< 1 Tarihi 17 >
1 Bayan Dawuda ya zauna a fadansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti.”
2 Natan ya amsa wa Dawuda ya ce, “Duk abin da kake tunani a zuciya, ka yi, gama Allah yana tare da kai.”
3 A daren nan maganar Allah ta zo wa Natan cewa,
4 “Ka tafi ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ba kai ba ne za ka gida mini gidan da zan zauna a ciki.
5 Ban taɓa zama a gida daga ranar da na fito da Isra’ila daga Masar ba har wa yau. Na yi ta yawo daga gefen da aka kafa tenti zuwa wani, daga wannan wuri zuwa wancan.
6 Duk inda na tafi tare da Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani daga cikin shugabanninsu waɗanda na umarta su yi kiwon mutanena, “Don me ba ku gida mini gidan al’ul ba?”’
7 “Yanzu, ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauke ka daga makiyaya da kuma daga bin garke, don ka zama mai mulki a bisa mutanena Isra’ila.
8 Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya.
9 Zan kuma tanada wuri domin mutanena Isra’ila, zan kuma kafa su saboda za su kasance da gidan kansu ba kuwa za a ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zaluntar su ba, yadda suka yi da farko
10 da kuma suka yi tun lokacin da na sa shugabanni a bisa mutanen Isra’ila. Zan rinjaye dukan abokan gābanka. “‘Na furta maka cewa Ubangiji zai gina maka gida,
11 sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka.
12 Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada.
13 Zan zama Ubansa, zai kuma zama ɗana. Ba zan taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi, kamar yadda na ɗauke ta daga wanda ya riga ka ba.
14 Zan sa shi a bisa gidana da mulkina har abada; kujerar sarautarsa za tă kahu har abada.’”
15 Natan ya faɗa wa Dawuda dukan kalmomin wahayin nan.
16 Sai Sarki Dawuda ya shiga ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, kuma wane ne iyalina, da ka kawo ni har zuwa nan?
17 Kuma sai ka ce wannan bai isa ba a idonka, ya Allah, ka yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Ka dube ni sai ka ce ni ne mafi ɗaukaka cikin mutane, ya Ubangiji Allah.
18 “Me kuma Dawuda zai ce maka saboda girmamawar da ka yi wa bawanka? Gama ka san bawanka,
19 Ya Ubangiji. Gama saboda bawanka da kuma bisa ga nufinka, ka yi wannan babban abu, ka kuma sanar da dukan manyan alkawura.
20 “Babu wani kamar ka, ya Ubangiji, babu kuma Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.
21 Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar?
22 Ka mai da mutanenka Isra’ila na kanka har abada, kuma kai, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.
23 “Yanzu kuwa, Ubangiji, bari alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa yă kahu har abada. Yi kamar yadda ka yi alkawari,
24 saboda zai kahu kuma sunanka zai zama mai girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘Ubangiji Maɗaukaki, Allah a bisa Isra’ila, Allahn Isra’ila ne!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka.
25 “Kai, Allahna, ka bayyana ga bawanka cewa za ka gina gida dominsa. Ta haka bawanka ya sami ƙarfin gwiwa ya yi addu’a gare ka.
26 Ya Ubangiji, kai ne Allah! Ka yi alkawari abubuwa masu kyau wa bawanka.
27 Yanzu ka ji daɗi don ka albarkace gidan bawanka, don yă ci gaba har abada a gabanka; gama kai, ya Ubangiji, ka albarkace shi, ya kuma sami albarka ke nan har abada.”