< 1 Tarihi 10 >

1 To, fa, Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa; Isra’ilawa kuwa suka gudu a gabansu, da yawa kuma suka mutu a kan Dutsen Gilbowa.
And the Philistines have fought with Israel, and the men of Israel flee from the face of the Philistines, and fall wounded in Mount Gilboa,
2 Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da’ya’yansa maza, suka kuma kashe’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa.
and the Philistines pursue after Saul, and after his sons, and the Philistines strike Jonathan, and Abinadab, and Malchi-Shua, sons of Saul.
3 Yaƙin ya yi tsanani kewaye da Shawulu, kuma sa’ad da maharba suka rutsa shi, sai suka ji masa rauni.
And the battle [is] heavy on Saul, and those shooting with the bow find him, and he is wounded by those shooting,
4 Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa.
and Saul says to the bearer of his weapons, “Draw your sword and pierce me with it, lest these uncircumcised come and have abused me.” And the bearer of his weapons has not been willing, for he fears exceedingly, and Saul takes the sword, and falls on it;
5 Da mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya fāɗi a kan takobinsa ya mutu.
and the bearer of his weapons sees that Saul [is] dead, and falls, he also, on the sword, and dies;
6 Ta haka Shawulu da’ya’yansa maza uku suka mutu, dukan gidansa kuwa suka mutu tare.
and Saul dies, and his three sons, and all his house—they died together.
7 Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.
And all the men of Israel who [are] in the valley see that they have fled and that Saul and his sons have died, and they forsake their cities and flee, and the Philistines come and dwell in them.
8 Kashegari, da Filistiyawa suka zo don su tuttuɓe waɗanda suka mutu, sai suka sami Shawulu da’ya’yansa maza sun mutu a Dutsen Gilbowa.
And it comes to pass, on the next day, that the Philistines come to strip the wounded, and find Saul and his sons fallen in Mount Gilboa,
9 Suka tuttuɓe shi suka yanke kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka kuma aika’yan aika ko’ina a ƙasar Filistiyawa, a yi shela labarin a cikin gumakansu da kuma mutanensu.
and strip him, and carry away his head and his weapons, and send [them] into the land of the surrounding Philistines to proclaim tidings [to] their idols and the people;
10 Suka sa kayan yaƙinsa a haikalin allahnsu suka kuma rataye kansa a haikalin Dagon.
and they put his weapons in the house of their gods, and have fixed his skull in the house of Dagon.
11 Sa’ad da mazaunan Yabesh Gileyad suka ji dukan abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu,
And all Jabesh-Gilead hears of all that the Philistines have done to Saul,
12 sai dukan jarumawa suka tafi suka ɗauki jikunan Shawulu da na’ya’yansa maza suka kawo Yabesh. Sa’an nan suka binne ƙasusuwan a ƙarƙashin babban itace oak a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.
and all the men of valor rise and carry away the body of Saul, and the bodies of his sons, and bring them to Jabesh, and bury their bones under the oak in Jabesh, and fast seven days.
13 Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba,
And Saul dies because of his trespass that he trespassed against YHWH, against the word of YHWH that he did not keep, and also for asking to inquire of a familiar spirit;
14 bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse.
and he did not inquire of YHWH, and He puts him to death, and turns around the kingdom to David son of Jesse.

< 1 Tarihi 10 >