< 1 Tarihi 2 >

1 Waɗannan su ne’ya’yan Isra’ila maza. Ruben, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Zebulun,
אלה בני ישראל ראובן שמעון לוי ויהודה יששכר וזבלון
2 Dan, Yusuf, Benyamin, Naftali, Gad da Asher.
דן יוסף ובנימן נפתלי גד ואשר
3 ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan da Shela. Waɗannan mutum uku Bat-shuwa mutuniyar Kan’ana ce ta haifa masa. Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.
בני יהודה ער ואונן ושלה--שלושה נולד לו מבת שוע הכנענית ויהי ער בכור יהודה רע בעיני יהוה--וימיתהו
4 Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera. Yahuda ya haifi’ya’ya maza biyar ne.
ותמר כלתו ילדה לו את פרץ ואת זרח כל בני יהודה חמשה
5 ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.
בני פרץ חצרון וחמול
6 ’Ya’yan Zera maza su ne, Zimri, Etan, Heman, Kalkol da Darda, su biyar ne.
ובני זרח זמרי ואיתן והימן וכלכל ודרע--כלם חמשה
7 ’Ya’yan Karmi maza su ne, Akar wanda ya kawo masifa wa Isra’ila ta wurin yin abin da aka haramta.
ובני כרמי--עכר עוכר ישראל אשר מעל בחרם
8 Ɗan Etan shi ne, Azariya.
ובני איתן עזריה
9 ’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne, Yerameyel, Ram da Kaleb.
ובני חצרון אשר נולד לו--את ירחמאל ואת רם ואת כלובי
10 Ram shi ne mahaifin Amminadab, Amminadab kuwa shi ne mahaifin Nashon, shugaban mutanen Yahuda.
ורם הוליד את עמינדב ועמינדב הוליד את נחשון נשיא בני יהודה
11 Nashon shi ne mahaifin Salma, Salma shi ne mahaifin Bowaz,
ונחשון הוליד את שלמא ושלמא הוליד את בעז
12 Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse.
ובעז הוליד את עובד ועובד הוליד את ישי
13 Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya,
ואישי הוליד את בכרו את אליאב--ואבינדב השני ושמעא השלשי
14 na huɗun Netanel, na biyar Raddai,
נתנאל הרביעי רדי החמישי
15 na shidan Ozem na bakwai kuma Dawuda.
אצם הששי דויד השבעי
16 ’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel.’Ya’yan Zeruhiya maza guda uku su ne Abishai, Yowab da Asahel.
ואחיתיהם צרויה ואביגיל ובני צרויה אבשי ויואב ועשהאל--שלשה
17 Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel.
ואביגיל ילדה את עמשא ואבי עמשא יתר הישמעאלי
18 Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon.
וכלב בן חצרון הוליד את עזובה אשה--ואת יריעות ואלה בניה ישר ושובב וארדון
19 Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur.
ותמת עזובה ויקח לו כלב את אפרת ותלד לו את חור
20 Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel.
וחור הוליד את אורי ואורי הוליד את בצלאל
21 Daga baya, Hezron ya kwana da’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub.
ואחר בא חצרון אל בת מכיר אבי גלעד והוא לקחה והוא בן ששים שנה ותלד לו את שגוב
22 Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad.
ושגוב הוליד את יאיר ויהי לו עשרים ושלוש ערים בארץ הגלעד
23 (Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.
ויקח גשור וארם את חות יאיר מאתם את קנת ואת בנתיה--ששים עיר כל אלה בני מכיר אבי גלעד
24 Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa.
ואחר מות חצרון בכלב אפרתה ואשת חצרון אביה ותלד לו את אשחור אבי תקוע
25 ’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne, Ram shi ne ɗan fari, sai Buna, Oren, Ozem da Ahiya.
ויהיו בני ירחמאל בכור חצרון הבכור רם ובונה וארן ואצם אחיה
26 Yerameyel yana da wata mata, wadda sunanta Atara; ita ce mahaifiyar Onam.
ותהי אשה אחרת לירחמאל ושמה עטרה היא אם אונם
27 ’Ya’yan Ram maza ɗan farin Yerameyel su ne, Ma’az, Yamin da Eker.
ויהיו בני רם בכור ירחמאל--מעץ וימין ועקר
28 ’Ya’yan Onam maza su ne, Shammai da Yada.’Ya’yan Shammai maza su ne, Nadab da Abishur.
ויהיו בני אונם שמי וידע ובני שמי נדב ואבישור
29 Sunan matar Abishur ita ce Abihayil, wadda ta haifa masa Aban da Molid.
ושם אשת אבישור אביהיל ותלד לו את אחבן ואת מוליד
30 ’Ya’yan Nadab maza su ne, Seled da Affayim. Seled ya mutu babu yara.
