< 1 Tarihi 12 >

1 Waɗannan su ne mutanen da suka zo wurin Dawuda a Ziklag, yayinda aka kore shi daga gaban Shawulu ɗan Kish (suna cikin jarumawan da suka taimake shi a yaƙi;
[投奔達味的戰士]當達味尚在逃避克士的兒子撒烏耳時,這些人就來到戚刻拉格,投奔達味。他們都是些勇士,善於作戰,
2 suna da baka suna kuma iya harba kibiya, ko majajjawa da hannun dama ko na hagu; su’yan’uwan Shawulu ne daga kabilar Benyamin):
能左右開弓,發石射傷的人,是本雅明人,為撒烏耳的同族兄弟;
3 Ahiyezer babbansu da Yowash’ya’yan Shema’a maza daga Gibeya; Yeziyel da Felet’ya’yan Azmawet; Beraka, Yehu daga Anatot,
為首的是阿希厄則耳,其次為基貝亞人舍瑪亞的兒子約阿士,阿次瑪委特的兒子耶齊耳和培肋特,貝辣加和阿納托特人耶胡,
4 da Ishmahiya daga Gibeyon, wani jarumi a cikin Talatin nan, wanda shi ne shugaban Talatin; Irmiya, Yahaziyel, Yohanan, Yozabad daga Gedera,
基貝紅人依市瑪雅,他在三十勇士之中,且是三十勇士的首領; 還有耶勒米雅,雅哈齊耳,約哈南和革德爾人的約匝巴得,
5 Eluzai, Yerimot, Beyaliya, Shemariya da Shefatiya daga Haruf;
厄路齋,耶黎摩特,貝阿里雅,舍瑪黎雅和哈黎夫人舍法提雅,
6 Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezer da Yashobeyam daga Kora;
厄耳卡納,依史雅,阿匝勒耳,約厄則爾和瑪芍貝罕,科辣黑人,
7 da Yoyela da Zebadiya’ya’yan Yeroham maza daga Gedor.
又有革多爾人耶洛罕的兒子約厄拉和則巴狄雅。
8 Sai waɗansu mutanen Gad suka koma suna goyon bayan Dawuda suka kuma haɗa kai da shi a kagararsa a hamada. Su ƙwararrun mayaƙa ne, a shirye don yaƙi, kuma suna iya riƙe garkuwa da māshi. Fuskokinsu kamar fuskoki zakoki, kuma suna da sauri kamar bareyi a kan duwatsu.
有些加得人到曠野的山岩中歸順了達味;他們是孔武有力,精於作戰,能使藤牌槍矛的勇士,面貌相似獅子,敏捷有如山上的羚羊:
9 Ezer shi ne babba, Obadiya shi ne mai binsa a shugabanci, Eliyab na uku,
首為厄則爾,次為敖巴狄雅,三為厄里雅布,
10 Mismanna na huɗu, Irmiya na biyar,
四為米舍曼納,五為耶勒米雅,
11 Attai na shida, Eliyel na bakwai,
六為阿泰,七為厄里耳,
12 Yohanan na takwas, Elzabad na tara,
八為約哈南,九為厄耳匝巴得,
13 Irmiya na goma da kuma Makbannai na goma sha ɗaya.
十為耶勒米雅烏,十一為瑪革邦乃:
14 Waɗannan mutanen Gad shugabannin mayaƙa ne; ƙarami a cikinsu zai iya ƙara da mutum ɗari, kuma babba a cikin zai iya ƙara da dubu.
這些人都是加得的子孫,軍隊的首領,小者可抵百人,大者可抵千人。
15 Su ne suka haye Urdun a wata na farko sa’ad da kogin ya yi ambaliya, suka kuma kori duk mai rai a kwarin, na wajen gabas da na wajen yamma.
就是這些人,在一月裏,約但何水漲到兩岸時,渡過了河,使平原所有的居民東奔西逃。
16 Sauran mutanen Benyamin da waɗansu mutanen Yahuda su ma suka zo wurin Dawuda a kagararsa.
此外,又有本雅明人和猶大人來到山砦見達味,
17 Sai Dawuda ya fita don yă tarye su, ya kuma ce musu, “In kun zo wurina da salama, don ku taimake ni, to, ina a shirye in bar ku ku haɗa kai tare da ni. Amma in kun zo don ku bashe ni ga abokan gābana sa’ad da hannuwana ba su da laifi a rikici, bari Allah na kakanninmu yă duba yă kuma shari’anta ku.”
達味出來迎接他們說:「如果你們帶來平安,有意協助我,我的心就與你們相契合;如果你們來是為將我這無辜的人出賣於敵人,願我們祖先的天主,予以鑑察,予以審判。」
18 Sai Ruhu ya sauko a kan Amasai, shugaban Talatin nan, sai ya ce, “Mu naka ne, ya Dawuda! Muna tare da kai, ya ɗan Yesse! Nasara, nasara gare ka, nasara kuma ga waɗanda suke taimakonka. Gama Allahnka zai taimake ka.” Saboda haka Dawuda ya karɓe su ya kuma mai da su shugabannin ƙungiyoyin maharansa.
當時,天主的神充滿在那三十個勇士的首領阿瑪賽身上,他遂說:「達味! 我們屬於你;葉瑟的兒子! 我們來協助你;平安! 願協助你的也都平安! 因為你的天主扶助了你。」達味便收留了他們,委他們為部隊隊長。
19 Waɗansu mutanen Manasse suka haɗa kai da Dawuda sa’ad da ya tafi tare da Filistiyawa don yă yaƙi Shawulu (Shi da mutanensa ba su taimaki Filistiyawa ba domin bayan shawarwari, shugabanninsu suka salame shi. Sun ce, “Za mu biya da kawunanmu in ya koma ga maigidansa Shawulu.”)
