< 1 Tarihi 7 >

1 ’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yashub da Shimron, su huɗu ne duka.
Hijos de Isacar: Tola, Fúa, Jasub y Simrón: cuatro.
2 ’Ya’yan Tola maza su ne, Uzzi, Refahiya, Yeriyel, Ibsam da Sama’ila, su ne kuma kawunan iyalansu. A zamanin mulkin Dawuda, an rubuta zuriyar Tola a matsayin mayaƙa a cikin tarihinsu, sun kai 22,600.
Hijos de Tola: Uzi, Refaías, Jeriel, Jahmai, Jibsam y Semuel, jefes de las casas paternas. De Tola fueron contados por sus familias 22.6000 hombres valientes en sus generaciones en el tiempo de David.
3 Ɗan Uzzi shi ne, Izrahiya.’Ya’yan Izrahiya maza su ne, Mika’ilu, Obadiya, Yowel da Isshiya. Dukansu biyar manya ne.
El hijo de Uzi fue Israhías, y los hijos de Israhías: Micael, Obadías, Joel e Isías, un total de cinco jefes.
4 Bisa ga tarihin iyalinsu, sun kai mutane 36,000 shiryayyu don yaƙi, gama suna da mata da’ya’ya da yawa.
Había con ellos en sus familias y sus casas paternas, 36.000 hombres guerreros, porque tuvieron muchas mujeres e hijos.
5 Dangin da suke maza masu yaƙi sun kasance na dukan gidajen Issakar ne, kamar yadda aka rubuta a cikin tarihi, su 87,000 ne duka.
Sus hermanos, según todas las familias de Isacar, contados por sus genealogías, eran 87.000 hombres valientes.
6 ’Ya’ya uku maza na Benyamin su ne, Bela, Beker da Yediyayel.
Hijos de Benjamín: Bela, Bequer y Jediael: tres.
7 ’Ya’yan Bela maza su ne, Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot da Iri, su ne kawunan iyalai, kuma su biyar ne duka. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna mazan da sun isa yaƙi 22,034.
Hijos de Bela: Ezbón, Uzi, Uziel, Jerimot e Iri: cinco jefes de casas paternas, hombres valientes y de la descendencia de los cuales fueron contados 22.034.
8 ’Ya’yan Beker maza su ne, Zemira, Yowash, Eliyezer, Eliyohenai, Omri, Yeremot, Abiya, Anatot da Alemet. Dukan waɗannan’ya’yan Beker maza ne.
Hijos de Bequer: Zemira, Joás, Eliezer, Elioenai, Omri, Jerimot, Abías, Anatot y Alamet. Todos éstos fueron hijos de Bequer.
9 Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna da kawunan iyalai da mazan da suka isa yaƙi 20,200.
Contados por sus descendencias, por sus familias, los que eran jefes de familias resultaron 20.200 hombres valientes.
10 Ɗan Yediyayel shi ne, Bilhan.’Ya’yan Bilhan maza su ne, Yewush, Benyamin, Ehud, Kena’ana, Zetan, Tarshish da Ahishahar.
Hijo de Jediael fue Bilhán. Los hijos de Bilhán: Jeús, Benjamín, Aod, Quenaana, Zetán, Tarsis y Ahisahar.
11 Dukan waɗannan’ya’yan Yediyayel maza kawunan iyalai ne. Akwai mazan da suka isa yaƙi waje 17,200.
Todos éstos fueron hijos de Jediael, jefes de familias, hombres valientes, 17.200 que salían a combatir en la guerra.
12 Shuffiyawa da Huffiyawa zuriyar Ir ne, kuma Hushiyawa zuriyar Aher ne.
Supim y Hupim fueron hijos de Hir. Husim fue hijo de Aher.
13 ’Ya’yan Naftali maza su ne, Yaziyel, Guni, Yezer da Shallum, su zuriyar Bilha ne.
Hijos de Neftalí: Jahzeel, Guni, Jezer y Salum, hijos de Bilha.
14 Zuriyar Manasse su ne, Asriyel zuriyarsa ne ta wurin ƙwarƙwararsa mutuniyar Aram. Ta haifa wa Makir mahaifin Gileyad.
Hijos de Manasés: Asriel, al cual dio a luz su concubina siria, quien también dio a luz a Maquir, padre de Galaad.
15 Makir ya auri mata daga cikin Huffiyawa da Shuffiyawa.’Yar’uwarsa ita ce Ma’aka. Wani daga zuriyar, sunansa Zelofehad, shi yana da’ya’yan mata ne kawai.
Maquir tomó como esposa a la hermana de Hupim y Supim. Se llamaba Maaca. El nombre del segundo descendiente fue Zelofehad, quien tuvo hijas.
16 Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa ta kuma ba shi suna Feresh. Sunan ɗan’uwansa Sheresh,’ya’yan Feresh maza kuwa su ne Ulam da Rakem.
