< Psalm 39 >

1 Dem Vorsänger, dem Jeduthun. Ein Psalm Davids. Ich habe gesagt: Ich will achten auf meine Wege, daß ich nicht sündige mit meiner Zunge; ich will meinem Mund einen Zaum anlegen, solange der Gottlose vor mir ist.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Yedutun. Zabura ta Dawuda. Na ce, “Zan lura da hanyoyina zan kuma kiyaye harshena daga zunubi; zan sa linzami a bakina muddin mugaye suna a gabana.”
2 Ich war gänzlich verstummt, schwieg auch vom Guten, aber mein Schmerz machte mich unglücklich.
Na yi shiru, ban ce kome ba, Ko a kan abin da yake da kyau! Amma duk da haka wahalata sai ƙaruwa take yi;
3 Mein Herz entbrannte in mir, durch mein Nachsinnen ward ein Feuer entzündet, ich mußte reden mit meiner Zunge.
zuciyata ta ƙara zafi a cikina. Kuma sa’ad da nake tunani, wuta ta yi ta kuna; sai na yi magana da harshena na ce,
4 Tue mir kund, o HERR, mein Ende und welches das Maß meiner Tage sei, damit ich weiß, wie vergänglich ich bin!
“Nuna mini, ya Ubangiji, ƙarshen rayuwata da kuma yawan kwanakina; bari in san yadda rayuwata tana wucewa da sauri.
5 Siehe, nur Handbreiten lang hast du meine Tage gemacht, und meine Lebenszeit ist wie nichts vor dir; wahrlich, jeder Mensch, wie fest er steht, ist nur ein Hauch! (Pause)
Ka sa kwanakina suka zama tafin hannu ne kawai; yawan shekaruna kamar ba kome ba ne a gabanka. Duk ran mutum shaƙar iska ne kurum, har ma waɗanda suke tsammani suke da kāriya. (Sela)
6 Ja, nur ein wandelnder Schatten ist jedermann; wahrlich, sie machen sich viel vergebliche Unruhe; sie sammeln und wissen nicht, wer es kriegen wird.
“Mutum dai shirim ne kawai yayinda yake kai da komowa. Yana ta yawo, amma a banza ne kawai; yakan tara dukiya, ba tare da sanin wa zai more ta ba.
7 Und nun, Herr, worauf habe ich gewartet? Meine Hoffnung steht zu dir!
“Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan nema? Begena yana a gare ka.
8 Errette mich von allen meinen Übertretungen, mache mich nicht den Narren zum Gespött!
Ka cece ni daga dukan laifofina; kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye.
9 Ich schweige und tue meinen Mund nicht auf; denn du hast es getan.
Na yi shiru; ba zan buɗe bakina ba, gama kai ne wanda ka aikata wannan.
10 Wende deine Plage von mir; denn ich bin verschmachtet von der Strafe deiner Hand.
Ka ɗauke bulalarka daga gare ni; na ji jiki ta wurin bugun da hannunka ya yi mini.
11 Wenn du jemand züchtigst um der Sünde willen, so lässest du gleich der Motte seine Schönheit vergehen; jeder Mensch ist nur ein Hauch! (Pause)
Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu; kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi, kowane mutum dai shaƙar iska ne. (Sela)
12 HERR, höre mein Gebet und vernimm mein Schreien; schweige nicht zu meinen Tränen; denn ich bin ein Gast bei dir, ein Pilgrim wie alle meine Väter.
“Ka ji addu’ata, ya Ubangiji, ka saurari kukata ta neman taimako; kada ka kurmance ga kukata. Gama ina zama tare da kai kamar baƙo, baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance.
13 Blicke weg von mir, daß ich mich erheitere, ehe ich dahinfahre und nicht mehr sei!
Ka kau da fuskarka daga gare ni, saboda in sāke yin farin ciki kafin in tafi in kuma rabu da nan.”

< Psalm 39 >