< 1 Tarihi 4 >

1 Zuriyoyin Yahuda su ne, Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal.
유다의 아들들은 베레스와 헤스론과 갈미와 훌과 소발이라
2 Reyahiya ɗan Shobal shi ne mahaifin Yahat, Yahat shi ne mahaifin Ahumai da Lahad. Waɗannan su ne gidajen Zoratiyawa.
소발의 아들 르아야는 야핫을 낳았고 야핫은 아후매와 라핫을 낳았으니 이는 소라 사람의 족속이며
3 Waɗannan su ne’ya’yan Etam. Yezireyel, Ishma da Idbash.’Yar’uwarsu ita ce Hazzelelfoni.
에담 조상의 자손들은 이스르엘과 이스마와 잇바스와 저희의 매제 하술렐보니와
4 Fenuwel shi ne mahaifin Gedor, kuma Ezer shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata da mahaifin Betlehem.
그들의 아비 브누엘과 후사의 아비 에셀이니 이는 다 베들레헴의 아비 에브라다의 맏아들 훌의 소생이며
5 Asshur mahaifin Tekowa yana da mata biyu, Hela da Na’ara.
드고아의 아비 아스훌의 두 아내는 헬라와 나아라라
6 Na’ara ta haifi Ahuzzam, Hefer, Temeni da Hawahashtari. Waɗannan su ne zuriyar Na’ara.
나아라는 그로 말미암아 아훗삼과 헤벨과 데므니와 하아하스다리를 낳았으니 이는 나아라의 소생이요
7 ’Ya’yan Hela maza su ne, Zeret, Zohar, Etnan,
헬라의 아들들은 세렛과 이소할과 에드난이며
8 da Koz. Koz ne mahaifin Anub da Hazzobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.
고스는 아눕과 소베바와 하룸의 아들 아하헬 족속들을 낳았으며
9 Yabez ya fi’yan’uwansa martaba. Mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, tana cewa, “Na haife shi da azaba.”
야베스는 그 형제보다 존귀한 자라 그 어미가 이름하여 야베스라 하였으니 이는 내가 수고로이 낳았다 함이었더라
10 Yabez ya yi kuka ga Allah na Isra’ila ya ce, “Ka yi mini albarka ka fadada yankina! Bari hannunka yă kasance tare da ni, yă kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni, don kada in shiga wahala.” Sai Allah ya ji roƙonsa.
야베스가 이스라엘 하나님께 아뢰어 가로되 원컨대 주께서 내게 복에 복을 더하사 나의 지경을 넓히시고 주의 손으로 나를 도우사 나로 환난을 벗어나 근심이 없게 하옵소서 하였더니 하나님이 그 구하는 것을 허락하셨더라
11 Kelub, ɗan’uwan Shuha, shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton.
수하의 형 글룹이 므힐을 낳았으니 므힐은 에스돈의 아비요
12 Eshton shi ne mahaifin Bet-Rafa, Faseya da Tehinna wanda ya haifi Ir Nahash. Waɗannan su ne mutanen Reka.
에스돈은 베드라바와 바세아와 이르나하스의 아비 드힌나를 낳았으니 이는 다 레가 사람이며
13 ’Ya’yan Kenaz maza su ne, Otniyel da Serahiya.’Ya’yan Otniyel maza su ne, Hatat da Meyonotai.
그나스의 아들들은 옷니엘과 스라야요 옷니엘의 아들은 하닷이며
14 Meyonotai shi ne mahaifin Ofra. Serahiya shi ne mahaifin Yowab, mahaifin Ge-Harashim. An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne.
므오노대는 오브라를 낳았고 스라야는 요압을 낳았으니 요압은 게하라심의 조상이라 저희들은 공장이었더라
15 ’Ya’yan Kaleb ɗan Yefunne maza su ne, Iru, Ela da Na’am. Ɗan Ela shi ne, Kenaz.
여분네의 아들 갈렙의 자손은 이루와 엘라와 나암과 엘라의 자손과 그나스요
16 ’Ya’yan Yahallelel su ne, Zif, Zifa, Tiriya da Asarel.
