< 1 Tarihi 15 >
1 Bayan Dawuda ya yi gine-gine wa kansa a Birnin Dawuda, sai ya shirya wuri domin akwatin alkawarin Allah, ya kuma kafa tenti dominsa.
2 Sa’an nan Dawuda ya ce, “Babu wani sai ko Lawiyawa kaɗai za su ɗauka akwatin alkawarin Allah, gama Ubangiji ya zaɓe su su ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji su kuma yi hidima a gabansa har abada.”
3 Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa.
4 Ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya da kuma Lawiyawa.
5 Daga zuriyar Kohat, Uriyel shugaba da dangi 120;
6 daga zuriyar Merari Asahiya shugaba da dangi 220;
7 daga zuriyar Gershom, Yowel shugaba da dangi 130;
8 daga zuriyar Elizafan, Shemahiya shugaba da dangi 200;
9 daga zuriyar Hebron, Eliyel shugaba da dangi 80;
10 daga zuriyar Uzziyel, Amminadab shugaba da dangi 112.
11 Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa.
12 Ya ce musu, “Ku ne kawunan iyalan Lawiyawa; ku da’yan’uwanku Lawiyawa, sai ku tsarkake kanku ku hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila, zuwa wurin da na shirya dominsa.
13 Domin ku, Lawiyawa ba ku haura da shi da farko ba ne ya sa Ubangiji Allahnmu ya husata a kanmu. Ba mu tambaye shi game da yadda za mu yi shi a hanyar da aka ƙayyade ba.”
14 Saboda haka firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu don su hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila.
15 Sai Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah da sanduna a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.
16 Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna.
17 Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berekiya daga cikin’yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kushahiya.
18 Tare da su kuma’yan’uwansa da suke biye bisa ga matsayi. Wato, Zakariya, Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ben, Ma’asehiya, Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom da Yehiyel, matsaran ƙofofi.
19 Mawaƙan nan Heman, Asaf da Etan, ne za su buga kugen tagulla.
20 Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot.
21 Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom, Yehiyel da Azaziya, ne za su ja garayu masu murya ƙasa-ƙasa bisa ga sheminit.
22 Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni.
23 Berekiya da Elkana, ne za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.
24 Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.
25 Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-Edom, da farin ciki.
26 Domin Allah ya taimaki Lawiyawan da suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, aka miƙa hadayar bijimai bakwai da raguna bakwai.
27 To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin.
28 Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.
29 Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta.