< Προς Κορινθιους Α΄ 13 >
1 Ἐὰν ταῖς γλώσσαις τῶν ἀνθρώπων λαλῶ καὶ τῶν ἀγγέλων, ἀγάπην δὲ μὴ ἔχω, γέγονα χαλκὸς ἠχῶν ἢ κύμβαλον ἀλαλάζον.
Koda ya zamanto ina magana da harsunan mutane, har ma da na mala'iku, amma kuma ba ni da kauna, na zama kamar kararrawa mai yawan kara, ko kuge mai amo.
2 Καὶ ἐὰν ἔχω προφητείαν, καὶ εἰδῶ τὰ μυστήρια πάντα καὶ πᾶσαν τὴν γνῶσιν, καὶ ἐὰν ἔχω πᾶσαν τὴν πίστιν, ὥστε ὄρη μεθιστάνειν, ἀγάπην δὲ μὴ ἔχω, οὐθέν εἰμι.
Ko da ya zamanto ina da baiwar annabci kuma na fahimci dukkan boyayyar gaskiya, da dukkan ilimi, ko ina da matukar bangaskiya, har ma zan iya kawar da duwatsu. muddin ba ni da kauna, ni ba komai ba ne.
3 Καὶ ἐὰν ψωμίσω πάντα τὰ ὑπάρχοντά μου, καὶ ἐὰν παραδῶ τὸ σῶμά μου ἵνα καυθήσωμαι, ἀγάπην δὲ μὴ ἔχω, οὐδὲν ὠφελοῦμαι.
Ko da ya zamanto na bayar da dukan mallakata domin a ciyar da matalauta, in kuma mika jikina domin a kona. Amma in ba ni da kauna, ban sami ribar komai ba. (Na bayar da jikina ne domin inyi fahariya.)
4 Ἡ ἀγάπη μακροθυμεῖ, χρηστεύεται· ἡ ἀγάπη οὐ ζηλοῖ· ἡ ἀγάπη οὐ περπερεύεται, οὐ φυσιοῦται,
Kauna na da hakuri da kirki. kauna bata kishi ko fahariya. kauna ba ta girman kai
5 οὐκ ἀσχημονεῖ, οὐ ζητεῖ τὰ ἑαυτῆς, οὐ παροξύνεται, οὐ λογίζεται τὸ κακόν,
ko fitsara. Bata bautar kanta. Bata saurin fushi, kuma bata ajiyar lissafin laifuffuka.
6 οὐ χαίρει ἐπὶ τῇ ἀδικίᾳ, συγχαίρει δὲ τῇ ἀληθείᾳ,
Bata farin ciki da rashin adalci. A maimako, tana farin ciki da gaskiya.
7 πάντα στέγει, πάντα πιστεύει, πάντα ἐλπίζει, πάντα ὑπομένει.
Kauna tana jurewa cikin dukan abubuwa, tana gaskata dukan abubuwa, tana da yarda game da dukan abubuwa, tana daurewa dukan abubuwa.
8 Ἡ ἀγάπη οὐδέποτε ἐκπίπτει· εἴτε δὲ προφητεῖαι, καταργηθήσονται· εἴτε γλῶσσαι, παύσονται· εἴτε γνῶσις, καταργηθήσεται.
Kauna ba ta karewa. Idan akwai anabce anabce, zasu wuce. Idan akwai harsuna, zasu bace. Idan akwai ilimi, zaya wuce.
9 Ἐκ μέρους δὲ γινώσκομεν, καὶ ἐκ μέρους προφητεύομεν·
Domin muna da sani bisa - bisa kuma muna anabci bisa - bisa.
10 ὅταν δὲ ἔλθῃ τὸ τέλειον, τότε τὸ ἐκ μέρους καταργηθήσεται.
Sa'adda cikakke ya zo, sai marar kammalar ya wuce.
11 Ὅτε ἤμην νήπιος, ὡς νήπιος ἐλάλουν, ὡς νήπιος ἐφρόνουν, ὡς νήπιος ἐλογιζόμην· ὅτε δὲ γέγονα ἀνήρ, κατήργηκα τὰ τοῦ νηπίου.
Da nake yaro, nakan yi magana irinta kuruciya, nakan yi tunani irin na kuruciya, nakan ba da hujjojina irin na kuruciya. Da na isa mutum na bar halayen kuruciya.
12 Βλέπομεν γὰρ ἄρτι δι᾽ ἐσόπτρου ἐν αἰνίγματι, τότε δὲ πρόσωπον πρὸς πρόσωπον· ἄρτι γινώσκω ἐκ μέρους, τότε δὲ ἐπιγνώσομαι καθὼς καὶ ἐπεγνώσθην.
Gama yanzu muna gani sama - sama kamar ta madubi, amma a ranar fuska da fuska, yanzu na sani bisa - bisa, amma a lokacin zan sami cikakken sani kamar yadda aka yi mani cikakken sani.
13 Νυνὶ δὲ μένει πίστις, ἐλπίς, ἀγάπη, τὰ τρία ταῦτα· μείζων δὲ τούτων ἡ ἀγάπη.
To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata: bangaskiya, da gabagadi mai zuwa, da kuma kauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce kauna.