여할렐렐의 아들은 십과 시바와 디리아와 아사렐이요
17 ’Ya’yan Ezra maza su ne, Yeter, Mered, Efer da Yalon. Ɗaya daga cikin matan Mered ta haifi Miriyam, Shammai da Ishba wanda ya haifi Eshtemowa.
에스라의 아들들은 예델과 메렛과 에벨과 얄론이며 메렛은 미리암과 삼매와 에스도모아의 조상 이스바를 낳았으니
18 (Matarsa mutuniyar Yahuda kuwa ta haifi Yared mahaifin Gedor, Heber mahaifin Soko, da kuma Yekutiyel mahaifin Zanowa.) Waɗannan su ne’ya’yan Bitiya’yar Fir’auna, wadda Mered ya aura.
이는 메렛의 취한 바로의 딸 비디아의 아들들이며 또 그 아내 여후디야는 그돌의 조상 예렛과 소고의 조상 헤벨과 사노아의 조상 여구디엘을 낳았으며
19 ’Ya’yan matar Hodiya,’yar’uwar Naham su ne, suka haifi Keyila Bagarme, da Eshtemowa mutumin Ma’aka.
나함의 누이인 호디야의 아내의 아들들은 가미 사람 그일라의 아비와 마아가 사람 에스드모아며
20 ’Ya’yan Shimon maza su ne, Amnon, Rinna, Ben-Hanan da Tilon. Zuriyar Ishi su ne, Zohet da Ben-Zohet.
시몬의 아들들은 암논과 린나와 벤하난과 딜론이요 이시의 아들들은 소헷과 벤소헷이더라
21 ’Ya’yan Shela ɗan Yahuda maza su ne, Er mahaifin Leka, La’ada mahaifin Maresha da kuma gidajen masu aikin lilin a Bet-Ashbeya,
유다의 아들 셀라의 자손은 레가의 아비 에르와 마레사의 아비 라아다와 세마포 짜는 자의 집 곧 아스베야의 집 족속과
22 da Yokim, mutanen Kozeba, da Yowash da Saraf wanda ya yi mulkin Mowab da kuma Yashubi Lehem (Waɗannan rubutattun tarihi ne na tun dā.)
또 요김과 고세바 사람들과 요아스와 모압을 다스리던 사람과 야수비네헴이니 이는 다 옛 기록에 의지한 것이라
23 Su ne maginan tukwane waɗanda suka zauna a Netayim da Gedera; sun zauna a can suka kuma yi wa sarki aiki.
이 모든 사람은 옹기장이가 되어 수풀과 산울 가운데 거하는 자로서 거기서 왕과 함께 거하여 왕의 일을 하였더라
24 Zuriyar Simeyon su ne, Nemuwel, Yamin, Yarib, Zera da Shawulu;
시므온의 아들들은 느무엘과 야민과 야립과 세라와 사울이요
25 Shawulu ya haifi Shallum, Shallum ya haifi Mibsam. Mibsam ya haifi Mishma.
사울의 아들은 살룸이요 그 아들은 밉삼이요 그 아들은 미스마요
26 Zuriyar Mishma su ne, Hammuwel ɗansa, wanda ya haifi Zakkur, shi Zakkur kuma ya haifi Shimeyi.
미스마의 아들은 함무엘이요 그 아들은 삭굴이요 그 아들은 시므이라
27 Shimeyi yana da’ya’ya maza goma sha shida da’ya’ya mata shida, amma’yan’uwansa ba su da’ya’ya da yawa; saboda haka gidansu gaba ɗaya ba tă zama mai mutane da yawa kamar mutanen Yahuda ba.