當達味與培肋舍特人一同去攻打撒烏耳時,也有些默納協人歸順了達味。其實達味並沒有協助培勒舍特人,因為培肋舍特人的首領議決將他遣回,說:「怕達味拿我們的頭去向他的主人撒烏耳投誠。」
20 Da Dawuda ya tafi Ziklag, waɗannan mutanen Manasse ne suka haɗa kai da shi. Adna, Yozabad, Yediyayel, Mika’ilu, Yozabad, Elihu da Zilletai, shugabannin ƙungiyoyi na dubu a cikin Manasse.
達味回漆刻拉格時,默納協人阿德納,約匝巴得,耶狄厄耳,米加耳,約匝巴得,厄里胡和漆肋泰,都歸順了他;他們都是默納協人中的千夫長。
21 Suka taimaki Dawuda a kan ƙungiyoyin hari, gama dukansu jarumawa ne sosai, kuma su shugabanni ne a cikin mayaƙansa.
這些人偕同達味攻擊了一群賊寇;他們皆是孔武有力的勇士,成了軍中的官長。
22 Kowace rana mutane suka riƙa zuwa don su taimaki Dawuda, sai da ya kasance da runduna mai girma, kamar mayaƙan Allah.
前來協助達味的人日漸增多,以致成了一強大的兵團,有如天主的軍旅。[擁護達味為王的戰士]
23 Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa.
來到赫貝龍達味前,欲把撒烏耳的王位,依照上主的命令,交於達味,而準備出征的人數如下:
24 Mutanen Yahuda, masu riƙe garkuwa da māshi, su 6,800 shiryayyu don yaƙi;
猶大子孫中,執盾持槍的武裝戰士六千八百人;
25 mutanen Simeyon, jarumawa shiryayyu don yaƙi, su 7,100;
西默盎子孫中,英勇有力的戰士七千一百人;
26 mutanen Lawi, su 4,600,
肋未子孫中,四千六百人;
27 haɗe da Yehohiyada, shugaban iyalin Haruna tare da mutane 3,700,
亞郎家族的族長約雅達,與他的侍從三千七百人,
28 da Zadok, matashi jarumi sosai, tare da shugabanni su 22 daga iyalinsa;
少年勇士匝多克和他的家人二十二個軍官;
29 mutanen Benyamin,’yan’uwan Shawulu, su 3,000, yawanci waɗanda suke biyayya ga gidan Shawulu sai lokacin;
撒烏耳的同族本雅明子孫中三千人。直到那時止,他們多半支持撒烏耳家;
30 mutanen Efraim, jarumawa, sanannu cikin gidajensu, su 20 800;
厄弗辣因子孫中,二萬零八百人,都是有力的勇士,在自己家族中也是有名望的人;
31 mutanen rabin kabilar Manasse, sanannu da sunaye suka zo suka mai da Dawuda sarki, su 18,000;
默納協半支派中,報名來立達味為王者一萬八千人;
32 mutanen Issakar, masu fahimtar lokuta suka kuma san abin da ya kamata Isra’ila ya yi, manya 200, tare da danginsu a ƙarƙashin shugabancinsu;
依撒加爾子孫中,識時務,指導以色列應如何行事的人,有族長二百人,同族的人都聽他們的指揮;
33 mutanen Zebulun, ƙwararru sojoji shiryayyu don yaƙi da kowane irin makami, suka zo don su taimaki Dawuda da zuciya ɗaya, su 50,000;
則步隆子孫中,能上陣作戰,會用各種武器,一心一意助戰的,有五萬人;
34 mutanen Naftali su 1,000 shugabanni, tare da mutane 37,000 masu riƙe garkuwa da masu;
納裴塔里子孫中,能上陣作戰的,有二萬八千六百人;
35 mutanen Dan, shiryayyu don yaƙi, su 28,600;
丹子孫中,能上陣作戰的,有二萬八千六百人;
36 mutanen Asher, ƙwararrun sojoji shiryayyu don yaƙi, su 40,000;
阿協爾子孫中,能上陣作戰的,有四萬人;
37 kuma daga gabashin Urdun, mutanen Ruben, Gad da kuma rabin kabilar Manasse, masu kayan yaƙi iri-iri, su 120,000.
約但河東岸,勒烏本族,加得族,默納協半支派中,能持各種兵器作戰的,共有十二萬人:
38 Dukan waɗannan mayaƙa ne waɗanda suka ba da kansu da yardar rai su yi hidima. Suka zo Hebron da cikakken niyya don su naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila. Duka sauran Isra’ilawa su ma suka goyi baya a naɗa Dawuda sarki.
以上這些人都是軍人,有行伍訓練的戰士,誠心來到赫貝龍,要立達味為全以色列的君王;其餘的眾以色列人,也都一心要立達味為王。
39 Mutanen suka yi kwana uku a can tare da Dawuda, suna ci suna sha, gama iyalansu sun yi musu tanadi.
他們在那裏與達味同住了三天,一同飲食,因為有他們的弟兄為他們預備好了一切。
40 Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.
附近的人,以及遠至依撒加爾,則步隆和納斐塔里的人,都用驢、駱駝、騾和牛,給他們載來大批食品:麵餅、無花果餅、葡萄乾餅、由和牛羊,因為當時在以色列充滿了快樂。

< 1 Tarihi 12 >