< 1 Tarihi 28 >

1 Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.
ויקהל דויד את כל שרי ישראל שרי השבטים ושרי המחלקות המשרתים את המלך ושרי האלפים ושרי המאות ושרי כל רכוש ומקנה למלך ולבניו עם הסריסים והגבורים ולכל גבור חיל--אל ירושלם
2 Sarki Dawuda ya miƙe tsaye ya ce, “Ku saurare ni,’yan’uwana da kuma mutanena. Na yi niyya in gina gida a matsayin wurin hutu domin akwatin alkawarin Ubangiji, domin zatin Allahnmu, na kuma yi shiri don in gina shi.
ויקם דויד המלך על רגליו ויאמר שמעוני אחי ועמי אני עם לבבי לבנות בית מנוחה לארון ברית יהוה ולהדם רגלי אלהינו והכינותי לבנות
3 Amma Allah ya ce mini, ‘Ba za ka gina gida domin Sunana ba, saboda kai mayaƙi ne ka kuma zub da jini.’
והאלהים אמר לי לא תבנה בית לשמי כי איש מלחמות אתה ודמים שפכת
4 “Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila.
ויבחר יהוה אלהי ישראל בי מכל בית אבי להיות למלך על ישראל לעולם--כי ביהודה בחר לנגיד ובבית יהודה בית אבי ובבני אבי--בי רצה להמליך על כל ישראל
5 Cikin dukan’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila.
ומכל בני--כי רבים בנים נתן לי יהוה ויבחר בשלמה בני--לשבת על כסא מלכות יהוה על ישראל
6 Ya ce mini, ‘Solomon ɗanka shi ne wanda zai gina gidana da filayen da suke kewaye da shi, gama na zaɓe shi yă zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa.
ויאמר לי--שלמה בנך הוא יבנה ביתי וחצרותי כי בחרתי בו לי לבן ואני אהיה לו לאב
7 Zan kafa mulkinsa har abada in bai kauce ga kiyaye umarnaina da dokokina ba, yadda ake yi a wannan lokaci.’
והכינותי את מלכותו עד לעולם אם יחזק לעשות מצותי ומשפטי--כיום הזה
8 “Saboda haka yanzu ina umartanku a gaban dukan Isra’ila da na taron jama’ar Ubangiji, da kuma a kunnuwan Allahnmu. Ku yi hankali ku kiyaye dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa ku kuma bar wa zuriyarku gādo har abada.
ועתה לעיני כל ישראל קהל יהוה ובאזני אלהינו שמרו ודרשו כל מצות יהוה אלהיכם--למען תירשו את הארץ הטובה והנחלתם לבניכם אחריכם עד עולם
9 “Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada.
ואתה שלמה בני דע את אלהי אביך ועבדהו בלב שלם ובנפש חפצה--כי כל לבבות דורש יהוה וכל יצר מחשבות מבין אם תדרשנו ימצא לך ואם תעזבנו יזניחך לעד
10 Ka lura fa, gama Ubangiji ya zaɓe ka don ka gina haikali a matsayin wuri mai tsarki. Ka yi ƙarfin hali ka kuma yi aiki.”
ראה עתה כי יהוה בחר בך לבנות בית למקדש--חזק ועשה
11 Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Solomon tsari domin shirayin haikalin, gine-ginensa, ɗakunan ajiyarsa, ɓangarorin bisansa, ɗakunan cikinsa da kuma wurin kafara.
ויתן דויד לשלמה בנו את תבנית האולם ואת בתיו וגנזכיו ועליתיו וחדריו הפנימים--ובית הכפרת
12 Ya ba shi tsarin dukan abin da Ruhu ya sa a zuciyarsa saboda filayen haikalin Ubangiji da ɗakunan kewaye, da ma’ajin haikalin Allah da kuma baitulmali na kayayyakin da aka keɓe.
ותבנית כל אשר היה ברוח עמו לחצרות בית יהוה ולכל הלשכות סביב--לאצרות בית האלהים ולאצרות הקדשים
13 Ya ba shi tsari game ɓangarori na firistoci da Lawiyawa, da game dukan aikin hidima a cikin haikalin Ubangiji, da kuma game da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a hidima.
ולמחלקות הכהנים והלוים ולכל מלאכת עבודת בית יהוה ולכל כלי עבודת בית יהוה
14 Ya kimanta yawan zinariya don dukan kayayyakin zinariyar da za a yi amfani a kowane irin hidima, da yawan azurfa don dukan kayayyakin azurfan da za a yi amfani a kowace irin hidima.
לזהב במשקל לזהב לכל כלי עבודה ועבודה לכל כלי הכסף במשקל לכל כלי עבודה ועבודה
15 Da yawan zinariya don wurin ajiye fitilan fitilu da fitilunsu, da yawan zinariyan da za a yi amfani don kowace fitila da wurin ajiye fitilanta; da kuma yawan azurfa don kowane wurin ajiye fitila da fitilunsa bisa ga yadda za a yi amfani da kowane wurin ajiye fitila;
ומשקל למנרות הזהב ונרתיהם זהב במשקל מנורה ומנורה ונרתיה ולמנרות הכסף במשקל למנורה ונרתיה כעבודת מנורה ומנורה
16 yawan zinariya don kowane tebur saboda burodi mai tsaki; da kuma yawan azurfa saboda teburin azurfa;
ואת הזהב משקל לשלחנות המערכת לשלחן ושלחן וכסף לשלחנות הכסף
17 yawan zinariya zalla, don cokula masu yatsu, kwanonin yayyafawa ruwa da kuma tuluna; yawan zinariya don kowane kwanon zinariya; yawan azurfa don kowane kwanon azurfa;
והמזלגות והמזרקות והקשות זהב טהור ולכפורי הזהב במשקל לכפור וכפור ולכפורי הכסף במשקל לכפור וכפור
18 da kuma yawan tacecciyar zinariya don bagaden turare. Ya kuma ba shi tsari don keken yaƙi, wato, kerubobin zinariyar da suka miƙe fikafikansu suka inuwantar da akwatin alkawarin Ubangiji.
ולמזבח הקטרת זהב מזקק במשקל ולתבנית המרכבה הכרובים זהב לפרשים וסככים על ארון ברית יהוה
19 Dawuda ya ce, “Dukan wannan, ina da shi a rubuce daga hannun Ubangiji zuwa gare ni, ya kuma ba ni ganewa cikin dukan tsarin fasalin, filla-filla.”
הכל בכתב מיד יהוה עלי השכיל--כל מלאכות התבנית
20 Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, “Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya, gama Ubangiji Allah, Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ko yă yashe ka ba, sai an gama dukan aikin saboda hidimar haikalin Ubangiji.
ויאמר דויד לשלמה בנו חזק ואמץ ועשה--אל תירא ואל תחת כי יהוה אלהים אלהי עמך--לא ירפך ולא יעזבך עד לכלות כל מלאכת עבודת בית יהוה
21 Sassan firistoci da na Lawiyawa suna a shirye domin dukan aiki a haikalin Allah, kuma kowane gwani mai niyya a kowace sana’a, zai taimake ka a cikin dukan aikin. Shugabanni da dukan mutane za su yi biyayya da kowane umarninka.”
והנה מחלקות הכהנים והלוים לכל עבודת בית האלהים ועמך בכל מלאכה לכל נדיב בחכמה לכל עבודה והשרים וכל העם לכל דבריך

< 1 Tarihi 28 >