< 1 Tarihi 18 >
1 Ana nan sai Dawuda ya ci Filistiyawa ya kuma rinjaye su, ya ƙwace Gat da ƙauyukan kewayenta daga mulkin Filistiyawa.
2 Dawuda ya kuma ci Mowabawa, suka zama bayinsa suka kuma biya haraji.
3 Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer sarkin Zoba, har can Hamat, sa’ad da ya je don yă kafa mulkinsa a wajen Kogin Yuferites.
4 Dawuda ya kame keken yaƙinsa dubu ɗaya, da mahayan kekunan yaƙi dubu bakwai da sojojin kafa guda dubu ashirin. Ya yayyanke dukan agaran dawakansa, amma ya bar dawakai da suka isa jan kekunan yaƙi ɗari.
5 Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu.
6 Ya sa ƙungiyoyin sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus. Arameyawan kuwa suka zama bayinsa, suka kuma kawo haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.
7 Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariyan da shugabannin sojojin Hadadezer suke riƙe, ya kawo su Urushalima.
8 Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam.
9 Sa’ad da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci mayaƙan Hadadezer sarkin Zoba gaba ɗaya,
10 sai ya aiki ɗansa Hadoram zuwa wurin Sarki Dawuda yă gaishe shi yă kuma yi masa barka da nasara a yaƙi a kan Hadadezer, wanda yake yaƙi da Towu. Hadoram ya kawo kowane irin kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla.
11 Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek.
12 Abishai ɗan Zeruhiya ya bugi mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.
13 Ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.
14 Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa.
15 Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci;
16 Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci; Shafsha shi ne magatakarda;
17 Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa;’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki.