< 1 Tarihi 29 >

1 Sa’an nan Sarki Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ɗana Solomon, wanda Allah ya zaɓa, matashi ne, kuma bai gogu ba. Aikin yana da yawa, domin wannan ƙasaitaccen ginin ba na mutum ba ne, na Ubangiji Allah ne.
[達味勸捐]達味王又對全會眾說:「我的兒子撒羅滿,天主所特天主;
2 Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim.
為此,我竭盡力量為我天主的殿宇,預備了金子作金器,銀子作銀器,銅作銅器,鐵作鐵器,木作木器,且有紅瑪瑙、可鑲嵌的寶石、孔雀石、斑色石、各種玉石,以及很多大理石。
3 Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali,
此外,因為我愛我天主的殿宇,除了我為建築聖殿所準備的以外,我還將我私蓄的金銀,獻給我天主的殿宇:
4 talenti dubu uku na zinariya (zinariyar Ofir) da tacecciyar azurfa dubu bakwai; don adon bangon gine-ginen,
就是敖非爾金子三千「塔冷通,」純銀七千「塔冷通,」為包殿內的牆壁;
5 don aikin zinariya da kuma aikin azurfa, don kuma dukan aikin da gwanaye za su yi. Yanzu fa wa yake da niyya yă miƙa kansa a yau don Ubangiji?”
金子用來製造金器,銀子用來製造銀器,和匠人所應作的一切巧工。今天誰自願給上主捐獻呢﹖」
6 Sai shugabannin iyalai, shugabannin kabilan Isra’ila, manyan hafsoshin mayaƙa dubu-dubu da manyan hafsoshi mayaƙa ɗari-ɗari, da shugabannin lura da ayyukan sarki suka yi bayarwa da yardar rai.
於是各族長、以色列各支派的首領、千夫長、百夫長以及掌管君王勞役的主管,都自願捐獻。
7 Suka bayar talenti dubu biyar na zinariya, talenti dubu goma na azurfa, talenti dubu goma sha takwas na tagulla da talenti dubu ɗari na ƙarfe don aiki a haikalin Allah.
為了天主殿宇的用途,他們捐獻了五千「塔冷通」金子,一萬「達理克,」一萬「塔冷通」銀子,一暗八千「塔冷通」銅和十萬「塔冷通」鐵。
8 Duk waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka ba da su ga Yehiyel mutumin Gershon ma’ajin haikalin Ubangiji.
凡有寶石的,都交入上主殿內府庫裏,由革爾雄人耶希耳保管。
9 Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai.
百姓都因這些人甘願捐獻而高興,因為他們都甘心情願向上主捐獻;達味君王也非常高興。[達味讚頌上主]
10 Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa, “Yabo gare ka, ya Ubangiji, Allah na mahaifinmu Isra’ila, har abada abadin.
達味遂在全會眾面前讚頌上主說:「上主,我們的祖先以色列的天主應受讚美,從永遠直到永遠!
11 Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.
上主! 偉大、能力、榮耀、壯麗和威嚴都歸於你,因為上天下地所有的一切都是你的。上主! 王權屬於你,你應受舉揚為萬有的元首。
12 Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.
富貴和光榮由你而來,你是一切的主宰;力量和權能在你手中;人強大,人昌盛,都出於你手。
13 Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka, muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.
我們的天主,現在我們稱頌你,讚揚你榮耀的名。
14 “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.
我算什麼﹖我的百姓又算什麼﹖竟有能力如此甘願捐獻﹖其實一切是由你而來,我們只是將由你手中得來的,再奉獻給你。
15 Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya.
我們在你面前是外方人,是旅居作客的,一如我們的祖先;我們在世上的時日有如陰影,不能持久。
16 Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne.
上主我們的天主! 我們為建築敬拜你聖名的殿宇所預備的這一切財物,都是由你而來,也完全是你的。
17 Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka.
我的天主! 我知道你考驗人心,你喜愛正直,我即以正直的心自願獻上這一切,並且我現在很喜歡看見你在這裏的百姓,都自願向你捐獻。
18 Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya.
上主,我們祖先亞巴郎、依撒格、以色列的天主! 求你永遠使你的人民保存這種心思意願,令他們的心靈堅定於你。
19 Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.”
求你賜給我兒撒羅滿一顆純全的心,遵守你的誡命、你的法律和你的典章,一一實行,用我所準備的來建築殿宇。」
20 Sa’an nan Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ku yabi Ubangiji Allahnku.” Saboda haka suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu; suka rusuna suka kuma fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji da kuma sarki.
達味對全會眾說:「你們應該讚頌上主,你們的天主! 」全會眾便讚頌了上主,他們祖先的天主,向上主,及君王俯首下拜。[撒羅滿登極]
21 Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila.
次日,他向上主獻了全燔祭:牛犢一千,公山羊一千,羔羊一千,以及同獻的奠祭,並為以色列民眾獻了許多犧牲。
22 Suka ci suka sha da farin ciki mai girma a gaban Ubangiji a wannan rana. Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist.
那天,他們在上主面前,歡天喜地地吃喝,以後,他們二次立達味的兒子撒羅滿為王,給他傅油,為上主作人君;又給匝多克傅油,立他為大司祭。
23 Saboda haka Solomon ya zauna a kujerar sarautar Ubangiji a matsayin sarki a maimakon mahaifinsa Dawuda. Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya.
於是撒羅滿坐在上主的寶座上,代他父親達味為王;他非常順利,全以色列都服從他。
24 Dukan shugabanni da jarumawa, har ma da dukan’ya’yan Sarki Dawuda maza, suka yi alkawari za su yi wa Sarki Solomon biyayya.
所有的首領、勇士以及達味王所有的兒子,都屬撒羅滿王權下。
25 Ubangiji ya ɗaukaka Solomon sosai a idon dukan Isra’ila, ya kuma ba shi darajar sarauta yadda babu sarki a Isra’ilan da ya taɓa samu.
上主在全以色列民眾面前,特別高舉了撒羅滿,賜予他君王的威嚴,勝過以前所有的以色列君王。[達味逝世]
26 Dawuda ɗan Yesse ya zama sarki a bisa dukan Isra’ila.
葉瑟的兒子達味統治了全以色列,
27 Ya yi mulki a bisa Isra’ila shekaru arba’in, shekaru bakwai a Hebron da kuma shekaru talatin da uku a Urushalima.
統治以色列為時凡四十年:在赫貝龍為王七年,在耶路撒冷為王三十三年。
28 Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki.
他死時年紀很大,享了高壽和榮華富貴;他的兒子撒羅滿繼位為王。
29 Game da ayyukan mulkin Sarki Dawuda, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin Sama’ila mai duba, tarihin annabi Natan da kuma tarihin Gad mai duba,
達味王的前後事蹟,都記載在先見者撒慕爾言行錄、先知納堂言行錄和先見者加得言行錄上。
30 tare da yadda mulkinsa da ikonsa da yanayin da suka kewaye shi da Isra’ila da kuma dukan masarautai na dukan sauran ƙasashe.
他與國家有關的大事、他的武功,以及他與以色列和四鄰各國所經歷的史事,全都記載在這些書上。

< 1 Tarihi 29 >