Maaca, esposa de Maquir, dio a luz un hijo, y lo llamó Peres. El nombre de su hermano fue Seres, los hijos del cual fueron Ulam y Requem.
17 Ɗan Ulam shi ne, Bedan. Duka waɗannan zuriyar Gileyad ne. Gileyad ɗan Makir ne, Makir kuma ɗan Manasse.
El hijo de Ulam fue Bedán. Éstos fueron los hijos de Galaad, hijo de Maquir, hijo de Manasés.
18 ’Yar’uwarsa Makir mai suna Hammoleket ta haifi Ishod, Abiyezer da Mala.
Su hermana Hamolequet dio a luz a Isod, Abiezer, Mahala y Semida.
19 ’Ya’yan Shemida maza su ne, Ahiyan, Shekem, Liki da Aniyam.
Los hijos de Semida fueron Ahián, Siquem, Likhi y Aniam.
20 Zuriyar Efraim su ne, Shutela, Bered, Tahat, Eleyada, Tahat
Hijos de Efraín: Sutela, Bered, Tahat, Elada, Tahat,
21 Zabad da Shutela. Wani ɗan ƙasa haifaffen mutanen Gat ya kashe Ezer da Elad, sa’ad da suka gangara don su ƙwace dabbobinsu.
Zabad Sutela, Ezer y Elad. Pero los hombres de Gat, naturales de aquella tierra, los mataron porque bajaron a quitarles sus ganados.
22 Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya.
Su padre Efraín les hizo duelo muchos días, y sus hermanos llegaron a consolarlo.
23 Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa.
Luego se unió a su esposa, la cual concibió y dio a luz un hijo, al cual llamó Bería, porque su casa estaba en aflicción.
24 ’Yarsa ita ce Sheyera, wadda ta gina Bet-Horon na kwari da na tudu da kuma Uzzen-Sheyera. Zuriyarsa ita ce,
Y su hija fue Seera, la cual edificó Bet-horón, la baja y la alta, y también Uzen-seera.
25 Refa, Reshef, Tela, Tahan,
Hijos de este Bería fueron Refa, Resef, Telah, Tahán,
26 Ladan, Ammihud, Elishama,
Laadán, Amiud, Elisama,
27 Nun da kuma Yoshuwa.
Non y Josué.
28 Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta.
La herencia y lugar de residencia de ellos fue Bet-ʼEl con sus aldeas, y hacia el oriente Naarán, y en el occidente Gezer y sus aldeas, asimismo Siquem con sus aldeas, hasta Gaza y sus aldeas;
29 A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa.
y junto al territorio de los hijos de Manasés, Bet-seán, Taanac, Meguido y Dor, cada uno con sus aldeas. En estos lugares vivieron los hijos de José, hijo de Israel.
30 ’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishwi da Beriya.’Yar’uwarsa ita ce Sera.
Hijos de Aser: Imna, Isúa, Isúi, Bería y su hermana Sera.
31 ’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel, wanda yake mahaifin Birzayit.
Hijos de Bería: Heber y Malquiel, el cual fue padre de Birzavit.
32 Heber shi ne mahaifin Yaflet, Shomer da Hotam da kuma’yar’uwarsu Shuwa.
Heber engendró a Jaflet, Semer, Hotam y Súa, hermana de ellos.
33 ’Ya’yan Yaflet maza su ne, Fasak, Bimhal da Ashwat. Waɗannan su ne’ya’yan Yaflet maza.
Hijos de Jaflet: Pasac, Bimhal y Asvat.
34 ’Ya’yan Shemer maza su ne, Ahi, Roga, Yehubba da Aram.
Hijos de Semer fueron: Ahi, Rohga, Jehúba y Aram.
35 ’Ya’yan ɗan’uwansa Helem su ne, Zofa, Imna, Shelesh da Amal.
Hijos de su hermano Helem fueron: Zofa, Imna, Seles y Amal.
36 ’Ya’yan Zofa maza su ne, Suwa, Harnefer, Shuwal, Beri, Imra,
Hijos de Zofa: Súa, Harnefer, Súal, Beri, Imra,
37 Bezer, Hod, Shamma, Shilsha, Itran da Bera.
Beser, Hod, Sama, Silsa, Itrán y Beera.
38 ’Ya’yan Yeter maza su ne, Yefunne, Fisfa da Ara.
Hijos de Jeter: Jefone, Pispa y Ara.
39 ’Ya’yan Ulla maza su ne, Ara, Hanniyel da Riziya.
Hijos de Ula: Ara, Haniel y Rezia.
40 Dukan waɗannan zuriyar Asher ne, kawunan iyalai, zaɓaɓɓun mutane, jarumawa sosai da kuma fitattun shugabanni. Yawan mutanen da suke a shirye don yaƙi, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, 26,000 ne.
Todos éstos fueron hijos de Aser, jefes de familias paternas, escogidos, hombres valientes, jefes de líderes. Fueron contados por sus familias entre los que podían tomar las armas. El número de ellos fue 26.000 hombres.

< 1 Tarihi 7 >