< 1 Tarihi 8 >

1 Benyamin shi ne mahaifin, Bela ɗansa na fari, Ashbel ɗansa na biyu, Ahara na uku,
Benjamin engendra Béla, son premier-né, Ashbel le second, Achrach le troisième,
2 Noha na huɗu da Rafa na biyar.
Nocha le quatrième, et Rapha le cinquième.
3 ’Ya’yan Bela maza su ne, Addar, Gera, Abihud
Les fils de Béla furent: Addar, Guéra, Abihud,
4 Abishuwa, Na’aman, Ahowa,
Abishua, Naaman, Achoach,
5 Gera, Shefufan da Huram.
Guéra, Shéphuphan et Huram.
6 Waɗannan su ne zuriyar Ehud, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Geba waɗanda aka kuma kwasa zuwa Manahat.
Voici les enfants d'Échud; ils étaient chefs des maisons des pères des habitants de Guéba, et ils les transportèrent à Manachath:
7 Na’aman, da Ahiya, da Gera. Gera ne shugabansu lokacin da aka kai su bauta, shi ne ya haifi Uzza da Ahilud.
Naaman, Achija et Guéra; c'est lui qui les transporta. Il engendra Uzza et Achichud.
8 An haifa’ya’ya maza wa Shaharayim a Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba’ara.
Shacharaïm eut des enfants au pays de Moab, après qu'il eut renvoyé Hushim et Baara, ses femmes.
9 Ya haifi Yobab, Zibiya, Hodesh, Malkam,
Il engendra de Hodèsh, sa femme, Jobab, Tsibia, Mésha, Malcam,
10 Yewuz, Sakiya da Mirma ta wurin Hodesh matarsa. Waɗannan su ne’ya’yansa, kawunan iyalai.
Jéuts, Shocja et Mirma. Ce sont là ses fils, chefs des pères.
11 Ya haifi Abitub da Efa’al ta wurin Hushim.
De Hushim il engendra Abitub, et Elpaal.
12 ’Ya’yan Efa’al maza su ne, Eber, Misham, Shemed (wanda ya gina Ono da Lod tare da ƙauyukan kewayensu),
Les fils d'Elpaal: Éber, Misheam, et Shémer, qui bâtit Ono, Lod et les villes de son ressort.
13 da Beriya da Shema, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Aiyalon waɗanda kuma suka kori mazaunan Gat.
Béria et Shéma, qui étaient chefs des pères des habitants d'Ajalon, mirent en fuite les habitants de Gath.
14 Ahiyo, Shashak, Yeremot
Achio, Shashak, Jérémoth,
15 Zebadiya, Arad, Eder,
Zébadia, Arad, Éder,
16 Mika’ilu, Isfa da Yoha su ne’ya’yan Beriya maza.
Micaël, Jishpha et Jocha, étaient fils de Béria.
17 Zebadiya, Meshullam, Hizki, Heber,
Zébadia, Meshullam, Hizki, Héber,
18 Ishmerai, Izliya da Yobab su ne’ya’yan Efa’al maza.
Jishméraï, Jizlia, et Jobab, étaient fils d'Elpaal.
19 Yakim, Zikri, Zabdi,
Jakim, Zicri, Zabdi,
20 Eliyenai, Zilletai, Eliyel,
Éliénaï, Tsilethaï, Éliel,
21 Adahiya, Berahiya da Shimra su ne’ya’yan Shimeyi maza.
Adaja, Béraja, et Shimrath, étaient fils de Shimeï.
22 Ishfan, Eber, Eliyel,
Jishpan, Éber, Éliel,
23 Abdon, Zikri, Hanan,
Abdon, Zicri, Hanan,
24 Hananiya, Elam, Antotiya,
Hanania, Élam, Anthothija,
25 Ifdehiya da Fenuwel su ne’ya’yan Shashak maza.
Jiphdéja et Pénuel, étaient fils de Shashak.
26 Shamsherai, Shehariya, Ataliya,
Shamshéraï, Shécharia, Athalia,
27 Ya’areshiya, Iliya da Zikri su ne’ya’yan Yeroham maza.
Jaareshia, Élija et Zicri, étaient fils de Jérocham.
28 Dukan waɗannan su ne kawunan iyalai, manya kamar yadda aka lissafta a cikin zuriyarsu, suka zauna a Urushalima.
Ce sont là les chefs des maisons des pères, chefs selon leur naissance. Ils habitaient à Jérusalem.
29 Yehiyel na Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Sunan matarsa Ma’aka,
Le père de Gabaon habitait à Gabaon; sa femme s'appelait Maaca.
30 ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,
Son fils, le premier-né, fut Abdon; puis Tsur, Kis, Baal, Nadab,
31 Gedor, Ahiyo, Zeker
Guédor, Achio et Zéker.
32 da Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
Mikloth engendra Shiméa. Ils habitèrent aussi près de leurs frères à Jérusalem, avec leurs frères.
33 Ner shi ne mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.
Ner engendra Kis; Kis engendra Saül; Saül engendra Jonathan, Malkishua, Abinadab et Eshbaal.
34 Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda ya zama mahaifin Mika.
Fils de Jonathan: Mérib-Baal. Mérib-Baal engendra Mica.
35 ’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tereya da Ahaz.
Fils de Mica: Pithon, Mélec, Thaeréa et Achaz.
36 Ahaz shi ne mahaifin Yehowadda, Yehowadda shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.
Achaz engendra Jéhoadda; Jéhoadda engendra Alémeth, Azmaveth et Zimri; Zimri engendra Motsa;
37 Moza shi ne mahaifin Bineya; Rafa, Eleyasa da kuma Azel.
Motsa engendra Binea, qui eut pour fils Rapha, qui eut pour fils Éleasa, qui eut pour fils Atsel.
38 Azel yana da’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Dukan waɗannan’ya’yan Azel maza ne.
Atsel eut six fils, dont voici les noms: Azrikam, Bocru, Ismaël, Shéaria, Obadia et Hanan. Tous ceux-là étaient fils d'Atsel.
39 ’Ya’yan ɗan’uwansa Eshek su ne, Ulam ɗan farinsa, Yewush ɗansa na biyu da Elifelet na uku.
Fils d'Eshek, son frère: Ulam, son premier-né, Jéush le second, et Éliphélet le troisième.
40 ’Ya’yan Ulam maza jarumawa ne sosai waɗanda suke iya riƙe baka. Suna da’ya’ya maza masu yawa da jikoki, 150 gaba ɗaya. Dukan waɗannan zuriyar Benyamin ne.
Les fils d'Ulam furent de vaillants guerriers, tirant de l'arc; et ils eurent beaucoup de fils et de petits-fils, cent cinquante. Tous ceux-là sont des enfants de Benjamin.

< 1 Tarihi 8 >