ובני נדב סלד ואפים וימת סלד לא בנים
31 Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan. Sheshan shi ne mahaifin Alai.
ובני אפים ישעי ובני ישעי ששן ובני ששן אחלי
32 ’Ya’yan Yada maza, ɗan’uwan Shammai su ne, Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu babu yara.
ובני ידע אחי שמי יתר ויונתן וימת יתר לא בנים
33 ’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel.
ובני יונתן פלת וזזא אלה היו בני ירחמאל
34 Sheshan ba shi da’ya’ya maza, sai’ya’ya mata kawai. Yana da bawa mutumin Masar mai suna Yarha.
ולא היה לששן בנים כי אם בנות ולששן עבד מצרי ושמו ירחע
35 Sheshan ya ba da’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai.
ויתן ששן את בתו לירחע עבדו לאשה ותלד לו את עתי
36 Attai shi ne mahaifin Natan, Natan shi ne mahaifin Zabad,
ועתי הליד את נתן ונתן הוליד את זבד
37 Zabad shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne mahaifin Obed,
וזבד הוליד את אפלל ואפלל הוליד את עובד
38 Obed shi ne mahaifin Yehu, Yehu shi ne mahaifin Azariya,
ועובד הוליד את יהוא ויהוא הליד את עזריה
39 Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa,
ועזריה הליד את חלץ וחלץ הליד את אלעשה
40 Eleyasa shi ne mahaifin Sismai, Sismai shi ne mahaifin Shallum
ואלעשה הליד את ססמי וססמי הליד את שלום
41 Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma shi ne mahaifin Elishama.
ושלום הוליד את יקמיה ויקמיה הליד את אלישמע
42 ’Ya’yan Kaleb maza, ɗan’uwan Yerameyel su ne, Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif, da ɗansa Maresha, wanda shi ne mahaifin Hebron.
ובני כלב אחי ירחמאל מישע בכרו הוא אבי זיף ובני מרשה אבי חברון
43 ’Ya’yan Hebron maza su ne, Kora, Taffuwa, Rekem da Shema.
ובני חברון--קרח ותפח ורקם ושמע
44 Shema shi ne mahaifin Raham, Raham kuma shi ne mahaifin Yorkeyam. Rekem shi ne mahaifin Shammai.
ושמע הוליד את רחם אבי ירקעם ורקם הוליד את שמי
45 Ɗan Shammai shi ne Mawon, Mawon kuma shi ne mahaifin Bet-Zur.
ובן שמי מעון ומעון אבי בית צור
46 Efa ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Haran, Moza da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez.
ועיפה פילגש כלב ילדה את חרן ואת מוצא ואת גזז וחרן הליד את גזז
47 ’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af.
ובני יהדי--רגם ויותם וגישן ופלט ועיפה ושעף
48 Ma’aka ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Sheber da Tirhana.
פילגש כלב מעכה ילד שבר ואת תרחנה
49 Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna da kuma Shewa, mahaifin Makbena da Gibeya.’Yar Kaleb ita ce Aksa.
ותלד שעף אבי מדמנה את שוא אבי מכבנה ואבי גבעא ובת כלב עכסה
50 Waɗannan su ne zuriyar Kaleb.’Ya’yan Hur maza, ɗan farin Efrata su ne, Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim,
אלה היו בני כלב בן חור בכור אפרתה--שובל אבי קרית יערים
51 Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader.
שלמא אבי בית לחם חרף אבי בית גדר
52 Zuriyar Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim su ne, Harowe, rabin Manahatiyawa,
ויהיו בנים לשובל אבי קרית יערים הראה חצי המנחות
53 kuma gidan Kiriyat Yeyarim su ne, Itrayawa, Futiyawa, Shumatiyawa da Mishratiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.
ומשפחות קרית יערים--היתרי והפותי והשמתי והמשרעי מאלה יצאו הצרעתי--והאשתאלי
54 Zuriyar Salma su ne, Betlehem, Netofawa, Atrot Bet Yowab, rabin Manahatiyawa, Zoriyawa,
בני שלמא בית לחם ונטופתי עטרות בית יואב וחצי המנחתי הצרעי
55 kuma gidan marubuta waɗanda suke zama a Yabez su ne, Tiratiyawa, Shimeyatiyawa da Sukatiyawa. Waɗannan su ne Keniyawa waɗanda suka zo daga Hammat, mahaifin gidan Rekab.
ומשפחות ספרים ישבו (ישבי) יעבץ תרעתים שמעתים שוכתים המה הקינים הבאים מחמת אבי בית רכב

< 1 Tarihi 2 >