< 1 Tarihi 23 >

1 Sa’ad da Dawuda ya tsufa yana kuma da cikakken shekaru, ya sa ɗansa Solomon sarki bisa Isra’ila.
ודויד זקן ושבע ימים וימלך את שלמה בנו על ישראל
2 Ya kuma tattara dukan shugabannin Isra’ila a wuri ɗaya, haka kuma ya yi da firistoci da Lawiyawa.
ויאסף את כל שרי ישראל והכהנים והלוים
3 Aka ƙidaya Lawiyawan da suke’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas.
ויספרו הלוים מבן שלשים שנה ומעלה ויהי מספרם לגלגלתם לגברים שלשים ושמונה אלף
4 Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai.
מאלה לנצח על מלאכת בית יהוה עשרים וארבעה אלף ושטרים ושפטים ששת אלפים
5 Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.”
וארבעת אלפים שערים וארבעת אלפים מהללים ליהוה בכלים אשר עשיתי להלל
6 Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari.
ויחלקם דויד מחלקות לבני לוי לגרשון קהת ומררי
7 Na Gershonawa, Ladan da Shimeyi.
לגרשני לעדן ושמעי
8 ’Ya’yan Ladan maza su ne, Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka.
בני לעדן הראש יחיאל וזתם ויואל--שלשה
9 ’Ya’yan Shimeyi maza su ne, Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka. Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan.
בני שמעי שלמות (שלמית) וחזיאל והרן--שלשה אלה ראשי האבות ללעדן
10 ’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne, Yahat, Zina, Yewush da Beriya. Waɗannan su ne’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka.
ובני שמעי--יחת זינא ויעוש ובריעה אלה בני שמעי ארבעה
11 Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki.
ויהי יחת הראש וזיזה השני ויעוש ובריעה לא הרבו בנים ויהיו לבית אב לפקדה אחת
12 ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka.
בני קהת עמרם יצהר חברון ועזיאל--ארבעה
13 ’Ya’yan Amram maza su ne, Haruna da Musa. Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada.
בני עמרם אהרן ומשה ויבדל אהרן להקדישו קדש קדשים הוא ובניו עד עולם--להקטיר לפני יהוה לשרתו ולברך בשמו עד עולם
14 An ƙidaya aka kuma haɗa’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.
ומשה איש האלהים--בניו יקראו על שבט הלוי
15 ’Ya’yan Musa maza su ne, Gershom da Eliyezer.
בני משה גרשום ואליעזר
16 Zuriyar Gershom su ne, Shebuwel ne ɗan fari.
בני גרשום שבואל הראש
17 Zuriyar Eliyezer su ne, Rehabiya ne ɗan fari. Eliyezer ba shi da waɗansu’ya’ya maza, amma’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa.
ויהיו בני אליעזר רחביה הראש ולא היה לאליעזר בנים אחרים ובני רחביה רבו למעלה
18 ’Ya’yan Izhar maza su ne, Shelomit ne ɗan fari.
בני יצהר שלמית הראש
19 ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.
בני חברון--יריהו הראש אמריה השני יחזיאל השלישי ויקמעם הרביעי
20 ’Ya’yan Uzziyel maza su ne, Mika na fari da Isshiya na biyu.
בני עזיאל--מיכה הראש וישיה השני
21 ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi.’Ya’yan Mali maza su ne, Eleyazar da Kish.
בני מררי מחלי ומושי בני מחלי אלעזר וקיש
22 Eleyazar ya mutu ba’ya’yan maza, yana da’ya’ya mata ne kawai.’Yan’uwansu,’ya’yan Kish maza, suka aure su.
וימת אלעזר ולא היו לו בנים כי אם בנות וישאום בני קיש אחיהם
23 ’Ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka.
בני מושי מחלי ועדר וירמות--שלושה
24 Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji.
אלה בני לוי לבית אבותיהם ראשי האבות לפקודיהם במספר שמות לגלגלתם עשה המלאכה לעבדת בית יהוה--מבן עשרים שנה ומעלה
25 Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada,
כי אמר דויד הניח יהוה אלהי ישראל לעמו וישכן בירושלם עד לעולם
26 Lawiyawa ba sa ƙara bukata su ɗauki tabanakul ko kuwa waɗansu kayayyakin da ake amfani da su a hidima.”
וגם ללוים--אין לשאת את המשכן ואת כל כליו לעבדתו
27 Bisa ga umarnin ƙarshe na Dawuda, za a ƙidaya Lawiyawa daga’yan shekara ashirin ko fiye.
כי בדברי דויד האחרונים המה מספר בני לוי מבן עשרים שנה ולמעלה
28 Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah.
כי מעמדם ליד בני אהרן לעבדת בית יהוה על החצרות ועל הלשכות ועל טהרת לכל קדש--ומעשה עבדת בית האלהים
29 Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa.
וללחם המערכת ולסלת למנחה ולרקיקי המצות ולמחבת ולמרבכת ולכל משורה ומדה
30 Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma
ולעמד בבקר בבקר להדות ולהלל ליהוה וכן לערב
31 da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu.
ולכל העלות עלות ליהוה לשבתות לחדשים ולמעדים--במספר כמשפט עליהם תמיד לפני יהוה
32 A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji.
ושמרו את משמרת אהל מועד ואת משמרת הקדש ומשמרת בני אהרן אחיהם--לעבדת בית יהוה

< 1 Tarihi 23 >