< 1 Tarihi 5 >

1 ’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila (shi ne ɗan fari, amma sa’ad da ya ƙazantar da gadon auren mahaifinsa, sai aka ba wa’yancin ɗan farinsa wa’ya’yan Yusuf maza ɗan Isra’ila; don kada a lissafta shi a tarihin zuriya bisa ga matsayin haihuwarsa,
以色列的长子原是吕便;因他污秽了父亲的床,他长子的名分就归了约瑟。只是按家谱他不算长子。
2 ko da yake Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin’yan’uwansa kuma mai mulki ya fito daga gare shi,’yancin zaman ɗan fari na Yusuf ne),
犹大胜过一切弟兄,君王也是从他而出;长子的名分却归约瑟。
3 ’ya’yan Ruben ɗan farin Isra’ila maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.
以色列长子吕便的儿子是哈诺、法路、希斯伦、迦米。
4 Zuriyar Yowel su ne, Shemahiya, Gog, Shimeyi,
约珥的儿子是示玛雅;示玛雅的儿子是歌革;歌革的儿子是示每;
5 Mika, Reyahiya, Ba’al,
示每的儿子是米迦;米迦的儿子是利亚雅;利亚雅的儿子是巴力;
6 da Beyera, wanda Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya ɗauka zuwa zaman bauta. Beyera shi ne shugaban mutanen Ruben.
巴力的儿子是备拉。这备拉作吕便支派的首领,被亚述王提革拉·毗列色掳去。
7 Danginsu bisa ga iyalansu da aka jera bisa ga tarihin zuriyarsu su ne, Yehiyel shi ne sarki, akwai Zakariya,
他的弟兄照着宗族,按着家谱作族长的是耶利、撒迦利雅、比拉。
8 da Bela ɗan Azaz. Azaz ɗan Shema daga dangin Yowel. Yowel ya yi zama a yankin Arower har zuwa Nebo da Ba’al-Meyon.
比拉是亚撒的儿子;亚撒是示玛的儿子;示玛是约珥的儿子;约珥所住的地方是从亚罗珥直到尼波和巴力·免,
9 Ta waje gabas sun zauna a ƙasar har zuwa bakin hamadan da ya nausa zuwa Kogin Yuferites, domin dabbobinsu sun ƙaru a Gileyad.
又向东延到幼发拉底河这边的旷野,因为他们在基列地牲畜增多。
10 A zamanin Shawulu zuriyar Ruben sun yi yaƙi da Hagirawa, suka ci su da yaƙi, suka zauna a wuraren zaman Hagirawan ko’ina a dukan yankin gabashin Gileyad.
扫罗年间,他们与夏甲人争战,夏甲人倒在他们手下,他们就在基列东边的全地,住在夏甲人的帐棚里。
11 Mutanen Gad sun zauna kusa da mutanen Ruben a Bashan, har zuwa Saleka.
迦得的子孙在吕便对面,住在巴珊地,延到撒迦。
12 Yowel shi ne babba, sai Shafan na biyu, sa’an nan Yanai da Shafat, su ne tushen Bashan.
他们中间有作族长的约珥,有作副族长的沙番,还有雅乃和住在巴珊的沙法。
13 Danginsu, bisa ga iyalai su ne, Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka.
他们族弟兄是米迦勒、米书兰、示巴、约赖、雅干、细亚、希伯,共七人。
14 Waɗannan su ne’ya’yan Abihayil ɗan Huri, ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Mika’ilu, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.
这都是亚比孩的儿子。亚比孩是户利的儿子;户利是耶罗亚的儿子;耶罗亚是基列的儿子;基列是米迦勒的儿子;米迦勒是耶示筛的儿子;耶示筛是耶哈多的儿子;耶哈多是布斯的儿子。
15 Ahi ɗan Abiyel, ɗan Guni, shi ne kan iyalinsu.
还有古尼的孙子、押比叠的儿子亚希。这都是作族长的。
16 Mutanen Gad sun zauna a Bashan da ƙauyukan da suke kurkusa da shi, da kuma a dukan makiyayan Sharon har zuwa iyaka inda suka kai.
他们住在基列与巴珊和巴珊的乡村,并沙 的郊野,直到四围的交界。
17 Dukan waɗannan sun shiga tarihin zuriya a lokacin mulkin Yotam sarkin Yahuda da Yerobowam sarkin Isra’ila.
这些人在犹大王约坦并在以色列王耶罗波安年间,都载入家谱。
18 Mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse sun kasance da mutane 44,760 shiryayyu don aikin soja, jarumawan da za su iya riƙe garkuwa da takobi, waɗanda suke iya yin amfani da baka, waɗanda kuma aka horar don yaƙi.
吕便人、迦得人,和玛拿西半支派的人,能拿盾牌和刀剑、拉弓射箭、出征善战的勇士共有四万四千七百六十名。
19 Suka yi yaƙi da Hagirawa, Yetur, Nafish da Nodab.
他们与夏甲人、伊突人、拿非施人、挪答人争战。
20 Aka taimake su a yaƙin, Allah kuma ya ba da Hagirawa da dukan abokansu gare su, domin sun yi kuka gare shi a lokacin yaƙin. Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi.
他们得了 神的帮助,夏甲人和跟随夏甲的人都交在他们手中;因为他们在阵上呼求 神,倚赖 神, 神就应允他们。
21 Suka ƙwace dabbobin Hagirawa, raƙuma dubu hamsin, tumaki dubu ɗari biyu da hamsin da kuma jakuna dubu biyu. Suka kuma kame mutane dubu ɗari ɗaya,
他们掳掠了夏甲人的牲畜,有骆驼五万,羊二十五万,驴二千;又有人十万。
22 waɗansu suka mutu, domin yaƙin na Allah ne. Suka zauna a ƙasar har lokacin da aka kai su zaman bauta.
敌人被杀仆倒的甚多,因为这争战是出乎 神。他们就住在敌人的地上,直到被掳的时候。
23 Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon).
玛拿西半支派的人住在那地。从巴珊延到巴力·黑们、示尼珥与黑门山。
24 Waɗannan su ne kawunan iyalansu. Efer, Ishi, Eliyel, Azriyel, Irmiya, Hodawiya da Yadiyel. Su jarumawa ne, sanannu, su ne kuma kawunan iyalansu.
他们的族长是以弗、以示、以列、亚斯列、耶利米、何达威雅、雅叠,都是大能的勇士,是有名的人,也是作族长的。
25 Amma ba su yi aminci da Allahn kakanninsu ba, suka kuma yi karuwanci ga waɗansu allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu.
他们得罪了他们列祖的 神,随从那地之民的神行邪淫;这民就是 神在他们面前所除灭的。
26 Saboda haka Allah na Isra’ila ya zuga ruhun Ful sarkin Assuriya (wato, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya), wanda ya kwashe mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse zuwa zaman bauta. Ya kwashe su zuwa Hala, Habor, Hara da kuma kogin Gozan, inda suke har wa yau.
故此,以色列的 神激动亚述王普勒和亚述王提革拉·毗列色的心,他们就把吕便人、迦得人、玛拿西半支派的人掳到哈腊、哈博、哈拉与歌散河边,直到今日还在那里。

< 1 Tarihi 5 >