< Προς Κορινθιους Α΄ 12 >
1 Περὶ δὲ τῶν πνευματικῶν, ἀδελφοί, οὐ θέλω ὑμᾶς ἀγνοεῖν.
Game da baye bayen Ruhu Mai Tsarki 'yan'uwa, bana so ku zama da jahilci.
2 Οἴδατε ὅτι ὅτε ἔθνη ἦτε, πρὸς τὰ εἴδωλα τὰ ἄφωνα ὡς ἂν ἤγεσθε, ἀπαγόμενοι.
Kun san cewa lokacin da ku ke al'ummai, an rude ku da alloli marasa magana ta hanyoyi dabam dabam marasa kan gado.
3 Διὸ γνωρίζω ὑμῖν ὅτι οὐδεὶς ἐν ˚Πνεύματι ˚Θεοῦ λαλῶν, λέγει, “Ἀνάθεμα ˚Ἰησοῦς”, καὶ οὐδεὶς δύναται εἰπεῖν, “˚Κύριος ˚Ἰησοῦς”, εἰ μὴ ἐν ˚Πνεύματι Ἁγίῳ.
Saboda haka ina so ku sani babu wanda ya ke magana da Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la'ananne ne.” Babu kuma wanda zaya ce, “Yesu Ubangili ne,” sai dai ta Ruhu Mai Tsarki.
4 Διαιρέσεις δὲ χαρισμάτων εἰσίν, τὸ δὲ αὐτὸ ˚Πνεῦμα.
Akwai bay bye iri iri, amma Ruhu daya ne.
5 Καὶ διαιρέσεις διακονιῶν εἰσιν, καὶ ὁ αὐτὸς ˚Κύριος.
Akwai hidimomi iri iri, amma Ubangiji daya ne.
6 Καὶ διαιρέσεις ἐνεργημάτων εἰσίν, καὶ ὁ αὐτὸς ˚Θεός, ὁ ἐνεργῶν τὰ πάντα ἐν πᾶσιν.
Akwai aikace aikace iri iri, amma Allah daya ke bayyanawa kowane mutum yadda zai aiwatar da su.
7 Ἑκάστῳ δὲ δίδοται ἡ φανέρωσις τοῦ ˚Πνεύματος πρὸς τὸ συμφέρον.
To ga kowanne an bayar da ikon nuna ayyukan Ruhu a fili domin amfanin kowa.
8 ὯΙ μὲν γὰρ διὰ τοῦ ˚Πνεύματος δίδοται λόγος σοφίας, ἄλλῳ δὲ λόγος γνώσεως κατὰ τὸ αὐτὸ ˚Πνεῦμα,
Ga wani ta wurin Ruhu an bayar da baiwar hikima, kuma ga wani kalmar sani ta wurin Ruhu daya.
9 ἑτέρῳ δὲ πίστις ἐν τῷ αὐτῷ ˚Πνεύματι, ἄλλῳ δὲ χαρίσματα ἰαμάτων ἐν τῷ ἑνὶ ˚Πνεύματι,
Ga wani an ba shi baiwar bangaskiya ta wurin Ruhun nan, ga wani kuwa an ba shi baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhun.
10 ἄλλῳ δὲ ἐνεργήματα δυνάμεων, ἄλλῳ προφητεία, ἄλλῳ διακρίσεις πνευμάτων, ἑτέρῳ γένη γλωσσῶν, ἄλλῳ δὲ ἑρμηνεία γλωσσῶν.
Ga wani yin ayyukan iko, ga wani kuwa annabci. Ga wani kuwa an ba shi baiwar bambance ruhohi, ga wani harsuna daban daban, kuma ga wani fassarar harsuna.
11 Πάντα δὲ ταῦτα ἐνεργεῖ τὸ ἓν καὶ τὸ αὐτὸ ˚Πνεῦμα, διαιροῦν ἰδίᾳ ἑκάστῳ καθὼς βούλεται.
