< 1 Jan 3 >
1 Gade ki grand amou Papa a te bay nou ke nou ta vin rele ti moun yo a Bondye! Konsa, se sa nou ye. Pou rezon sa lemonn pa rekonèt nou, paske li pa t rekonèt Li.
Dubi irin kaunar da Allah ya bamu, har da za a kira mu 'ya'yan Allah, haka muke kuwa. Saboda wannan dalili ne duniya bata san muba, saboda bata san shi ba.
2 Alò, chè zanmi yo, nou se ti moun a Bondye, epi li poko fin devwale ki sa n ap ye. Nou konnen ke lè Li parèt nou va tankou Li, paske nou va wè Li menm jan ke Li ye.
Kaunatattu, yanzu mu 'ya'yan Allahne, kuma ba a bayyana mana yadda zamu zama ba tukuna, mun sani sa'adda Almasihu zai bayyana, zamu zama kamarsa, domin zamu ganshi kamar yadda yake.
3 Epi tout moun ki gen espwa sa sou Li, vin pi li menm, menm jan ak Li.
Dukkan wanda yake da wannan bege game da gidan gobe ya kan tsarkake kansa, kamar yadda shima yake da tsarki.
4 Epi tout moun ki pratike peche, transgrese lalwa. Peche a se transgresyon lalwa.
Dukkan wanda yaci gaba da yin zunubi yana ketare shari'a kenan. Gama zunubi ketare shari'a ne.
5 Nou konnen ke Li te parèt pou Li ta kapab retire peche yo, epi nan Li pa gen peche.
Kun sani Almasihu ya bayyana domin ya dauke zunubai ne. Kuma a cikinsa babu zunubi.
6 Okenn moun ki rete nan Li pa peche, men okenn ki viv nan peche pa t wè Li, ni yo pa konnen Li.
Ba wanda zai kasance a cikinsa da zai cigaba da yin zunubi. Ba wanda zai ci gaba da aikata zunubi da zai ce ya sanshi, ko kuma ya ganshi.
7 Ti moun yo, pa kite pèsòn twonpe nou. Sila ki pratike ladwati a se jis, menm jan ke Li jis.
'Ya'yana kaunatattu, kada ku bari kowa ya baudar da ku, wanda yake aikata adalci shi adali ne, kamar yadda Almasihu yake adali.
8 Men sila ki pratike peche se a dyab la, paske dyab la te peche depi kòmansman a. Fis a Bondye te parèt pou rezon sila, ke Li ta kapab detwi zèv a dyab yo.
Wanda yake aikata zunubi na ibilis ne, gama ibilis yayi zunubi tun daga farko. Dalilin haka ne Dan Allah ya bayyana, domin ya rushe ayyukan ibilis.
9 Nanpwen pèsòn ki ne de Bondye ki pratike peche paske jèm Li tou rete nan li, epi li pa kapab peche, paske li ne a Bondye.
Duk wanda aka haife shi daga Allah ba ya yin zunubi, saboda irin Allah na cikinsa. Ba zaya iya ci gaba da yin zunubi ba domin an haife shi daga wurin Allah.
10 Selon sa pitit a Bondye yo, ak pitit a dyab yo se byen klè. Nenpòt ki pa pratike ladwati a pa de Bondye, ni sila ki pa renmen frè li.
Ta haka ne ake bambanta 'ya'yan Allah da 'ya'yan ibilis. Dukkan wanda baya aikata adalci ba na Allah bane; haka kuma wanda ba ya kaunar dan'uwansa.
11 Paske sa se mesaj la ke nou te tande depi kòmansman a ke nou dwe renmen yon lòt.
Domin wannan shine sakon da kuka ji tun daga farko: cewa mu kaunaci junanmu,
12 Pa kon Caïn, ki te apatyen a mechan a, epi te asasinen frè l. Men poukisa li te asasinen li? Paske zèv li te mal, epi sa yo a frè l te jis.
ba kamar Kayinu ba wanda yake na shaidan kuma ya kashe dan'uwansa. Me yasa ya kashe shi? Saboda ayyukansa miyagu ne, na dan'uwansa kuma masu adalci ne.
13 Pa etonnen, frè yo, si lemonn rayi nou.
Kada kuyi mamaki 'yan'uwana, idan duniya ta ki ku.
14 Nou konnen ke nou kite lanmò, epi antre nan lavi akoz ke nou renmen frè nou yo. Sila ki pa renmen, rete nan lanmò.
Mun sani mun ratsa mutuwa zuwa cikin rai, saboda muna kaunar 'yan'uwa. Dukkan wanda ba ya yin kauna, shi matacce ne.
15 Nenpòt ki rayi frè l se yon asasen. Epi nou konnen ke nanpwen asasen ki gen lavi etènèl a anndan li. (aiōnios )
Dukkan wanda yake kin dan'uwansa, mai kisan kai ne. Kun kuma sani babu rai na har abada a cikin mai kisankai. (aiōnios )
16 Men konsa nou rekonèt lamou; ke Li te bay vi Li pou nou. Epi konsa, nou ta dwe bay vi nou yo pou frè nou yo.
Ta wurin haka muka san kauna, da ya ke Almasihu ya bayar da ransa saboda mu. Mu ma ya kamata mu bada ranmu saboda 'yan'uwamu.
17 Men nenpòt ki gen byen a lemonn sa, pou l wè frè l nan bezwen, epi sere kè l kontre li, ki jan lamou Bondye kapab rete nan li?
Amma duk wanda yake da kayan duniya, ya ga dan'uwansa cikin bukata, kuma bai ji tausayinsa ba, ta yaya kaunar Allah ke cikinsa?
18 Ti moun yo, pa kite nou renmen avèk pawòl, ni avèk lang, men nan zèv ak nan verite.
'Ya'yana kaunatattu, kada muyi kauna ta fatar baki kawai, amma muyi aikin kauna da gaskiya.
19 Nou va rekonèt konsa ke nou nan laverite, epi va gen asirans nan kè nou devan Li:
Ta wurin haka mun sani mu masu gaskiya ne kuma mun tabbatar da zuciyarmu a gabansa.
20 si kè nou kondannen nou, Bondye se bokou pi gran ke kè nou, epi Li konnen tout bagay.
Gama idan zuciyarmu bata kayar damu ba, Allah ya fi zuciyarmu girma, kuma yana sane da kome.
21 Byeneme yo, si kè nou pa kondannen nou, nou gen konfyans devan Bondye.
Kaunatattu, idan zuciyarmu bata kashe mu ba, muna da gabagadi a gaban Allah.
22 Pou sa a, nenpòt ke nou mande, nou va resevwa de Li, paske nou kenbe kòmandman Li yo, epi fè bagay yo ki fè plezi devan zye Li yo.
Kuma duk abin da muka nema zamu samu a wurinsa, saboda muna kiyaye dokokinsa, muna yin abubuwan da suka gamshe shi.
23 Men sa se kòmandman Li, ke nou kwè nan non a Fis Li a, Jésus Kri, epi renmen yon lòt, kon Li te kòmande nou.
Kuma ummurninsa kenan: mu bada gaskiya ga sunan Dansa Yesu Almasihu, mu yi kaunar juna kuma kamar yanda ya bamu wannan doka.
24 Sila a ki kenbe kòmandman Li yo, rete nan Li, epi Li rete nan li menm. Nou konnen konsa ke Li rete nan nou, akoz Li te bay nou Lespri Li.
Duk wanda yake kiyaye umarnin Allah, yana cikinsa, Allah kuma yana cikin mutumin. Ta haka muka gane cewa yana cikinmu, Ta wurin Ruhu, wanda ya bamu.