< 1 Tarihi 25 >

1 Dawuda tare da shugabannin mayaƙa, suka keɓe waɗansu daga’ya’yan Asaf, Heman da Yedutun don hidimar yin annabci, suna amfani da garayu, molaye da ganguna. Ga jerin mutanen da suka yi wannan hidima.
David and some of the temple officials (OR, army commanders) chose some of the descendants of Asaph, Heman, and Jeduthun to be in charge of proclaiming God’s messages, and to play harps and lyres and cymbals. This is a list of the men whom they chose for that work:
2 Daga’ya’yan Asaf, Zakkur, Yusuf, Netaniya da Asarela.’Ya’yan Asaf sun kasance a ƙarƙashin kulawar Asaf, wanda ya yi annabci a ƙarƙashin kulawar sarki.
From the sons of Asaph they chose Zaccur, Joseph, Nethaniah, and Aserelah. Asaph supervised them. And the king appointed Asaph to proclaim God’s messages.
3 Game da Yedutun kuwa, daga’ya’yansa maza. Gedaliya, Zeri, Yeshahiya, Shimeyi, Hashabiya da Mattitiya, su shida ne duka, a ƙarƙashin kulawar mahaifinsu Yedutun, wanda ya yi annabci, yana amfani da garaya a yin godiya da yabon Ubangiji.
From the sons of Jeduthun they chose six men: Gedaliah, Zeri, Jeshaiah, Shimei, Hashabiah, and Mattithiah. Jeduthun supervised them and also proclaimed God’s messages, playing his harp while he thanked and praised Yahweh.
4 Game da Heman kuwa, daga’ya’yansa maza. Bukkiya, Mattaniya, Uzziyel, Shebuwel, Yerimot; Hananiya, Hanani, Eliyata, Giddalti, Romamti-Ezer, Yoshbekasha, Malloti, Hotir da Mahaziyot.
From the sons of Heman, who was one of the king’s prophets, they chose Bukkiah, Mattaniah, Uzziel, Shubael, Jerimoth, Hananiah, Hanani, Eliathah, Giddalti, Romamti-Ezer, Joshbekashah, Mallothi, Hothir, and Mahazioth.
5 Dukan waɗannan’ya’yan Heman ne mai duba na sarki. An ba shi su ta wurin alkawarin Allah don yă ɗaukaka shi. Allah ya ba Heman’ya’ya maza goma sha huɗu da’ya’ya mata uku.
God promised to cause Heman to be strong, so altogether, God have him 14 sons and three daughters.
6 Dukan waɗannan mutane suna a ƙarƙashin kulawar mahaifansu don kaɗe-kaɗe da bushe-bushe a cikin haikalin Ubangiji, da ganguna, molaye da garayu, don hidima a gidan Allah. Asaf, Yedutun da Heman suna ƙarƙashin kulawar sarki.
All those men were supervised by their fathers while they played music in the temple of Yahweh. They played cymbals, lyres, and harps. And their fathers—Asaph, Jeduthun and Heman—were supervised by the king.
7 Da su da danginsu, dukansu su 288 ne kuma horarru da ƙwararru ne a kaɗe-kaɗe da bushe-bushe domin Ubangiji.
Those men and their relatives were all trained and skilled for playing musical instruments in the temple. That was their work for Yahweh. Including their relatives, there were 288 of them.
8 Baba ko yaro, malami ko ɗalibi, duk suka jefa ƙuri’a saboda ayyukan da za su yi.
All of them, including ones who were young and those who were old, cast lots to determine what work they would do.
9 Ƙuri’a ta fari, wadda take don Asaf, ta fāɗo a kan Yusuf,’ya’yansa maza da danginsa, 12 ta biyu a kan Gedaliya, danginsa da’ya’yansa maza, 12
From the family of Asaph, the first ones selected were Joseph and 12 of his sons and relatives.
10 ta uku a kan Zakkur,’ya’yansa da danginsa, 12
Next, Gedaliah and 12 of his sons and relatives were selected.
11 ta huɗu a kan Izri,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Zaccur and 12 of his sons and relatives were selected.
12 ta biyar a kan Netaniya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Nethaniah and 12 of his sons and relatives were selected.
13 ta shida a kan Bukkiya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Bukkiah and 12 of his sons and relatives were selected.
14 ta bakwai a kan Yesarela,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Jesarelah and 12 of his sons and relatives were selected.
15 ta takwas a kan Yeshahiya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Jeshaiah and 12 of his sons and relatives were selected.
16 ta tara a kan Mattaniya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Mattaniah and 12 of his sons and relatives were selected.
17 ta goma a kan Shimeyi,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Shimei and 12 of his sons and relatives were selected.
18 ta goma sha ɗaya a kan Azarel,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Azarel and 12 of his sons and relatives were selected.
19 ta goma sha biyu a kan Hashabiya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Hashabiah and 12 of his sons and relatives were selected.
20 ta goma sha uku a kan Shubayel,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Shubael and 12 of his sons and relatives were selected.
21 ta goma sha huɗu a kan Mattitiya,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Mattithiah and 12 of his sons and relatives were selected.
22 ta goma sha biya a kan Yeremot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Jerimoth and 12 of his sons and relatives were selected.
23 ta goma sha shida a kan Hananiya, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Hananiah and 12 of his sons and relatives were selected.
24 ta goma sha bakwai a kan Yoshbekasha, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Joshbekashah and 12 of his sons and relatives were selected.
25 ta goma sha takwas a kan Hanani, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa 12
Next, Hanani and 12 of his sons and relatives were selected.
26 ta goma sha tara a kan Malloti, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Mallothi and 12 of his sons and relatives were selected.
27 ta ashirin a kan Eliyata, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Eliathah and 12 of his sons and relatives were selected.
28 ta ashirin da ɗaya a kan Hotir, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Hothir and 12 of his sons and relatives were selected.
29 ta ashirin da biyu a kan Giddalti, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Giddalti and 12 of his sons and relatives were selected.
30 ta ashirin da uku a kan Mahaziyot, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa, 12
Next, Mahazioth and 12 of his sons and relatives were selected.
31 ta ashirin da huɗu a kan Romamti-Ezer, na goma sha biya a kan Yerimot,’ya’yansa maza da danginsa 12.
Next, Romamti-Ezer and 12 of his sons and relatives were selected.

< 1 Tarihi 25 >