< 1 Tarihi 16 >
1 Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah.
2 Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji.
3 Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace.
4 Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.
5 Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna,
6 Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.
7 A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.
8 Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.
9 Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.
10 Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.
11 Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.
12 Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke,
13 Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.
14 Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya.
15 Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,
16 alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku.
17 Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari.
18 “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.”
19 Sa’ad da suke kima, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,
20 suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga wannan mulki zuwa wancan.
21 Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna.
22 “Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.”
23 Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana.
24 Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.
25 Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.
26 Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai.
27 Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.
28 Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,
29 ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.
30 Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba.
31 Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “Ubangiji yana mulki!”
32 Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri; bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!
33 Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya.
34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce.
35 Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”
36 Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”
37 Dawuda ya bar Asaf da’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.
38 Ya kuma bar Obed-Edom da’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi.
39 Dawuda ya bar Zadok firist da’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon
40 don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila.
41 Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
42 Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki.’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.
43 Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka.