< 1 Tarihi 26 >

1 Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne, Daga Korayawa, Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin’ya’yan Asaf maza.
למחלקות לשערים--לקרחים משלמיהו בן קרא מן בני אסף
2 Meshelemiya yana da’ya’ya maza. Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu,
ולמשלמיהו בנים--זכריהו הבכור ידיעאל השני זבדיהו השלישי יתניאל הרביעי
3 Elam na biyar, Yehohanan na shida da Eliyehoyenai na bakwai.
עילם החמישי יהוחנן הששי אליהועיני השביעי
4 Obed-Edom shi ma yana da’ya’ya maza. Shemahiya ɗan fari, Yehozabad na biyu, Yowa na uku, Sakar na huɗu Netanel na biyar,
ולעבד אדם בנים--שמעיה הבכור יהוזבד השני יואח השלשי ושכר הרביעי ונתנאל החמישי
5 Ammiyel na shida, Issakar na bakwai da Feyuletai na takwas. (Gama Allah ya albarkace Obed-Edom.)
עמיאל הששי יששכר השביעי פעלתי השמיני כי ברכו אלהים
6 Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai.
ולשמעיה בנו נולד בנים הממשלים לבית אביהם כי גבורי חיל המה
7 ’Ya’yan Shemahiya maza su ne, Otni, Rafayel, Obed da Elzabad; danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne.
בני שמעיה עתני ורפאל ועובד אלזבד אחיו--בני חיל אליהו וסמכיהו
8 Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka.
כל אלה מבני עבד אדם המה ובניהם ואחיהם איש חיל בכח לעבדה--ששים ושנים לעבד אדם
9 Meshelemiya yana da’ya’ya maza da kuma’yan’uwa, waɗanda jarumawa ne, su 18 ne duka.
ולמשלמיהו בנים ואחים בני חיל--שמונה עשר
10 Hosa dangin Merari yana da’ya’ya maza. Shimri na fari (ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, mahaifinsa ya sa shi na fari),
ולחסה מן בני מררי בנים--שמרי הראש כי לא היה בכור וישימהו אביהו לראש
11 Hilkiya ne na biyu, Tabaliya ne na uku sai kuma Zakariya na huɗu.’Ya’ya da dangin Hosa su 13 ne duka.
חלקיהו השני טבליהו השלשי זכריהו הרבעי כל בנים ואחים לחסה שלשה עשר
12 Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi.
לאלה מחלקות השערים לראשי הגברים משמרות--לעמת אחיהם לשרת בבית יהוה
13 Aka jefa ƙuri’u don kowace ƙofa bisa ga iyalansu, ƙarami da babba.
ויפילו גורלות כקטן כגדול לבית אבותם--לשער ושער
14 Ƙuri’a don Ƙofar Gabas ta fāɗo a kan Shelemiya. Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa.
ויפל הגורל מזרחה לשלמיהו וזכריהו בנו יועץ בשכל הפילו גורלות ויצא גורלו צפונה
15 Ƙuri’a don Ƙofar Kudu ta fāɗo a kan Obed-Edom, ƙuri’a don ɗakin ajiya kuwa ta fāɗo a kan’ya’yansa maza.
לעבד אדם נגבה ולבניו בית האספים
16 Ƙuri’u don Ƙofar Yamma da kuma Ƙofar Shalleket a hanyar bisa suka fāɗo a kan Shuffim da Hosa. Aikin tsaro bisa ga mai tsaro.
לשפים ולחסה למערב עם שער שלכת במסלה העולה משמר לעמת משמר
17 Akwai Lawiyawa shida da suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu-biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.
למזרח הלוים ששה לצפונה ליום ארבעה לנגבה ליום ארבעה ולאספים שנים שנים
18 Game da filin waje ta yamma kuwa, akwai masu tsaro huɗu a hanya da kuma biyu a filin kansa.
לפרבר למערב--ארבעה למסלה שנים לפרבר
19 Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari.
אלה מחלקות השערים לבני הקרחי ולבני מררי
20 ’Yan’uwansu Lawiyawa kuwa su ne suke lura da ma’ajin gidan Allah da kuma baitulmali don kayayyakin da aka keɓe.
והלוים--אחיה על אוצרות בית האלהים ולאצרות הקדשים
21 Ladan ɗan Gershon ne, kuma kaka ga iyalai masu yawa, har ma da iyalin ɗansa Yehiyeli,
בני לעדן בני הגרשני ללעדן ראשי האבות ללעדן הגרשני--יחיאלי
22 ’ya’yan Yehiyeli maza su ne, Zetam da ɗan’uwansa Yowel. Su ne suke kula da ma’ajin haikalin Ubangiji.
בני יחיאלי--זתם ויואל אחיו על אצרות בית יהוה
23 Daga zuriyar Amram, Izhar, mutanen Hebron da kuma Uzziyel, su ma aka ba su aiki.
לעמרמי ליצהרי לחברוני לעזיאלי
24 Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami’i mai lura da baitulmali.
ושבאל בן גרשום בן משה נגיד על האצרות
25 Danginsa na wajen Eliyezer su ne, Rehabiya, Yeshahiya, Yoram, Zikri da Shelomit.
ואחיו לאליעזר--רחביהו בנו וישעיהו בנו וירם בנו וזכרי בנו ושלמות (ושלמית) בנו
26 Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa.
הוא שלמות ואחיו על כל אצרות הקדשים אשר הקדיש דויד המלך וראשי האבות לשרי האלפים והמאות--ושרי הצבא
27 Sun keɓe waɗansu ganimar da aka kwaso a yaƙi don gyaran haikalin Ubangiji.
מן המלחמות ומן השלל הקדישו--לחזק לבית יהוה
28 Shelomit da’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe.
וכל ההקדיש שמואל הראה ושאול בן קיש ואבנר בן נר ויואב בן צרויה--כל המקדיש על יד שלמית ואחיו
29 Daga mutanen Izhar, Kenaniya da’ya’yansa maza su aka sa a ayyukan da ba na haikali ba, su suka zama manya da kuma alƙalai a bisa Isra’ila.
ליצהרי כנניהו ובניו למלאכה החיצונה על ישראל--לשטרים ולשפטים
30 Daga zuriyar Hebron, Hashabiya da danginsa, su jarumawa dubu ɗaya da ɗari bakwai ne, su suke lura da Isra’ila yamma da Urdun don dukan aikin Ubangiji da kuma hidimar sarki.
לחברוני חשביהו ואחיו בני חיל אלף ושבע מאות על פקדת ישראל מעבר לירדן מערבה--לכל מלאכת יהוה ולעבדת המלך
31 Game da zuriyar Hebron kuwa, Yeriya ne babba bisa ga tarihin zuriyar iyalansu. A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka yi binciken tarihi, aka tarar jarumawa cikin zuriyar Hebron suna zama a Yazer cikin Gileyad ne.
לחברוני יריה הראש לחברוני לתלדתיו לאבות--בשנת הארבעים למלכות דויד נדרשו וימצא בהם גבורי חיל ביעזיר גלעד
32 Yeriya yana da’yan’uwa guda dubu biyu da ɗari bakwai, jarumawa da kuma kawunan iyalai, sai Sarki Dawuda ya sa su lura da mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse game da kome da ya shafi Allah da kuma al’amuran sarki.
ואחיו בני חיל אלפים ושבע מאות--ראשי האבות ויפקידם דויד המלך על הראובני והגדי וחצי שבט המנשי לכל דבר האלהים ודבר המלך

< 1 Tarihi 26 >