Dukan wadannan Ruhu daya ne ya ke iza su, ya kuma rarraba baye bayen ga kowannen su yadda ya nufa.
12 Καθάπερ γὰρ τὸ σῶμα ἕν ἐστιν, καὶ μέλη πολλὰ ἔχει, πάντα δὲ τὰ μέλη τοῦ σώματος, πολλὰ ὄντα, ἕν ἐστιν σῶμα, οὕτως καὶ ὁ ˚Χριστός.
Kamar yadda jiki daya ne amma da gabobi da yawa kuma duk gabobin na jiki daya ne, haka nan Almasihu yake.
13 Καὶ γὰρ ἐν ἑνὶ ˚Πνεύματι ἡμεῖς πάντες εἰς ἓν σῶμα ἐβαπτίσθημεν, εἴτε Ἰουδαῖοι, εἴτε Ἕλληνες, εἴτε δοῦλοι, εἴτε ἐλεύθεροι, καὶ πάντες ἓν ˚Πνεῦμα ἐποτίσθημεν.
Gama ta Ruhu daya aka yi wa kowa baftisma cikin jiki daya, ko Yahudawa ko al'ummai, ko bayi ko 'ya'ya, dukan mu kuwa an shayar da mu Ruhu daya.
14 Καὶ γὰρ τὸ σῶμα οὐκ ἔστιν ἓν μέλος, ἀλλὰ πολλά.
Gama jiki ba daya ba ne sungun, amma gabobi ne da yawa.
15 Ἐὰν εἴπῃ ὁ πούς, “Ὅτι οὐκ εἰμὶ χείρ, οὐκ εἰμὶ ἐκ τοῦ σώματος”, οὐ παρὰ τοῦτο, οὐκ ἔστιν ἐκ τοῦ σώματος.
Idan kafa ta ce, “tun da dai ni ba hannu ba ne to ni ba fannin jikin bane,” wannan baya rage masa matsayin sa a jikin ba.
16 Καὶ ἐὰν εἴπῃ τὸ οὖς, “Ὅτι οὐκ εἰμὶ ὀφθαλμός, οὐκ εἰμὶ ἐκ τοῦ σώματος”, οὐ παρὰ τοῦτο, οὐκ ἔστιν ἐκ τοῦ σώματος.
Kuma da kunne zaya ce, '''Da yake ni ba ido ba ne, ai, ni ba gabar jiki ba ne,'' fadar haka ba za ta raba shi da zama gabar jikin ba.
17 Εἰ ὅλον τὸ σῶμα ὀφθαλμός, ποῦ ἡ ἀκοή; Εἰ ὅλον ἀκοή, ποῦ ἡ ὄσφρησις;
Idan dukan jikin ya kasance ido ne da me za a ji? Da dukan jikin kunne ne, da me za a sunsuna?
18 Νυνὶ δὲ ὁ ˚Θεὸς ἔθετο τὰ μέλη, ἓν ἕκαστον αὐτῶν ἐν τῷ σώματι, καθὼς ἠθέλησεν.
Amma Allah ya shirya gabobin jiki bisa ga tsarin sa.
19 Εἰ δὲ ἦν τὰ πάντα ἓν μέλος, ποῦ τὸ σῶμα;
Amma da duk jiki gaba daya ce, da ina jikin zai kasance?
20 Νῦν δὲ πολλὰ μὲν μέλη, ἓν δὲ σῶμα.
Ga shi akwai gabobi da yawa, kuma jiki daya ne.
21 Οὐ δύναται δὲ ὁ ὀφθαλμὸς εἰπεῖν τῇ χειρί, “Χρείαν σου οὐκ ἔχω”, ἢ πάλιν ἡ κεφαλὴ τοῖς ποσίν, “Χρείαν ὑμῶν οὐκ ἔχω.”
Ba da ma ido ya fadawa hannu, ''Bana bukatar ka,'' ko kuma kai ya fadawa kafafu, ''Ba na bukatar ku.''
