< 5 Mose 8 >

1 "Ihr sollt das ganze Gesetz, das ich dir heute gebiete, mit Bedacht erfüllen, auf daß ihr leben bleibet, euch mehret und das Land besetzet, das der Herr euren Vätern zugeschworen!
Ku hankali, ku bi kowane umarnin da nake ba ku a yau, saboda ku rayu, ku ƙaru, ku kuma shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku.
2 Gedenke des ganzen Weges, den dich der Herr, dein Gott, seit vierzig Jahren in der Steppe geführt hat, dich zu demütigen und zu prüfen, um zu erfahren, was in deinem Herzen ist, ob du seine Gebote halten wirst oder nicht!
Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku a dukan hanya, a cikin hamada waɗannan shekaru arba’in, don yă ƙasƙantar da ku, yă kuma gwada ku don yă san abin da yake a zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa, ko babu.
3 Er beugte dich und ließ dich hungern; aber dann speiste er dich mit Manna, das dir und deinen Vätern unbekannt gewesen, um dich zu lehren, daß der Mensch nicht vom Brot allein lebe, sondern daß der Mensch von allem lebt, was durch des Herrn Mund entsteht.
Ya ƙasƙantar da ku, ya bar ku da yunwa, sa’an nan ya ciyar da ku da Manna, wadda ku, ko kakanninku, ba su sani ba, ta haka ne ya sa kuka sani cewa, ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta wurin kowace kalmar da ta fito daga bakin Ubangiji.
4 Dein Kleid ist nicht an dir zerfallen, und dein Fuß nicht geschwollen, diese vierzig Jahre.
Tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba a waɗannan shekaru arba’in.
5 So erkenne in deinem Herzen, daß dich der Herr, dein Gott, so erzieht, wie jemand seinen Sohn erzieht!
Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku.
6 Halte die Gebote des Herrn, deines Gottes, auf seinen Wegen wandelnd und ihn fürchtend!
Ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuna tafiya cikin hanyoyinsa, kuna kuma girmama shi.
7 Denn der Herr, dein Gott, bringt dich in ein treffliches Land, in ein Land mit Wasserbächen, Quellen und Seen, die im Tal und auf dem Berg entspringen,
Gama Ubangiji Allahnku yana fitar da ku zuwa cikin ƙasa mai kyau, ƙasa mai rafuffuka da tafkunan ruwa, tare da maɓulɓulai masu gudu a kwari da tuddai;
8 in ein Land mit Weizen und Gerste, Weinreben, Feigen und Granaten, in ein Land mit Oliven und Honig,
ƙasa mai alkama da sha’ir, inabi da ɓaure, rumman, man zaitun da zuma;
9 in ein Land, wo du nicht kümmerlich Brot essen mußt, sondern keinen Mangel hast, in ein Land, dessen Steine Eisen sind und aus dessen Bergen du Erz gräbst.
ƙasa inda abinci ba zai yi ƙaranci ba, ba kuma za ku rasa kome ba; ƙasa ce inda ƙarfe ne duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.
10 Du wirst essen und satt werden. Preise dann den Herrn, deinen Gott, für das treffliche Land, das er dir gegeben!
Sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sai ku yabi Ubangiji Allahnku saboda ƙasa mai kyau da ya ba ku.
11 Hüte dich, daß du nicht des Herrn, deines Gottes, vergäßest und seine Gesetze, Gebote und Gebräuche nicht mehr hieltest, die ich dir heute gebiete!
Ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji Allahnku, har ku kāsa kiyaye umarnansa, dokokinsa da ƙa’idodinsa da nake ba ku a wannan rana ba.
12 Issest du dich satt und baust schöne Wohnhäuser,
To, sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sa’ad da kuka gina gidaje masu kyau, kuka zauna,
13 mehren sich deine Rinder und Schafe, wird dir Silber und Gold in Menge zu eigen, mehrt sich all das Deine,
sa’ad da kuma garkunanku na shanu da na tumaki suka ƙaru, azurfanku da zinariyarku kuma suka ƙaru, sa’an nan dukan abin da kuke da shi ya haɓaka,
14 dann werde nicht dein Herz hochmütig! Vergiß nicht des Herrn, deines Gottes, der dich aus Ägypterlande geführt, aus dem Sklavenhause,
to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma.
15 der dich geleitet durch die große schreckliche Wüste, wo Schlangen, Nattern und Skorpione sind und Dürre, wo kein Wasser ist; der dir Wasser quellen ließ aus Kieselfelsen,
Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.
16 der dich in der Wüste mit Manna speiste, das deine Väter nicht gekannt, der dich beugte und prüfte, damit er dir Gutes tun könnte in deiner Zukunft!
Ya ba ku Manna don ku ci a cikin hamada, wani abin da kakanninku ba su taɓa sani ba, don yă ƙasƙantar yă kuma gwada ku, saboda yă yi muku alheri daga baya.
17 Denke nicht: 'Meine Kraft und die Stärke meiner Hand hat mir diesen Reichtum verschafft!'
Wataƙila ku ce wa kanku, “Ikona da ƙarfin hannuwana ne suka ba ni da wannan arziki.”
18 Bedenke, daß der Herr, dein Gott, dir Kraft gibt, Reichtum zu schaffen, damit er seinen Bund bekräftige, den er deinen Vätern zugeschworen, wie es heute ist!
Amma ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne wanda yake ba ku azanci na yin arziki, ta haka kuwa ya tabbatar da alkawarinsa, wanda ya rantse wa kakanninku, kamar yadda yake a yau.
19 Vergissest du aber des Herrn, deines Gottes, folgst du anderen Göttern, dienst ihnen und wirfst dich vor ihnen hin, so erkläre ich euch zum voraus aufs feierlichste, daß ihr umkommen werdet.
In kuka manta da Ubangiji Allahnku, kuka kuma bi waɗansu alloli, kuka yi musu sujada, kuka kuma rusuna musu, to, a yau ina gargaɗe ku cewa tabbatacce za a hallaka ku.
20 Wie die Völker, die der Herr vor euch vertilgt, so werdet ihr umkommen, zur Strafe dafür, daß ihr nicht auf die Stimme des Herrn, eures Gottes, hört."
Kamar al’ummai da Ubangiji ya hallakar kafin ku, haka zai hallaka ku, domin ba ku yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku ba.

< 5 Mose 8 >