시므이는 아들 열여섯과 딸 여섯이 있으나 그 형제에게는 자녀가 몇이 못되니 그 온 족속이 유다 자손처럼 번성하지 못하였더라
28 Sun zauna a Beyersheba, Molada, Hazar Shuwal,
시므온 자손의 거한 곳은 브엘세바와 몰라다와 하살수알과
29 Bilha, Ezem, Tolad
빌하와 에셈과 돌랏과
30 Betuwel, Horma, Ziklag,
브두엘과 호르마와 시글락과
31 Bet-Markabot, Hazar-Susim, Bet-Biri da Sha’arayim. Waɗannan su ne garuruwansu har lokacin mulkin Dawuda.
벧말가봇과 하살수심과 벧비리와 사아라임이니 다윗 왕 때까지 이 모든 성읍이 저희에게 속하였으며
32 Ƙauyukan da suke kewayensu su ne Etam, Ayin, Rimmon, Token da Ashan, garuruwa biyar;
그 향촌은 에담과 아인과 림몬과 도겐과 아산 다섯 성읍이요
33 da kuma dukan ƙauyuka kewaye da waɗannan garuruwa har zuwa Ba’al. Waɗannan ne wuraren zamansu. Suka kuma ajiye tarihin zuriya.
또 그 각 성읍 사면에 촌이 있어 바알까지 미쳤으니 시므온 자손의 주소가 이러하고 각기 보계가 있더라
34 Zuriyar Simeyon ta ƙunshi Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya.
또 메소밥과 야믈렉과 아마시야의 아들 요사와
35 Akwai Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya. Yoshibiya ɗan Seraya ne. Serahiya kuma ɗan Asiyel ne.
요엘과 아시엘의 증손 스라야의 손자 요시비야의 아들 예후와
36 Akwai Eliyohenai da Ya’akoba, da Yeshohahiya, da Asahiya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benahiya.
또 엘료에내와 야아고바와 여소하야와 아사야와 아디엘과 여시미엘과 브나야와
37 Akwai Ziza ɗan Shifi. Shifi ɗan Allon ne. Allon ɗan Yedahiya ne. Yedahiya ɗan Shimri ne. Shimri kuma ɗan Shemahiya ne.
또 스마야의 오대손 시므리의 현손 여다야의 증손 알론의 손자 시비의 아들 시사니
38 Mutanen da aka jera sunayensu a bisa, shugabannin gidajensu ne. Iyalansu sun ƙaru sosai,
이 위에 녹명된 자는 다 그 본족의 족장이라 그 종족이 더욱 번성한지라
39 suka tafi bayan garin Gedor wajajen gabashin kwari suna neman makiyaya domin garkunansu.
저희가 그 양떼를 위하여 목장을 구하고자 하여 골짜기 동편 그돌 지경에 이르러
40 Suka sami makiyaya mai ciyawa mai kyau, ƙasar kuma tana da fāɗi, da salama, kuma zaman lafiya. A dā waɗansu mutanen Ham sun zauna a can.
아름답고 기름진 목장을 발견하였는데 그 땅이 광활하고 안정하니 이는 옛적부터 거기 거한 사람은 함의 자손인 까닭이라
41 Mutanen da aka jera sunayensu sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Suka yaƙi mutanen Ham a wuraren zamansu, haka kuma suka yi da Meyunawa da suke can, suka hallaka su ƙaƙaf, yadda yake har yă zuwa yau. Sa’an nan suka zauna a wurin, gama akwai makiyaya domin garkunansu.
이 위에 녹명된 자가 유다 왕 히스기야 때에 가서 저희의 장막을 쳐서 파하고 거기 있는 모우님 사람을 쳐서 진멸하고 대신하여 오늘까지 거기 거하였으니 이는 그 양떼를 먹일 목장이 거기 있음이며
42 Mutum ɗari biyar na waɗannan mutane Simeyon, waɗanda Felatiya, Neyariya, Refahiya da Uzziyel,’ya’yan Ishi maza suka jagorance, sun mamaye ƙasar tudu ta Seyir.
또 시므온 자손 중에 오백 명이 이시의 아들 블라댜와 느아랴와 르바야와 웃시엘로 두목을 삼고 세일 산으로 가서
43 Suka karkashe raguwar Amalekawan da suka tsere, suka kuma zauna a can har yă zuwa yau.
피하여 남아 있는 아말렉 사람을 치고 오늘까지 거기 거하였더라

< 1 Tarihi 4 >