< 1 Tarihi 19 >

1 Ana nan, sai Nahash sarkin Ammonawa ya mutu, sai ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
[達味戰勝聯軍]此後,阿孟子民的君王納哈士死了,他的兒子繼位為王。
2 Dawuda ya yi tunani, “Zan nuna jinƙai ga Hanun ɗan Nahash, domin mahaifinsa ya nuna alheri gare ni.” Saboda haka Dawuda ya aika da tawaga don yă yi wa Hanun ta’aziyya game da mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka iso wurin Hanun a ƙasar Ammonawa don su ta’azantar da shi,
達味心想:我要善待納哈士的兒子哈農,因為他父親曾善待了我。於是達味派遣使者去慰問他,哀悼他的父親。但當達味的臣僕來到阿孟子民的境內哈農那裏慰問他時,
3 sai manyan Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aika mutanen nan wurinka su ta’azantar da kai? Ba mutanensa sun zo ne su bincika su kuma leƙi ƙasar su tumɓuke ta ba?”
阿孟子民的公卿對哈農說:「達味派人來慰問你,你以為他是尊敬你的父親嗎﹖他的臣僕到你這裏來,安知不是為調查、探聽、破壞這地方﹖」
4 Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda, ya yi musu aski, ya yayyanka rigunansu a daidai ɗuwawunsu, sa’an nan ya sallame su.
哈農遂拿住達味的臣僕,將他們的鬍鬚剃去,將他們下半截至臀部的衣服也都割去,然後放他們走了。
5 Da wani ya zo ya faɗa wa Dawuda game da mutanen, sai ya aiki’yan aika su sadu da su, gama an ƙasƙantar da su ainun. Sarki ya ce, “Ku zauna a Yeriko har sai gemunku sun yi girma, sa’an nan ku dawo.”
他們走了以後,有人將這些人所遭遇的事告訴了達味,達味遂即派人前去迎接他們;因為這些人很覺羞恥,王便吩咐說:「你們暫且留在耶里哥,等鬍鬚長起後再回來。」
6 Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba.
阿孟子民見自己同達味結下了仇恨,哈農和阿孟子民便派人用一千「塔冷通」銀子,向二河之間的阿蘭,瑪阿加的阿蘭及祚巴去僱戰車和騎兵。
7 Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi.
他們僱得了戰車三萬二千輛,又僱得了瑪阿加王和他的軍隊。他們來到,就在默德巴前紮營;阿孟子民也從自己的城內出來,集合備戰。
8 Da jin haka, Dawuda ya aiki Yowab tare da dukan mayaƙa masu yaƙi.
達味一聽說,遂派約阿布率領全部精兵出擊。
9 Ammonawa suka fito suka ja dāgā a ƙofar birninsu, yayinda sarakunan da suka zo, su kansu suka ware suna a fili.
阿孟子民出來,在城門前擺了陣,來助戰的王子們另在田間擺了陣。
10 Yowab ya ga cewa akwai dāgā a gabansa da bayansa; sai ya zaɓi waɗansu mayaƙa mafi kyau a Isra’ila ya sa su a kan Arameyawa.
約阿布見前後受敵,便由以色列勁旅中,挑選一隊精兵擺陣進攻阿蘭人;
11 Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin kulawar Abishai ɗan’uwansa, aka sa a kan Ammonawa.
將期餘的軍隊,交由自己的兄弟阿彼瑟指揮,叫他列陣進攻阿孟子民,
12 Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ni ƙarfi, sai ka kawo mini ɗauke da ni; amma in Ammonawa sun fi ka ƙarfi, sai in kawo maka ɗauke.
對他說:「若我打不下阿蘭人,你就來援助我;若你打不下阿孟子民,我就來援助你。
13 Ka yi ƙarfin hali bari mu yi yaƙi da jaruntaka saboda mutanenmu da biranen Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da ya ga ya yi masa kyau.”
你當勇敢! 為了我們的民族,為了我們天主的城,我們應當奮鬥。願上主成就他認為美好的事! 」
14 Sai Yowab da ƙungiyoyin mayaƙan da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Arameyawa, Arameyawan kuwa suka gudu a gabansa.
然後,約阿布帶著軍隊往前進攻阿蘭人,阿蘭人便在他面前逃走了。
15 Sa’ad da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka guda a gaban ɗan’uwansa Abishai suka shiga cikin birni. Sai Yowab ya koma Urushalima.
阿孟子民見阿蘭人逃走,他們也在約阿布的兄弟阿彼瑟面前逃走,退入城中;以後,約阿布回了耶路撒冷。
16 Bayan Arameyawa suka ga cewa Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka aiki’yan aika suka sa aka kawo Arameyawan da suke hayen Kogi waɗanda Shobak shugaban mayaƙan Hadadezer yake shugabanta.
阿蘭人見自己為以色列打敗,遂派使者將大河那邊的阿蘭人調來,由哈達德則爾的元帥芍法客率領。
17 Sa’ad da aka faɗa wa Dawuda wannan, sai tattara dukan Isra’ila ya haye Urdun; ya tafi wurinsu ya kuwa ja dāgā ɗaura da su. Dawuda ya ja dāgārsa don yă sadu da Arameyawa a yaƙi, su kuwa suka yi yaƙi da shi.
達味一得了情報,就調集所有的以色列人,渡過約但河,來到赫藍,擺陣向他們進攻。當達味擺陣攻擊阿蘭人時,阿蘭人就來迎戰。
18 Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, mutanen Dawuda kuwa suka kashe masu hawan keken yaƙinsu dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya kuma kashe Shobak shugaban mayaƙansu.
但阿蘭人在以色列面前潰退,達味乘勝擊殺了阿蘭七千騎兵,四萬步兵,也殺了他們的元帥芍法客。
19 Da abokan tarayyar Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka nemi salama da Dawuda suka kuma zama bayinsa. Saboda haka Arameyawa ba su ƙara yarda su taimaki Ammonawa ba.
哈達德則爾的臣僕見他們敗於以色列,便與達味講和,表示臣服。從此阿蘭人再不敢協助阿孟子民了。

< 1 Tarihi 19 >