< Ézéchiel 1 >
1 La trentième année, le quatrième mois, le cinquième jour du mois, comme j'étais parmi les captifs près du fleuve Chébar, les Cieux s'ouvrirent, et je vis des visions de Dieu.
A shekara ta talatin, a wata na huɗu a rana biyar, yayinda nake cikin’yan zaman bauta kusa da Kogin Kebar, sai sammai suka buɗe na kuwa ga wahayoyin Allah.
2 Le cinquième jour du mois (c'était la cinquième année de la captivité du roi Jéhojachin),
A rana biyar ga wata, a shekara ta biyar ne ta zaman bautan Sarki Yehohiyacin,
3 la parole de l'Éternel fut adressée à Ézéchiel, fils de Buzi, le sacrificateur, dans le pays des Chaldéens, près du fleuve Chébar; et là, la main de l'Éternel fut sur lui.
maganar Ubangiji ta zo wa Ezekiyel firist, ɗan Buzi, kusa da Kogin Kebar a ƙasar Babiloniyawa. A can hannun Ubangiji yana a kansa.
4 Et je regardai, et voici, du nord arrivait un tourbillon, une grande nuée et un globe de feu; et une splendeur l'environnait, et de son centre, du centre du feu, sortait comme l'éclat de l'airain.
Na duba, sai na ga guguwa ta taso daga arewa babban hadari cike da walƙiya kewaye da haske mai haske sosai. Tsakiyar wutar ta yi kamar ƙarfe mai cin wuta balbal,
5 Et de son centre sortait une forme de quatre animaux; et tel était leur aspect: ils avaient une figure humaine.
a cikin wutar kuwa akwai abin da ya yi kamar halittu guda huɗu. A bayyane kamanninsu ya yi kamar siffar mutum,
6 Et chacun d'eux avait quatre faces, et chacun d'eux avait quatre ailes.
amma kowannensu yana da fuskoki huɗu da fikafikai guda huɗu.
7 Et leurs pieds étaient droits, et la plante de leurs pieds avait la forme du pied d'un veau, et ils brillaient comme l'éclat de l'airain poli.
Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne; kuma ƙafafunsu sun yi kamar na maraƙi suna kuma walƙiya kamar tagullar da aka goge.
8 Et ils avaient par-dessous leurs ailes des mains d'homme, à chacun de leurs quatre côtés; et tous quatre ils avaient leurs visages et leurs ailes.
A ƙarƙashin fikafikansu huɗu suna da hannuwan mutum a kowane gefe. Dukansu huɗu suna da fuskoki da fikafikai,
9 Leurs ailes étaient attachées l'une à l'autre; ils ne se tournaient point en se mettant en marche, mais ils suivaient chacun la direction de leurs faces.
kuma fikafikansu suna taɓan juna. Kowanne ya miƙe gaba; ba sa juyawa sa’ad da suke tafiya.
10 [Par devant] leurs faces avaient la figure de la face d'un homme, et à droite la figure de celle d'un lion pour tous les quatre, et à gauche la figure de celle d'un bœuf pour tous les quatre, et [par derrière] celle d'un aigle pour tous les quatre.
Fuskokinsu sun yi kamar haka. Kowanne a cikin huɗun yana da fuskar mutum, kuma a gefen dama kowanne yana da fuskar zaki, a hagu kuma fuskar maraƙi; kowanne yana kuma da fuskar gaggafa.
11 Et en haut leurs faces et leurs ailes étaient séparées; deux ailes des uns étaient attachées aux ailes des autres, et deux couvraient leurs corps.
Haka fuskokinsu suka kasance. Fikafikansu sun buɗu sama; kowanne yana da fikafikai biyu, ɗaya yana taɓa fikafikan ɗayan halittar a ɗayan gefe, fikafikai biyu kuma suna rufe jikinsa.
12 Or ils allaient chacun dans la direction de leurs faces; ils allaient où l'esprit les poussait à aller, et ne se tournaient point dans leur marche.
Kowanne ya miƙe gaba sosai. Duk inda ruhu zai tafi, can za su, ba tare da juyawa ba yayinda suke tafiya.
13 Et l'aspect de ces animaux ressemblait à des charbons de feu brûlants; c'était comme l'aspect des flambeaux, et ce feu circulait entre les animaux, et répandait de l'éclat, et du feu sortaient des éclairs.
Kamannin halittun ya yi kamar garwashi mai cin wuta ko kuwa kamar fitilu. Wuta tana kai da kawowa a cikin halittun; ta yi haske ƙwarai, walƙiya kuma tana wulgawa daga cikinta.
14 Et les animaux couraient et revenaient tels qu'on voit la foudre.
Halittun suna gaggauta kai da kawowa kamar walƙiya.
15 Comme je regardais les animaux, voici, il y avait une roue sur la terre près des animaux à leurs quatre côtés.
Yayinda nake kallon rayayyun halittun nan, sai na ga da’ira a ƙasa kusa da kowace halitta da fuskokinsa huɗu.
