< 1 Tarihi 6 >

1 ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.
利未的兒子是革順、哥轄、米拉利。
2 ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
哥轄的兒子是暗蘭、以斯哈、希伯倫、烏薛。
3 Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam.’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
暗蘭的兒子是亞倫、摩西,還有女兒米利暗。亞倫的兒子是拿答、亞比戶、以利亞撒、以他瑪。
4 Eleyazar shi ne mahaifin Finehas, Finehas mahaifin Abishuwa,
以利亞撒生非尼哈;非尼哈生亞比書;
5 Abishuwa mahaifin Bukki, Bukki mahaifin Uzzi,
亞比書生布基;布基生烏西;
6 Uzzi mahaifin Zerahiya, Zerahiya mahaifin Merahiyot,
烏西生西拉希雅;西拉希雅生米拉約;
7 Merahiyot mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub,
米拉約生亞瑪利雅;亞瑪利雅生亞希突;
8 Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Ahimawaz,
亞希突生撒督;撒督生亞希瑪斯;
9 Ahimawaz mahaifin Azariya, Azariya mahaifin Yohanan,
亞希瑪斯生亞撒利雅;亞撒利雅生約哈難;
10 Yohanan mahaifin Azariya (shi ne ya yi hidima a matsayin firist a haikalin da Solomon ya gina a Urushalima),
約哈難生亞撒利雅(這亞撒利雅在所羅門於耶路撒冷所建造的殿中,供祭司的職分);
11 Azariya mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub,
亞撒利雅生亞瑪利雅;亞瑪利雅生亞希突;
12 Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Shallum,
亞希突生撒督;撒督生沙龍;
13 Shallum mahaifin Hilkiya, Hilkiya mahaifin Azariya,
沙龍生希勒家;希勒家生亞撒利雅;
14 Azariya mahaifin Serahiya, Serahiya kuwa mahaifin Yehozadak.
亞撒利雅生西萊雅;西萊雅生約薩答。
15 Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar.
當耶和華藉尼布甲尼撒的手擄掠猶大和耶路撒冷人的時候,這約薩答也被擄去。
16 ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershom, Kohat da Merari.
利未的兒子是革順、哥轄、米拉利。
17 Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Gershom. Libni da Shimeyi.
革順的兒子名叫立尼、示每。
18 ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
哥轄的兒子是暗蘭、以斯哈、希伯倫、烏薛。
19 ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. Waɗannan suke gidajen Lawiyawan da aka jera bisa ga kakanninsu.
米拉利的兒子是抹利、母示。這是按着利未人宗族分的各家。
20 Na Gershom su ne, Libni, Yahat, Zimma,
革順的兒子是立尼;立尼的兒子是雅哈;雅哈的兒子是薪瑪;
21 Yowa, Iddo, Zera da Yeyaterai.
薪瑪的兒子是約亞;約亞的兒子是易多;易多的兒子是謝拉;謝拉的兒子是耶特賴。
22 Zuriyar Kohat su ne, Amminadab, Kora, Assir,
哥轄的兒子是亞米拿達;亞米拿達的兒子是可拉;可拉的兒子是亞惜;
23 Elkana, Ebiyasaf, Assir,
亞惜的兒子是以利加拿;以利加拿的兒子是以比雅撒;以比雅撒的兒子是亞惜;
24 Tahat, Uriyel, Uzziya da Shawulu.
亞惜的兒子是他哈;他哈的兒子是烏列;烏列的兒子是烏西雅;烏西雅的兒子是少羅。
25 Zuriyar Elkana su ne, Amasai, Ahimot,
以利加拿的兒子是亞瑪賽和亞希摩。
26 Elkana, Zofai, Nahat,
亞希摩的兒子是以利加拿;以利加拿的兒子是瑣菲;瑣菲的兒子是拿哈;
27 Eliyab Yeroham, Elkana da Sama’ila.
拿哈的兒子是以利押;以利押的兒子是耶羅罕;耶羅罕的兒子是以利加拿;以利加拿的兒子是撒母耳。
28 ’Ya’yan Sama’ila maza su ne, Yowel ɗan fari da Abiya ɗa na biyu.
