< Προς Κορινθιους Α΄ 3 >
1 Καὶ ἐγώ, ἀδελφοί, οὐκ ἠδυνήθην ὑμῖν λαλῆσαι ὡς πνευματικοῖς, ἀλλ᾽ ὡς σαρκικοῖς, ὡς νηπίοις ἐν Χριστῷ.
Amma ni, yan'uwa, ba zan iya magana da ku kamar mutane masu ruhaniya ba, amma kamar mutane masu jiki, kamar jarirai cikin Almasihu.
2 γάλα ὑμᾶς ἐπότισα καὶ οὐ βρῶμα· οὔπω γὰρ ἠδύνασθε. ἀλλ᾽ οὔτε ἔτι νῦν δύνασθε· ἔτι γὰρ σαρκικοί ἐστε.
Na shayar da ku da Madara ba da nama ba, don baku isa cin nama ba, kuma ko yanzu ma baku isa ba.
3 ὅπου γὰρ ἐν ὑμῖν ζῆλος καὶ ἔρις καὶ διχοστασίαι, οὐχὶ σαρκικοί ἐστε καὶ κατὰ ἄνθρωπον περιπατεῖτε;
Gama har yanzu ku masu jiki ne. Muddin akwai kishi da jayayya a tsakaninku, ashe, ku ba masu jiki ba ne, kuma kuna tafiya bisa magwajin mutane?
4 ὅταν γὰρ λέγῃ τις, ἐγὼ μέν εἰμι Παύλου, ἕτερος δὲ ἐγὼ Ἀπολλώ, οὐχὶ σαρκικοί ἐστε;
Domin in wani ya ce, “Ina bayan Bulus,” wani kuma ya ce, “Ina bayan Afollos,” ashe, ba zaman mutuntaka kuke yi ba?
5 Τίς οὖν ἐστι Παῦλος, τίς δὲ Ἀπολλὼς ἀλλ᾽ ἢ διάκονοι δι᾽ ὧν ἐπιστεύσατε, καὶ ἑκάστῳ ὡς ὁ Κύριος ἔδωκεν;
To wanene Afollos? Wanene kuma Bulus? Bayi ne wadanda kuka bada gaskiya ta wurin su, kowannen su kuwa Allah ya bashi ayyuka.
6 ἐγὼ ἐφύτευσα, Ἀπολλὼς ἐπότισεν, ἀλλ᾽ ὁ Θεὸς ηὔξανεν·
Ni nayi shuka, Afolos yayi banruwa, amma Allah ne ya sa girma.
7 ὥστε οὔτε ὁ φυτεύων ἐστί τι οὔτε ὁ ποτίζων, ἀλλ᾽ ὁ αὐξάνων Θεός.
Don haka, da mai shukar da mai banruwan, ba komi bane. Amma Allah ne mai sa girman.
8 ὁ φυτεύων δὲ καὶ ὁ ποτίζων ἕν εἰσιν· ἕκαστος δὲ τὸν ἴδιον μισθὸν λήψεται κατὰ τὸν ἴδιον κόπον.
Da mai shukar, da mai banruwan, duk daya suke, kuma kowannen su zai sami nasa lada, gwargwadon aikinsa.
9 Θεοῦ γάρ ἐσμεν συνεργοί· Θεοῦ γεώργιον, Θεοῦ οἰκοδομή ἐστε.
Gama mu abokan aiki ne na Allah. Ku gonar Allah ne, ginin Allah kuma.
10 Κατὰ τὴν χάριν τοῦ Θεοῦ τὴν δοθεῖσάν μοι ὡς σοφὸς ἀρχιτέκτων θεμέλιον τέθεικα, ἄλλος δὲ ἐποικοδομεῖ· ἕκαστος δὲ βλεπέτω πῶς ἐποικοδομεῖ·
Bisa ga alherin Allah da aka bani a matsayin gwanin magini, na kafa harsashi, wani kuma yana dora gini a kai. Sai dai kowane mutum, ya lura da yadda yake dora ginin.
11 θεμέλιον γὰρ ἄλλον οὐδεὶς δύναται θεῖναι παρὰ τὸν κείμενον, ὅς ἐστιν Ἰησοῦς Χριστός.
Gama ba wanda ke iya kafa wani harsashin daban da wanda aka rigaya aka kafa, wato, Yesu Almasihu.