22 Ἀλλὰ πολλῷ μᾶλλον τὰ δοκοῦντα μέλη τοῦ σώματος ἀσθενέστερα ὑπάρχειν, ἀναγκαῖά ἐστιν,
Amma, sai ma gabobin da ake gani kamar raunannu su ne masu humimmanci, gabobin jiki kuwa da ake gani kamar sun kasa sauran daraja, mu kan fi ba su martaba.
23 καὶ ἃ δοκοῦμεν ἀτιμότερα εἶναι τοῦ σώματος, τούτοις τιμὴν περισσοτέραν περιτίθεμεν, καὶ τὰ ἀσχήμονα ἡμῶν, εὐσχημοσύνην περισσοτέραν ἔχει,
Ta haka gabobinmu marasa kyan gani, akan kara kyautata ganinsu. Gabobin mu masu kyan kuma ba sai an yi masu ado ba.
24 τὰ δὲ εὐσχήμονα ἡμῶν, οὐ χρείαν ἔχει. Ἀλλὰ ὁ ˚Θεὸς συνεκέρασεν τὸ σῶμα, τῷ ὑστερουμένῳ, περισσοτέραν δοὺς τιμήν,
Amma Allah ne da kansa ya hada jiki, yana bada mafificiyar martaba ga kaskantacciyar gaba.
25 ἵνα μὴ ᾖ σχίσμα ἐν τῷ σώματι, ἀλλὰ τὸ αὐτὸ ὑπὲρ ἀλλήλων μεριμνῶσι τὰ μέλη.
Yayi haka ne domin kada a sami tsattsaguwa a cikn jikin, amma domin gabobin su kula da juna da matsananciyar lura.
26 Καὶ εἴτε πάσχει ἓν μέλος, συμπάσχει πάντα τὰ μέλη· εἴτε δοξάζεται μέλος, συγχαίρει πάντα τὰ μέλη.
Kuma idan gaba daya na wahala, dukan gabobin suna wahala tare. ko kuma idan an girmama gaba daya, dukan gabobin na farin ciki tare.
27 Ὑμεῖς δέ ἐστε σῶμα ˚Χριστοῦ, καὶ μέλη ἐκ μέρους.
Yanzu ku jikin Almasihu ne, saboda haka kuma kowannen ku gabarsa ne.
28 Καὶ οὓς μὲν ἔθετο ὁ ˚Θεὸς ἐν τῇ ἐκκλησίᾳ πρῶτον ἀποστόλους, δεύτερον προφήτας, τρίτον διδασκάλους, ἔπειτα δυνάμεις, ἔπειτα χαρίσματα ἰαμάτων, ἀντιλήμψεις, κυβερνήσεις, γένη γλωσσῶν.
A cikin ikilisiya, Allah ya sa wasu su zama, na farko manzanni, na biyu annabawa, na uku masu koyarwa, sa'an nan sai masu yin ayyukan iko, sai masu aikin warkarwa, da masu bayar da taimako, da masu aikin tafiyar da al'amura, da masu harsuna daban daban.
29 Μὴ πάντες ἀπόστολοι; Μὴ πάντες προφῆται; Μὴ πάντες διδάσκαλοι; Μὴ πάντες δυνάμεις;
To kowa manzo ne? ko kuwa duka annabawa ne? ko kuma duka masu koyarwa ne? Kowa ne ke yin manyan ayyukan iko?
30 Μὴ πάντες χαρίσματα ἔχουσιν ἰαμάτων; Μὴ πάντες γλώσσαις λαλοῦσιν; Μὴ πάντες διερμηνεύουσιν;
Ko kuwa dukan su ne suke da baiwar warkarwa? Dukan su ne ke magana da harsuna? ko kuma dukan su ne ke fassara harsuna?
31 Ζηλοῦτε δὲ τὰ χαρίσματα τὰ μείζονα. Καὶ ἔτι καθʼ ὑπερβολὴν ὁδὸν, ὑμῖν δείκνυμι.
Amma bari ku himmantu ga neman baiwa mafi girma. Kuma zan nuna maku wata hanya mafificiya.