< 1 Tarihi 24 >
1 Waɗannan su ne sassan’ya’yan Haruna maza.’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
亚伦子孙的班次记在下面:亚伦的儿子是拿答、亚比户、以利亚撒、以他玛。
2 Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci.
拿答、亚比户死在他们父亲之先,没有留下儿子;故此,以利亚撒、以他玛供祭司的职分。
3 Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima.
以利亚撒的子孙撒督和以他玛的子孙亚希米勒,同着大卫将他们的族弟兄分成班次。
4 Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar.
以利亚撒子孙中为首的比以他玛子孙中为首的更多,分班如下:以利亚撒的子孙中有十六个族长,以他玛的子孙中有八个族长;
5 Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.
都掣签分立,彼此一样。在圣所和 神面前作首领的有以利亚撒的子孙,也有以他玛的子孙。
6 Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.
作书记的利未人拿坦业的儿子示玛雅在王和首领,与祭司撒督、亚比亚他的儿子亚希米勒,并祭司利未人的族长面前记录他们的名字。在以利亚撒的子孙中取一族,在以他玛的子孙中取一族。
7 Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib, na biyu a kan Yedahiya,
掣签的时候,第一掣出来的是耶何雅立,第二是耶大雅,
8 na uku a kan Harim, na huɗu a kan Seyorim,
第三是哈琳,第四是梭琳,
9 na biyar a kan Malkiya, na shida a kan Miyamin,
第五是玛基雅,第六是米雅民,
10 na bakwai a kan Hakkoz, na takwas a kan Abiya,
第七是哈歌斯,第八是亚比雅,
11 na tara a kan Yeshuwa, na goma a kan Shekaniya,
第九是耶书亚,第十是示迦尼,
12 na goma sha ɗaya a kan Eliyashib, na goma sha biyu a kan Yakim,
第十一是以利亚实,第十二是雅金,
13 na goma sha uku a kan Huffa, na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab,
第十三是胡巴,第十四是耶是比押,
14 na goma sha biyar a kan Bilga, na goma sha shida a kan Immer,
第十五是璧迦,第十六是音麦,
15 na goma sha shida a kan Hezir, na goma sha takwas a kan Haffizzez,
第十七是希悉,第十八是哈辟悉,
16 na goma sha tara a kan Fetahahiya, na ashirin a kan Ezekiyel,
第十九是毗他希雅,第二十是以西结,
17 na ashirin da ɗaya wa Yakin, na ashirin da biyu a kan Gamul,
第二十一是雅斤,第二十二是迦末,
18 na ashirin da uku wa Delahiya da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya.
第二十三是第来雅,第二十四是玛西亚。
19 Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.
这就是他们的班次,要照耶和华—以色列的 神借他们祖宗亚伦所吩咐的条例进入耶和华的殿办理事务。
20 Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.
利未其余的子孙如下:暗兰的子孙里有书巴业;书巴业的子孙里有耶希底亚。
21 Game da Rehabiya kuwa, daga’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.
利哈比雅的子孙里有长子伊示雅。
22 Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga’ya’yan Shelomot maza, Yahat.
以斯哈的子孙里有示罗摩;示罗摩的子孙里有雅哈。
23 ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
希伯伦 的子孙里有长子耶利雅,次子亚玛利亚,三子雅哈悉,四子耶加面。
24 Ɗan Uzziyel shi ne, Mika; daga’ya’yan Mika maza, Shamir.
乌薛的子孙里有米迦;米迦的子孙里有沙密。
25 Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.
米迦的兄弟是伊示雅;伊示雅的子孙里有撒迦利雅。
26 ’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi. Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno.
米拉利的儿子是抹利、母示、雅西雅;雅西雅的儿子有比挪;
27 ’Ya’yan Merari su ne, daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.
米拉利的子孙里有雅西雅的儿子比挪、朔含、撒刻、伊比利。
28 Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da’ya’ya maza.
抹利的儿子是以利亚撒;以利亚撒没有儿子。
29 Daga Kish, ɗan Kish shi ne, Yerameyel.
基士的子孙里有耶拉篾。
30 Kuma’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu.
母示的儿子是末力、以得、耶利摩。按着宗族这都是利未的子孙。
31 Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.
他们在大卫王和撒督,并亚希米勒与祭司利未人的族长面前掣签,正如他们弟兄亚伦的子孙一般。各族的长者与兄弟没有分别。