12 εἰ δέ τις ἐποικοδομεῖ ἐπὶ τὸν θεμέλιον τοῦτον χρυσόν, ἄργυρον, λίθους τιμίους, ξύλα, χόρτον, καλάμην,
Yanzu fa in wani ya dora gini a kan harashin da zinariya, ko azurfa, ko duwatsu masu daraja, ko itace, ko ciyawa, ko tattaka,
13 ἑκάστου τὸ ἔργον φανερὸν γενήσεται· ἡ γὰρ ἡμέρα δηλώσει· ὅτι ἐν πυρὶ ἀποκαλύπτεται· καὶ ἑκάστου τὸ ἔργον ὁποῖόν ἐστι τὸ πῦρ δοκιμάσει.
aikinsa zai bayyanu, domin ranar nan zata tona shi. Gama za a bayyana shi cikin wuta. Wutar kuwa zata gwada ingancin aikin da kowa ya yi.
14 εἴ τινος τὸ ἔργον μενεῖ ὃ ἐπῳκοδόμησε, μισθὸν λήψεται·
Duk wanda aikinsa ya tsaya, zai karbi lada;
15 εἴ τινος τὸ ἔργον κατακαήσεται, ζημιωθήσεται, αὐτὸς δὲ σωθήσεται, οὕτως δὲ ὡς διὰ πυρός.
amma duk wanda aikinsa ya kone, zai sha Asara, amma shi kansa zai tsira, sai dai kamar ta tsakiyar wuta.
16 Οὐκ οἴδατε ὅτι ναὸς Θεοῦ ἐστε καὶ τὸ Πνεῦμα τοῦ Θεοῦ οἰκεῖ ἐν ὑμῖν;
Ashe, baku san ku haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikin ku?
17 εἴ τις τὸν ναὸν τοῦ Θεοῦ φθείρει, φθερεῖ τοῦτον ὁ Θεός· ὁ γὰρ ναὸς τοῦ Θεοῦ ἅγιός ἐστιν, οἵτινές ἐστε ὑμεῖς.
Idan wani ya lalata haikalin Allah, Allah zai lalata shi. Gama haikalin Allah mai tsarki ne, kuma haka ku ke.
18 Μηδεὶς ἑαυτὸν ἐξαπατάτω· εἴ τις δοκεῖ σοφὸς εἶναι ἐν ὑμῖν ἐν τῷ αἰῶνι τούτῳ, μωρὸς γενέσθω, ἵνα γένηται σοφός. (aiōn )
Kada kowa ya rudi kansa. Idan wani a cikin ku na ganin shi mai hikima ne a wannan zamani, bari ya zama” wawa” domin ya zama mai hikima. (aiōn )
19 ἡ γὰρ σοφία τοῦ κόσμου τούτου μωρία παρὰ τῷ Θεῷ ἐστι. γέγραπται γάρ· ὁ δρασσόμενος τοὺς σοφοὺς ἐν τῇ πανουργίᾳ αὐτῶν·
Gama hikimar duniyar nan wauta ce a gun Allah. Gama a rubuce yake, “Yakan kama masu hikima a cin makircin su.”
20 καὶ πάλιν· Κύριος γινώσκει τοὺς διαλογισμοὺς τῶν σοφῶν, ὅτι εἰσὶ μάταιοι.
Har wa yau, “Ubangiji ya san tunanin masu hikima banza ne.”
21 ὥστε μηδεὶς καυχάσθω ἐν ἀνθρώποις· πάντα γὰρ ὑμῶν ἐστιν,
haka ba sauran fariya akan mutane! Domin kuwa kome naku ne,
22 εἴτε Παῦλος εἴτε Ἀπολλὼς εἴτε Κηφᾶς εἴτε κόσμος εἴτε ζωὴ εἴτε θάνατος εἴτε ἐνεστῶτα εἴτε μέλλοντα, πάντα ὑμῶν ἐστιν,
Ko Bulus, ko Afollos, ko kefas, ko duniya, ko rai, ko mutuwa, ko abubuwa na yanzu, ko abubuwa masu zuwa. Duka naku ne,
23 ὑμεῖς δὲ Χριστοῦ, Χριστὸς δὲ Θεοῦ.
Ku kuwa na Almasihu ne, Almasihu kuma na Allah ne.