16 L'aspect des roues et leur structure étaient ceux de la pierre de Tarsis; et la forme de l'une était celle des quatre; et leur aspect et leur structure étaient comme si une roue passait par le milieu de l'autre roue.
Ga kamanni da fasalin da’irorin. Suna ƙyalƙyali kamar kirisolit, kuma dukan huɗun sun yi kama da juna. Kowacce ta yi kamar da’ira a cikin da’ira.
17 Dans leur marche elles cheminaient de leurs quatre côtés, et ne se tournaient point dans leur marche.
Yayinda suke tafiya, sukan nufi duk wani gefe guda cikin gefe huɗun da halittun suka nufa; da’irorin ba za su juya ba sa’ad da halittun suke tafiya.
18 Et leurs jantes étaient hautes et formidables, et leurs jantes étaient remplies d'yeux de toutes parts à toutes quatre.
Ƙarafansu da suka yi kamar zobe sun yi tsayi suna kuma da bantsoro, dukan ƙarafan nan huɗu kuwa da suka yi kamar zobe suna cike da idanu a kewaye.
19 Quand les animaux marchaient, les roues cheminaient aussi à côté d'eux, et quand les animaux s'élevaient de terre, les roues s'élevaient aussi.
Sa’ad da rayayyun halittun suke tafiya, da’irorin da suke kusa da su kan motsa; kuma sa’ad da rayayyun halittun sun tashi sama, da’irorin su ma sukan tashi sama.
20 Au lieu où l'esprit les poussait à aller, ils y allaient, là où l'esprit les poussait à aller; et les roues s'élevaient avec eux, car l'esprit des animaux était dans les roues.
Duk inda ruhu za shi, su ma can za su, kuma da’irorin za su tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun nan yana a cikin da’irorin.
21 Quand ils allaient, elles allaient; et quand ils s'arrêtaient, elles s'arrêtaient; et quand ils s'élevaient de terre, les roues s'élevaient aussi avec eux, car l'esprit des animaux était dans les roues.
Sa’ad da halittun sun motsa, sai su ma su motsa; sa’ad da halittun sun tsaya cik, su ma sai su tsaya cik, sa’ad da kuma halittun sukan tashi sama, da’irorin suka tashi tare da su, domin ruhun rayayyun halittun nan yana a cikin da’irorin.
22 Et au-dessus des têtes des animaux était comme un firmament qui avait l'air d'un cristal merveilleux, étendu sur leurs têtes dans le haut.
A bisa kawunan rayayyun halittun nan akwai abin da ya yi kamar ƙanƙara, mai bantsoro.
23 Et sous le firmament étaient leurs ailes dirigées l'une contre l'autre; chacun en avait deux qui de chaque côté couvraient leur corps.
A ƙarƙashin al’arshin fikafikansu sun miƙe kyam ɗaura da juna, kuma kowanne yana da fikafikai biyu da suka rufe jikinsa.
24 Et j'entendis le bruit de leurs ailes pareil au bruit de grandes eaux, pareil à la voix du Tout-Puissant, quand ils marchaient, tumulte pareil au bruit d'un camp; quand ils s'arrêtaient, ils laissaient retomber leurs ailes.
Sa’ad da halittun suke tafiya, sai na ji ƙarar fikafikansu, kamar rurin ruwaye masu gudu, kamar muryar Maɗaukaki, kamar hayaniyar rundunar mayaƙa. In sun tsaya cik, sukan sauko da fikafikansu.
25 Et une voix retentissait au-dessus du firmament qui était sur leur tête; quand ils s'arrêtaient, ils laissaient retomber leurs ailes.
Sai aka ji murya daga al’arshi a kan kawunansu yayinda suke tsaye da fikafikansu a sauke.
26 Et au-dessus du firmament posé sur leur tête était une forme de trône, qui avait l'aspect du saphir, et sur la forme de trône était une figure ayant l'air d'un homme placé dessus en haut.
A bisa al’arshin a kan kawunansu akwai abin da ya yi kamar saffaya, kuma a can bisa a kan kursiyin akwai siffa kamar na mutum.
27 Et au dedans et autour je vis comme le brillant de l'airain, comme l'aspect du feu; en regardant de ses reins en haut et en regardant de ses reins en bas, je vis comme l'aspect du feu, et une splendeur l'environnait.
Na ga daga abin da ya yi kamar kwankwasonsa zuwa bisa ya yi kamar ƙarfe mai walƙiya, sai ka ce wuta, kuma daga kwankwasonsa zuwa ƙasa ya yi kamar wuta; haske kuma mai walƙiya sosai kewaye da shi.
28 Tel l'aspect de l'arc qui est dans la nue au jour de la pluie, tel était l'aspect de la splendeur qui l'environnait. C'était l'aspect de l'image de la gloire de l'Éternel. Et je regardai et tombai sur ma face, et j'entendis la voix de quelqu'un qui parlait.
Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka hasken da ya kewaye shi. Wannan shi ne kwatancin kamannin ɗaukakar Ubangiji. Sa’ad da na gani, sai na fāɗi rubda ciki, na kuma ji muryar wani tana magana.