< 1 Tarihi 3 >
1 Waɗannan su ne’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron. Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;
2 na ukun, Absalom ɗan Ma’aka’yar Talmai sarkin Geshur; na huɗun, Adoniya ɗan Haggit;
3 na biyar, Shefatiya ɗan Abital; da kuma na shida, Itireyam ta wurin matarsa Egla.
4 Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida. Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku,
5 kuma waɗannan su ne yaran da aka haifa masa a can. Shimeya, Shobab, Natan da Solomon. Waɗannan huɗu ne Bat-shuwa’yar Ammiyel ta haifa.
6 Akwai kuma Ibhar, Elishama, Elifelet,
7 Noga, Nefeg, Yafiya,
8 Elishama, Eliyada da Elifelet, su tara ne duka.
9 Dukan waɗannan’ya’yan Dawuda ne maza, ban da’ya’yansa maza ta wurin ƙwarƙwaransa. Tamar ita ce’yar’uwarsu.
10 Zuriyar Solomon su ne Rehobowam, da Abiya, da Asa, da Yehoshafat,
11 da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,
12 da Amaziya, da Azariya, da Yotam,
13 da Ahaz, da Hezekiya da Manasse,
14 da Amon, da Yosiya.
15 ’Ya’yan Yosiya maza su ne, Yohanan ɗan fari, Yehohiyakim ɗa na biyu, Zedekiya ɗa na uku Shallum ɗa na huɗu.
16 Magādan Yehohiyakim su ne, Yekoniya ɗansa, da Zedekiya.
17 Zuriyar Yekoniya kamamme su ne, Sheyaltiyel,
18 Malkiram, Fedahiya, Shenazzar, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya.
19 ’Ya’yan Fedahiya su ne, Zerubbabel da Shimeyi.’Ya’yan Zerubbabel maza su ne, Meshullam da Hananiya. Shelomit ce’yar’uwarsu.
20 Akwai kuma waɗansu biyar, Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya da Yushab-Hesed.
21 Zuriyar Hananiya su ne, Felatiya da Yeshahiya, Refahiya, Arnan, Obadiya da Shekaniya.
22 Zuriyar Shekaniya su ne, Shemahiya da’ya’yansa maza. Hattush, Igal, Bariya, Neyariya da Shafat, su shida ne duka.
23 ’Ya’yan Neyariya maza su ne, Eliyohenai, Hezekiya da Azrikam, su uku ne duka.
24 ’Ya’yan Eliyohenai su ne, Hodawiya, Eliyashib, Felahiya, Akkub, Yohanan, Delahiya da Anani, su bakwai ne duka.