撒母耳的長子是約珥,次子是亞比亞。
29 Zuriyar Merari su ne, Mali, Libni, Shimeyi, Uzza,
米拉利的兒子是抹利;抹利的兒子是立尼;立尼的兒子是示每;示每的兒子是烏撒;
30 Shimeya, Haggiya da Asahiya.
烏撒的兒子是示米亞;示米亞的兒子是哈基雅;哈基雅的兒子是亞帥雅。
31 Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can.
約櫃安設之後,大衛派人在耶和華殿中管理歌唱的事。
32 Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.
他們就在會幕前當歌唱的差,及至所羅門在耶路撒冷建造了耶和華的殿,他們便按着班次供職。
33 Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da’ya’yansu maza. Daga mutanen Kohat akwai, Heman, mawaƙi ɗan Yowel, ɗan Sama’ila,
供職的人和他們的子孫記在下面: 哥轄的子孫中有歌唱的希幔。希幔是約珥的兒子;約珥是撒母耳的兒子;
34 ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyel, ɗan Towa,
撒母耳是以利加拿的兒子;以利加拿是耶羅罕的兒子;耶羅罕是以列的兒子;以列是陀亞的兒子;
35 ɗan Zuf, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai,
陀亞是蘇弗的兒子;蘇弗是以利加拿的兒子;以利加拿是瑪哈的兒子;瑪哈是亞瑪賽的兒子;
36 ɗan Elkana, ɗan Yowel, ɗan Azariya, ɗan Zefaniya
亞瑪賽是以利加拿的兒子;以利加拿是約珥的兒子;約珥是亞撒利雅的兒子;亞撒利雅是西番雅的兒子;
37 ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,
西番雅是他哈的兒子;他哈是亞惜的兒子;亞惜是以比雅撒的兒子;以比雅撒是可拉的兒子;
38 ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila;
可拉是以斯哈的兒子;以斯哈是哥轄的兒子;哥轄是利未的兒子;利未是以色列的兒子。
39 da kuma Asaf’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa. Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya,
希幔的族兄亞薩是比利家的兒子,亞薩在希幔右邊供職。比利家是示米亞的兒子;
40 ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya, ɗan Malkiya,
示米亞是米迦勒的兒子;米迦勒是巴西雅的兒子;巴西雅是瑪基雅的兒子;
41 ɗan Etni, ɗan Zera, ɗan Adahiya
瑪基雅是伊特尼的兒子;伊特尼是謝拉的兒子;謝拉是亞大雅的兒子;
42 ɗan Etan, ɗan Zimma, ɗan Shimeyi,
亞大雅是以探的兒子;以探是薪瑪的兒子;薪瑪是示每的兒子;
43 ɗan Yahat, ɗan Gershom, ɗan Lawi;
示每是雅哈的兒子;雅哈是革順的兒子。革順是利未的兒子。
44 da kuma daga’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa. Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi, ɗan Malluk,
他們的族弟兄米拉利的子孫,在他們左邊供職的有以探。以探是基示的兒子;基示是亞伯底的兒子;亞伯底是瑪鹿的兒子;
45 ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,
瑪鹿是哈沙比雅的兒子;哈沙比雅是亞瑪謝的兒子;亞瑪謝是希勒家的兒子;
46 ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer,
希勒家是暗西的兒子;暗西是巴尼的兒子;巴尼是沙麥的兒子;
47 ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.
沙麥是末力的兒子;末力是母示的兒子;母示是米拉利的兒子;米拉利是利未的兒子。
48 Aka ba’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah.
他們的族弟兄利未人也被派辦上帝殿中的一切事。
49 Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta.
