su ne matsaran ƙofofi na sansanin Lawiyawa.
直到現今他們看守東面的王門;他們曾作過肋未營內的守門者。
19 Shallum ɗan Kore, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, da’yan’uwansa matsaran ƙofofi daga iyalin (mutanen Kohat) su suke da hakkin tsaron madogaran ƙofar Tenti kamar dai yadda kakanninsu suka kasance da hakkin tsaron mashigin mazaunin Ubangiji.
沙隆是科勒的兒子,科勒是阿彼雅撒夫的兒子,阿彼雅撒夫是科辣黑的兒子;他家族內的兄弟科辣黑人擔任敬禮的工作,看守會幕的門檻;他們的祖先曾在上主的軍營中防守營門。
20 A dā Finehas ɗan Eleyazar ne yake lura da matsaran, kuma Ubangiji ya kasance tare da shi.
厄肋阿匝爾的兒子丕乃哈斯曾作過他們的首領。─願天主與他們同在!
21 Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada.
默舍肋米雅的兒子則加黎雅曾看守會幕的大門。
22 Duka-duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai 212. Aka rubuta su zuriya-zuriya a ƙauyukansu. Dawuda da Sama’ila mai duba ne suka sa matsaran a wurarensu na aminci.
被選看守門檻的,共計二百一十二人。他們曾在本村莊內登過記,達味和先見者撒慕爾給他們派定了這職務。
23 Su da zuriyarsu, su suke lura da tsaron ƙofofin gidan Ubangiji, gidan da ake kira Tenti.
他們和自己的子孫在天主的聖殿,即會幕門口任守衛之職,
24 Matsaran suna a kusurwoyi huɗu, gabas, yamma, arewa da kudu.
守衛東西南北四方的大門。
25 ’Yan’uwansu a ƙauyukansu sukan zo lokaci, lokaci su yi ayyukansu kwana bakwai, bakwai.
在村莊住的同族兄弟,每七天應依時來同他們換班,
26 Amma manyan matsara huɗu, waɗanda suke Lawiyawa, an danƙa musu hakkin lura da ɗakuna da kuma wuraren ajiya a gidan Allah.
因為四位守門之長是肋未人,應常值班看守天主聖殿的廂房和庫房。
27 Sukan kwana a kewayen gidan Allah, domin dole su tsare shi; kuma su suke lura da mabuɗi don buɗewa a kowace safiya.
所以應在天主聖殿的四周過夜,因為他們有守護和每晨開門的職責。
28 Waɗansunsu su ne suke lura da kayayyakin da ake amfani da su a hidimar haikali; sukan ƙirga su sa’ad da ake shigar da su da sa’ad da ake fitar da su.
他們中有些人照著行禮的器皿,依數取出,原數送回;
29 An sa waɗansu su lura da kayayyakin da kuma dukan waɗansu kayan wuri mai tsarki, da kuma gari da ruwan inabi, da mai, turare da kuma kayan yaji.
有些人照管用具,即聖所內的一切用具,以及麵粉、酒、油、乳香和香料;
30 Amma waɗansu firistoci ne suke harhaɗa kayan yajin.
但用香料配製香液是司祭子孫的職務。
31 Wani Balawe mai suna Mattitiya, ɗan farin Shallum mutumin Kora ne aka danƙa masa hakkin toya burodin miƙawa.
肋未人瑪提提雅,科辣黑族人沙隆的長子,負責照管烤餅的事。
32 Waɗansu’yan’uwansu Kohatawa ne suke lura da shiryawa burodin da ake kaiwa a tebur a kowane Asabbaci.
他們的兄弟刻哈特的子孫,每安息日照料備製供餅的事。
33 Waɗanda suke mawaƙa, kawunan iyalan Lawiyawa, sukan zauna a ɗakunan haikali kuma ba sa yin waɗansu ayyuka domin su suke da hakkin aiki dare da rana.
這些是歌詠員......肋未家族的族長,住在廂房內,不做別的事,只日夜執行自己的職務。
34 Dukan waɗannan su ne kawunan iyalan Lawiyawa, manya kamar yadda aka lissafta su a zuriyarsu, kuma suna zama a Urushalima.
以上是肋未家族按家系,在耶路撒冷的族長。[撒烏耳的祖先和後裔]
35 Yehiyel mahaifin Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Matarsa ita ce Ma’aka
住在基貝紅的,有基貝紅的父親耶依耳,他的妻子名叫瑪阿加。
36 ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,
他的長子阿貝冬、其次是族爾,克士、巴耳、乃爾、納達布、
37 Gedor, Ahiyo, Zakariya da Miklot.
革多爾、阿希約、則加黎雅和米刻羅特。
38 Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
米刻羅特生史曼;他們兄弟彼此為鄰,住在耶路撒冷。
39 Ner shi mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.
乃爾生克士,克士生撒烏耳,撒烏耳生約納堂、瑪耳基叔亞、阿彼納達布和依市巴耳。
40 Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda shi ne mahaifin Mika.
約納堂的兒子:默黎巴耳;默黎巴耳生米加、
41 ’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tareya da Ahaz.
米加的兒子:丕東、默肋客、塔勒亞和阿哈茲。
42 Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.
阿哈茲生約阿達,約阿達生阿肋默特、阿次瑪委特和齊默黎;齊默黎生摩匝,
43 Moza shi ne mahaifin Bineya; Refahiya, Eleyasa da kuma Azel.
摩匝生彼納;彼納的兒子勒法雅,勒法雅的兒子厄拉撒,厄拉撒的兒子阿責耳;
44 Azel yana da’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Waɗannan su ne’ya’yan Azel maza.
阿責耳有六個兒子,他們的名字是:阿次黎岡、波革魯、依市瑪耳、沙黎雅、敖巴狄雅和哈南:以上是阿責耳的兒子。