< 1 Tarihi 14 >

1 To, fa, Hiram sarkin Taya ya aika da’yan aika zuwa wurin Dawuda, tare da gumaguman al’ul, maginan duwatsu da kafintoci, don su gina wa Dawuda fada.
泰爾王希蘭將香柏木運到大衛那裏,又差遣使者和石匠、木匠給大衛建造宮殿。
2 Dawuda kuwa ya san cewa Ubangiji ya kafa shi a matsayin sarki a bisa Isra’ila kuma cewa an ɗaukaka mulkinsa saboda mutanensa Isra’ila.
大衛就知道耶和華堅立他作以色列王,又為自己的民以色列,使他的國興旺。
3 A Urushalima, Dawuda ya ƙara auren waɗansu mata, ya kuma zama mahaifin ƙarin’ya’yan maza da mata.
大衛在耶路撒冷又立后妃,又生兒女。
4 Ga sunayen yaran da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,
在耶路撒冷所生的眾子是沙母亞、朔罷、拿單、所羅門、
5 Ibhar, Elishuwa, Elfelet,
益轄、以利書亞、以法列、
6 Noga, Nefeg, Yafiya,
挪迦、尼斐、雅非亞、
7 Elishama, Beyeliyada da Elifelet.
以利沙瑪、比利雅大、以利法列。
8 Sa’ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila, sai suka haura da cikakken mayaƙa don su neme shi, amma Dawuda ya ji game da wannan ya kuwa fita don yă ƙara da su.
非利士人聽見大衛受膏作以色列眾人的王,非利士眾人就上來尋索大衛。大衛聽見,就出去迎敵。
9 To, fa, Filistiyawa suka zo suka kai wa Kwarin Refayim hari;
非利士人來了,布散在利乏音谷。
10 sai Dawuda ya roƙi Allah ya ce, “In tafi in yaƙi Filistiyawa? Za ka ba da su gare ni?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ka tafi, zan ba da su gare ka.”
大衛求問上帝,說:「我可以上去攻打非利士人嗎?你將他們交在我手裏嗎?」耶和華說:「你可以上去,我必將他們交在你手裏。」
11 Saboda haka Dawuda da mutanensa suka haura zuwa Ba’al-Ferazim, a can kuwa suka ci Filistiyawa da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa kan raraki ƙasa, haka Allah ya raraki abokan gābana ta wurin hannuna.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim.
非利士人來到巴力‧毗拉心,大衛在那裏殺敗他們。大衛說:「上帝藉我的手沖破敵人,如同水沖去一般」;因此稱那地方為巴力‧毗拉心。
12 Filistiyawa suka yashe allolinsu, Dawuda kuma ya ba da umarnai a ƙone su a wuta.
非利士人將神像撇在那裏,大衛吩咐人用火焚燒了。
13 Filistiyawa suka sāke kai hari wa kwarin;
非利士人又布散在利乏音谷。
14 sai Dawuda ya sāke roƙi Allah, Allah kuwa ya amsa masa, “Kada ka tafi kai tsaye, amma ka yi zobe kewaye da su, ka kuma fāɗa musu a gaban itatuwan tsamiya.
大衛又求問上帝。上帝說:「不要一直地上去,要轉到他們後頭,從桑林對面攻打他們。
15 Da zarar ka ji motsin takawa a sama itatuwan tsamiya, ka fita don yaƙi, domin wannan zai nuna cewa Allah ya fita a gabanka don yă bugi mayaƙan Filistiyawa.”
你聽見桑樹梢上有腳步的聲音,就要出戰,因為上帝已經在你前頭去攻打非利士人的軍隊。」
16 Saboda haka Dawuda ya yi kamar yadda Allah ya umarce shi, suka kuma bugi mayaƙan Filistiyawa, tun daga Gibeyon har zuwa Gezer.
大衛就遵着上帝所吩咐的,攻打非利士人的軍隊,從基遍直到基色。
17 Sai sunan Dawuda ya bazu ko’ina a ƙasar, Ubangiji kuwa ya sa dukan al’ummai suka ji tsoronsa.
於是大衛的名傳揚到列國,耶和華使列國都懼怕他。

< 1 Tarihi 14 >