< Genèse 20 >
1 Et Abraham se transporta de là dans la région du Midi, et se fixa entre Kadès et Sur, et fit un séjour à Gérar.
Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi wajajen Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. Ya zauna a Gerar na ɗan lokaci,
2 Et Abraham disait de Sarah, sa femme: C'est ma sœur. Alors Abimélech, roi de Gérar, envoya enlever Sarah.
a can ne Ibrahim ya ce game da matarsa Saratu, “Ita’yar’uwata ce.” Sai Abimelek sarkin Gerar ya aiko a kawo masa Saratu.
3 Mais Dieu descendit vers Abimélech dans un songe de la nuit, et lui dit: Voici, tu vas mourir à cause de la femme que tu as enlevée et qui est mariée à un mari.
Amma wata rana da dad dare Allah ya zo wa Abimelek a cikin mafarki ya ce masa, “Kai da matacce ɗaya kuke, saboda matar da ka ɗauka. Ita matar aure ce.”
4 Cependant Abimélech ne s'était point approché d'elle. Et il dit: Seigneur, veux-tu faire périr un peuple, même innocent?
Abimelek dai bai riga ya kusace ta ba tukuna, saboda haka ya ce, “Ya Ubangiji za ka hallaka al’umma marar laifi?
5 Ne m'a-t-il pas dit: C'est ma sœur, et elle, elle-même a dit: Il est mon frère? C'est dans l'innocence de mon cœur et la pureté de mes mains que je l'ai fait.
Ba shi ne ya ce mini, ‘Ita’yar’uwata ba ce,’ ita ma ba tă ce, ‘Shi ɗan’uwana ba ne’? Na yi haka da kyakkyawan nufi da hannuwa masu tsabta.”
6 Et Dieu lui dit en songe: Je sais aussi que tu l'as fait dans l'innocence de ton cœur, et aussi t'ai-je empoché de pécher contre moi; c'est pourquoi je n'ai pas permis que tu la touchasses.
Sai Allah ya ce masa a cikin mafarki “I, na san ka yi wannan da kyakkyawan nufi, saboda haka ne na kiyaye ka daga yin mini zunubi. Shi ya sa ban bar ka ka taɓa ta ba.
7 Maintenant donc rends la femme à son mari, car il est prophète et il intercédera pour toi, afin que tu vives; mais si tu ne la rends pas, sache que tu mourras, toi et tout ce qui t'appartient.
Yanzu ka komar da matar mutumin, gama shi annabi ne, zai kuma yi maka addu’a, za ka kuwa rayu. In ba ka komar da ita ba fa, ka sani tabbatacce kai da dukan abin da yake naka za ku mutu.”
8 Alors Abimélech se leva le matin, et manda tous ses serviteurs, et redit toutes ces choses à leurs oreilles, et ces hommes furent très effrayés.
Kashegari da sassafe, sai Abimelek ya tara dukan fadawansa, ya faɗa musu duk abin da ya faru, suka ji tsoro ƙwarai da gaske.
9 Et Abimélech fit appeler a Abraham et lui dit: Qu'est-ce que tu nous as fait, et en quoi ai-je manqué à ton égard que tu aies attiré sur moi et sur mon royaume une si grande culpabilité? Tu t'es porté envers moi à des actions qu'on ne fait pas.
Sa’an nan Abimelek ya kira Ibrahim ciki ya ce, “Me ke nan ka yi mana? Ta wace hanya ce na yi maka laifi har da ka kawo irin wannan babban laifi a kaina da kuma masarautata? Ka yi mini abubuwan da bai kamata a yi ba.”
10 Et Abimélech dit à Abraham: Qu'avais-tu en vue pour en agir ainsi avec moi?
Abimelek ya kuma ce wa Ibrahim, “Me ya sa ka yi wannan?”
11 Et Abraham dit: C'est que je me disais: assurément il n'y a aucune crainte de Dieu dans ce lieu, et ils me tueront à cause de ma femme.
Ibrahim ya ce, “Na ce a raina, ‘Tabbatacce babu tsoron Allah a wannan wuri, za su kuwa kashe ni saboda matata.’
12 Aussi bien elle est vraiment ma sœur, fille de mon père, seulement n'est-elle pas fille de ma mère, et elle est devenue ma femme.
Ban da haka, tabbatacce ita’yar’uwata ce,’yar mahaifina, ko da yake ba daga uwata ba, ta kuma zama matata.
13 Et lorsque Dieu me fit quitter, pour voyager, la maison de mon père, je lui dis: Fais-moi cette grâce: dans quelque lieu que nous allions, dis de moi: C'est mon frère.
Sa’ad da Allah ya sa na tashi daga gidan mahaifina na ce mata, ‘Wannan shi ne yadda za ki nuna mini ƙaunarki. Duk inda muka tafi, ki ce game da ni, “Shi ɗan’uwana ne.”’”
14 Alors Abimélech prit des brebis et des bœufs et des serviteurs et des servantes, et en fit un don à Abraham et lui rendit Sarah, sa femme.
Sai Abimelek ya kawo awaki da shanu da bayi maza da mata, ya ba wa Ibrahim, ya kuma komar da Saratu matarsa gare shi.
15 Et Abimélech dit: Tu as tout mon pays devant toi; établis-toi où il le plaira.
Abimelek ya kuma ce, “Ƙasata tana gabanka, ka zauna a duk inda kake so.”
16 Et à Sarah il dit: Voici, j'ai donné mille sicles d'argent à ton frère: eh bien! que ce soit une réparation auprès de tous tes entours, et auprès de tous le voilà justifiée.
Ga Saratu kuwa ya ce, “Ina ba wa ɗan’uwanki shekel dubu na azurfa, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa cewa ba ki da laifi.”
17 Alors Abraham intercéda auprès de Dieu, et Dieu guérit Abimélech et sa femme et ses servantes, et elles purent enfanter.
Sai Ibrahim ya yi addu’a ga Allah, Allah kuma ya warkar da Abimelek, da matarsa da bayinsa mata domin su haihu,
18 Car l'Éternel avait frappé de stérilité toutes les femmes de la maison d'Abimélech, à cause de Sarah, femme d'Abraham.
gama Ubangiji ya rufe kowace mahaifa a gidan Abimelek saboda Saratu, matar Ibrahim.