亞倫和他的子孫在燔祭壇和香壇上獻祭燒香,又在至聖所辦理一切的事,為以色列人贖罪,是照上帝僕人摩西所吩咐的。
50 Waɗannan su ne zuriyar Haruna, Eleyazar, Finehas, Abishuwa,
亞倫的兒子是以利亞撒;以利亞撒的兒子是非尼哈;非尼哈的兒子是亞比書;
51 Bukki, Uzzi, Zerahiya,
亞比書的兒子是布基;布基的兒子是烏西;烏西的兒子是西拉希雅;
52 Merahiyot, Amariya, Ahitub,
西拉希雅的兒子是米拉約;米拉約的兒子是亞瑪利雅;亞瑪利雅的兒子是亞希突;
53 Zadok da Ahimawaz.
亞希突的兒子是撒督;撒督的兒子是亞希瑪斯。
54 Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne):
他們的住處按着境內的營寨,記在下面:哥轄族亞倫的子孫先拈鬮得地,
55 Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta.
在猶大地中得了希伯崙和四圍的郊野;
56 Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne.
只是屬城的田地和村莊都為耶孚尼的兒子迦勒所得。
57 Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa,
亞倫的子孫得了逃城希伯崙,又得了立拿與其郊野,雅提珥、以實提莫與其郊野;
58 Hilen, Debir,
希崙與其郊野,底璧與其郊野,
59 Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu.
亞珊與其郊野,伯‧示麥與其郊野。
60 Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu. Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka.
在便雅憫支派的地中,得了迦巴與其郊野,阿勒篾與其郊野,亞拿突與其郊野。他們諸家所得的城共十三座。
61 Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse.
哥轄族其餘的人又拈鬮,在瑪拿西半支派的地中得了十座城。
62 Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan.
革順族按着宗族,在以薩迦支派的地中,亞設支派的地中,拿弗他利支派的地中,巴珊內瑪拿西支派的地中,得了十三座城。
63 Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.
米拉利族按着宗族拈鬮,在呂便支派的地中,迦得支派的地中,西布倫支派的地中,得了十二座城。
64 Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu.
以色列人將這些城與其郊野給了利未人。
65 Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata.
這以上錄名的城,在猶大、西緬、便雅憫三支派的地中,以色列人拈鬮給了他們。
66 Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim.
哥轄族中有幾家在以法蓮支派的地中也得了城邑,
67 A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer,
在以法蓮山地得了逃城示劍與其郊野,又得了基色與其郊野,
68 Yokmeyam, Bet-Horon,
約緬與其郊野,伯‧和崙與其郊野,
69 Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu.
亞雅崙與其郊野,迦特‧臨門與其郊野。
70 Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat.
哥轄族其餘的人在瑪拿西半支派的地中得了亞乃與其郊野,比連與其郊野。
71 Mutanen Gershom suka sami waɗannan. Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu;
革順族在瑪拿西半支派的地中得了巴珊的哥蘭與其郊野,亞斯他錄與其郊野;
72 daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat,
又在以薩迦支派的地中得了基低斯與其郊野,大比拉與其郊野,
73 Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu;
拉末與其郊野,亞年與其郊野;
74 daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon,
在亞設支派的地中得了瑪沙與其郊野,押頓與其郊野,
75 Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu;
戶割與其郊野,利合與其郊野;
76 daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.
在拿弗他利支派的地中得了加利利的基低斯與其郊野,哈們與其郊野,基列亭與其郊野。
77 Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan. Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu;
還有米拉利族的人在西布倫支派的地中得了臨摩挪與其郊野,他泊與其郊野;
78 daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza,
又在耶利哥的約旦河東,在呂便支派的地中得了曠野的比悉與其郊野,雅哈撒與其郊野,
79 Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu;
基底莫與其郊野,米法押與其郊野;
80 daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim,
又在迦得支派的地中得了基列的拉末與其郊野,瑪哈念與其郊野,
81 Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu.
希實本與其郊野,雅謝與其郊野。

< 1 Tarihi 6 >