< 1 Tarihi 11 >
1 Dukan Isra’ila fa suka taru wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu jiki da jininka ne.
2 A dā, ko a lokacin da Shawulu yake sarki, ai, kai ne kake shugabantar Isra’ila a yaƙe-yaƙe. Kuma Ubangiji Allahnka ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayin mutanena Isra’ila, za ka kuma zama mai mulkinsu.’”
3 Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, suka yi yarjejjeniya da shi a gaban Ubangiji, suka kuwa shafe Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila, yadda Ubangiji ya yi alkawari ta wurin Sama’ila.
4 Dawuda tare da dukan Isra’ilawa suka taka zuwa Urushalima (wato, Yebus). Yebusiyawan da suke zama a wurin
5 suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka, Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, Birnin Dawuda.
6 Dawuda ya ce, “Duk wanda ya jagoranci yaƙi a kan Yebusiyawa zai zama babban shugaban mayaƙa.” Yowab ɗan Zeruhiya ya fara haurawa, ta haka ya zama shugaba.
7 Dawuda zauna a kagarar, ta haka aka kira ta Birnin Dawuda.
8 Sai ya gina birni kewaye da shi, daga madogaran gini zuwa katangar da take kewaye, yayinda Yowab ya maido da sauran birnin.
9 Dawuda kuwa ya ƙara ƙarfi, domin Ubangiji Maɗaukaki yana tare da shi.
10 Waɗannan su ne manyan jarumawan Dawuda, su ne, tare da dukan Isra’ila, suka ba wa mulkinsa goyon baya mai ƙarfi da ya kai bisa dukan ƙasar, yadda Ubangiji ya yi alkawari.
11 Ga jerin sunayen jarumawan Dawuda. Yashobeyam wani ɗan Hakmoni, shi ne babban shugaba; ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe a ƙarawa guda kawai.
12 Biye da shi, shi ne Eleyazar ɗan Dodo mutumin Aho, ɗaya daga cikin jarumawa uku.
13 Yana tare da Dawuda a Fas Dammim sa’ad da Filistiyawa suka taru can don yaƙi. A wani wuri inda akwai gona cike da sha’ir, sojoji suka gudu daga Filistiyawa.
14 Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha’ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuma ya kawo babban nasara.
15 Wata rana uku cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara wurin Dawuda zuwa dutse a kogon Adullam, yayinda ƙungiyar Filistiyawa suke sansani a Kwarin Refayim.
16 A lokacin Dawuda yana cikin mafaka, sojojin Filistiyawa kuma suna a Betlehem.
17 Dawuda ya ji marmarin ruwan sha sai ya ce, “Kash, a ce wani zai sami mini ruwan sha daga rijiya kusa da ƙofar Betlehem mana!”
18 Sai Ukun suka kutsa kai cikin sansanin Filistiyawa, suka ja ruwa daga rijiyar da take kusa da ƙofar Betlehem suka ɗauko shi suka kawo wa Dawuda. Amma ya ƙi yă sha; a maimako, sai ya zubar da shi a gaban Ubangiji.
19 Ya ce, “Allah yă sawwaƙe in yi haka, ya kamata in sha jinin waɗannan mutanen da suka yi kasai da rayukansu?” Domin sun yi kasai da rayukansu don su dawo da shi, Dawuda bai sha shi ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.
20 Abishai ɗan’uwan Yowab shi ma babba ne cikin Ukun nan. Ya ɗaga māshinsa a kan mutum ɗari uku, waɗanda ya kashe, ya kuma zama sananne kamar Ukun.
21 Aka ninka girmama shi bisa Ukun, sai ya zama shugaba, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.
22 Benahiya ɗan Yehohiyada shi ma wani barden yaƙi ne daga Kabzeyel, wanda ya yi manyan abubuwa. Ya bugi gwanayen Mowab biyu. Ya kuma gangara zuwa cikin rami a ranar da aka yi dusar ƙanƙara ya kashe zaki.
23 Ya kuma kashe wani mutumin Masar mai tsayi ƙafa bakwai da rabi. Ko da yake mutumin Masar yana da māshi kamar sandan masaƙa a hannunsa, Benahiya ya yaƙe shi da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannun mutumin Masar ya kuma kashe shi da māshin nan nasa.
24 Irin abubuwan da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma sananne ne kamar waɗannan jarumawa uku.
25 Aka ɗauka shi da bangirma fiye da Talatin nan, amma ba a haɗa shi cikin Ukun ba. Dawuda kuwa ya sa shi yă lura da masu tsaron lafiyarsa.
26 Jarumawan nan su ne, Asahel ɗan’uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem,
27 Shammot mutumin Haror, Helez mutumin Felon,
28 Ira ɗan Ikkesh daga Tekowa, Abiyezer daga Anatot,
29 Sibbekai mutumin Husha, Ilai mutumin Aho,
30 Maharai mutumin Netofa, Heled ɗan Ba’ana mutumin Netofa,
31 Ittai ɗan Ribai daga Gibeya a Benyamin, Benahiya mutumin Firaton,
32 Hurai daga kogunan Ga’ash, Abiyel mutumin Arba,
33 Azmawet mutumin Harum, Eliyaba mutumin Sha’albo,
34 ’ya’yan Hashem mutumin Gizon maza, Yonatan ɗan Shageye mutumin Harar,
35 Ahiyam ɗan Sakar mutumin Harar, Elifal ɗan Ur,
36 Hefer mutumin Mekerat, Ahiya mutumin Felon,
37 Hezro mutumin Karmel, Na’arai ɗan Ezbai,
38 Yowel ɗan’uwan Natan, Mibhar ɗan Hagiri,
39 Zelek mutumin Ammon Naharai Baroti, mai ɗaukar kayan yaƙin Yowab ɗan Zeruhiya,
40 Ira mutumin Itra, Gareb mutumin Itra,
41 Uriya mutumin Hitti Zabad ɗan Alai,
42 Adina ɗan Shiza mutumin Ruben, wanda shi ne babba na mutanen Ruben, kuma talatin suna tare da shi,
43 Hanan ɗan Ma’aka, Yoshafat mutumin Mit,
44 Uzziya mutumin Ashtarot, Shama da Yehiyel’ya’yan Hotam mutumin Arower maza,
45 Yediyayel ɗan Shimri, ɗan’uwansa Yoha mutumin Tiz,
46 Eliyel mutumin Ma’aha, Yeribai da Yoshawiya’ya’yan Elna’am maza, Itma mutumin Mowab,
47 Eliyel, Obed da Ya’asiyel mutumin Mezob.