< Προς Τιμοθεον Α΄ 5 >
1 Πρεσβυτέρῳ μὴ ἐπιπλήξῃς, ἀλλὰ παρακάλει ὡς πατέρα, νεωτέρους ὡς ἀδελφούς,
Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin’yan’uwanka,
2 πρεσβυτέρας ὡς μητέρας, νεωτέρας, ὡς ἀδελφὰς ἐν πάσῃ ἁγνείᾳ.
tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye,’yan mata kuma a matsayin’yan’uwa da matuƙar tsarki.
3 χήρας τίμα τὰς ὄντως χήρας.
Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi.
4 εἰ δέ τις χήρα τέκνα ἢ ἔκγονα ἔχει, μανθανέτωσαν πρῶτον τὸν ἴδιον οἶκον εὐσεβεῖν καὶ ἀμοιβὰς ἀποδιδόναι τοῖς προγόνοις· τοῦτο γάρ ἐστιν ἀποδεκτὸν ἐνώπιον τοῦ θεοῦ.
Amma in gwauruwa tana da’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.
5 ἡ δὲ ὄντως χήρα καὶ μεμονωμένη ἤλπικεν ἐπὶ τὸν θεὸν καὶ προσμένει ταῖς δεήσεσιν καὶ ταῖς προσευχαῖς νυκτὸς καὶ ἡμέρας·
Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako.
6 ἡ δὲ σπαταλῶσα ζῶσα τέθνηκεν.
Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai.
7 καὶ ταῦτα παράγγελλε, ἵνα ἀνεπίλημπτοι ὦσιν.
Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.
8 εἰ δέ τις τῶν ἰδίων καὶ μάλιστα οἰκείων οὐ προνοεῖται, τὴν πίστιν ἤρνηται καὶ ἔστιν ἀπίστου χείρων.
In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.
9 χήρα καταλεγέσθω μὴ ἔλαττον ἐτῶν ἑξήκοντα γεγονυῖα ἑνὸς ἀνδρὸς γυνή,
Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta,
10 ἐν ἔργοις καλοῖς μαρτυρουμένη, εἰ ἐτεκνοτρόφησεν, εἰ ἐξενοδόχησεν, εἰ ἁγίων πόδας ἔνιψεν, εἰ θλιβομένοις ἐπήρκεσεν, εἰ παντὶ ἔργῳ ἀγαθῷ ἐπηκολούθησεν.
aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.
11 νεωτέρας δὲ χήρας παραιτοῦ· ὅταν γὰρ καταστρηνιάσωσιν τοῦ χριστοῦ, γαμεῖν θέλουσιν,
Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure.
12 ἔχουσαι κρῖμα, ὅτι τὴν πρώτην πίστιν ἠθέτησαν·
Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko.
13 ἅμα δὲ καὶ ἀργαὶ μανθάνουσιν περιερχόμεναι τὰς οἰκίας, οὐ μόνον δὲ ἀργαί, ἀλλὰ καὶ φλύαροι καὶ περίεργοι, λαλοῦσαι τὰ μὴ δέοντα.
Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba.
14 βούλομαι οὖν νεωτέρας γαμεῖν, τεκνογονεῖν, οἰκοδεσποτεῖν, μηδεμίαν ἀφορμὴν διδόναι τῷ ἀντικειμένῳ λοιδορίας χάριν·
Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna.
15 ἤδη γάρ τινες ἐξετράπησαν ὀπίσω τοῦ σατανᾶ.
Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan.
16 εἴ τις πιστὴ ἔχει χήρας, ἐπαρκείσθω αὐταῖς, καὶ μὴ βαρείσθω ἡ ἐκκλησία, ἵνα ταῖς ὄντως χήραις ἐπαρκέσῃ.
In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.
17 Οἱ καλῶς προεστῶτες πρεσβύτεροι διπλῆς τιμῆς ἀξιούσθωσαν, μάλιστα οἱ κοπιῶντες ἐν λόγῳ καὶ διδασκαλίᾳ·
Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa.
18 λέγει γὰρ ἡ γραφή, Βοῦν ἀλοῶντα οὐ φιμώσεις· καί, Ἄξιος ὁ ἐργάτης τοῦ μισθοῦ αὐτοῦ.
Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.”
19 κατὰ πρεσβυτέρου κατηγορίαν μὴ παραδέχου, ἐκτὸς εἰ μὴ ἐπὶ δύο ἢ τριῶν μαρτύρων.
Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku.
20 τοὺς ἁμαρτάνοντας, ἐνώπιον πάντων ἔλεγχε, ἵνα καὶ οἱ λοιποὶ φόβον ἔχωσιν.
Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro.
21 διαμαρτύρομαι ἐνώπιον τοῦ θεοῦ καὶ χριστοῦ Ἰησοῦ καὶ τῶν ἐκλεκτῶν ἀγγέλων, ἵνα ταῦτα φυλάξῃς χωρὶς προκρίματος, μηδὲν ποιῶν κατὰ πρόσκλισιν.
Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.
22 χεῖρας ταχέως μηδενὶ ἐπιτίθει, μηδὲ κοινώνει ἁμαρτίαις ἀλλοτρίαις, σεαυτὸν ἁγνὸν τήρει.
Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki.
23 μηκέτι ὑδροπότει, ἀλλὰ οἴνῳ ὀλίγῳ χρῶ, διὰ τὸν στόμαχον καὶ τὰς πυκνάς σου ἀσθενείας.
Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.
24 τινῶν ἀνθρώπων αἱ ἁμαρτίαι πρόδηλοί εἰσιν, προάγουσαι εἰς κρίσιν· τισὶν δὲ καὶ ἐπακολουθοῦσιν.
Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya.
25 ὡσαύτως καὶ τὰ ἔργα τὰ καλὰ πρόδηλα, καὶ τὰ ἄλλως ἔχοντα κρυβῆναι οὐ δύνανται.
Haka ma ayyuka nagari a fili suke, ko ba ma a fili suke ba, ba a iya ɓoye su.